{"id":4524,"date":"2025-05-17T04:40:17","date_gmt":"2025-05-17T04:40:17","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4524"},"modified":"2025-05-17T04:40:17","modified_gmt":"2025-05-17T04:40:17","slug":"tajdidin-shehu-dan-fodiyo-tabbatar-da-addini-neman-mulki-ko-kabilanci-2-sheikh-aminu-aliyu-gusau","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4524","title":{"rendered":"TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU"},"content":{"rendered":"<p>TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2).<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>DAIDAITA FAHIMTA:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kafin mu tsunduma a cikin munakashar da zamu yi yana da kyau mu daidaita fahimtar jama&#8217;a kan wasu manyan shubuhohi da ke tattare da wannan tattaunawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga cikin abubuwan da tarihi ingantacce ya tabbatar akwai cewar:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>1 . Shehu Dan Fodiyo ba shine ya yo hijira daga wani wurin ya sauka kasar Hausa ya kulla yakin da su ba. Ba shine ya jagoranto Fulani zuwa kasar Hausa ba. Shehu haifaffen dan kasar Gobir ne. Kakannin sa sun yi shekaru a kalla dari biyu da hansin (250) zuwa dari uku (300) da tarewa kasar Gobir kafin a haife shi. Don haka Shehu ba bako ba ne a Gobir, bai san ko ina ba banda kasar Hausa. Su ma Sarakunan Gobir da na sauran kasashen Hausa wadanda Shehu ya yi lokaci da su ba su dauki Fulani baki ba, sun dai dauki cewar su ma talakawansu ne, kamar sauran Hausawa. A cikin dukkan littafan tarihin jihadin Shehu babu inda aka taba ruwaito cewar Sarakunan kasar Hausa na lokacin suna kiran Fulani da &#8220;Baki&#8221;, sai dai ko su ce masu &#8220;&#8216;yan Fulani&#8221;, ko kuma su ce masu &#8220;mabiyan Usman&#8221;, saboda wanda ya yi a kalla shekaru dari uku ga wuri ya wuce a ce masa bako. Kalmar cewar &#8220;Baki&#8221; sun zo sun yi tawaye sun karbe mulki, masu son kawo fitina a yau ne suka zo da ita. Zamu yi karin bayani game da yawan shekarun da Hausawa suka riga Fulani da su, da zuwa kasar da bayan zuwansu ake kiranta &#8220;kasar Hausa&#8221; in sha Allahu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>2 . Shehu Tajdidin Musulunci ya yi. Shehu malami ne mai Da&#8217;awa, wanda dukkan matakan da ya dauka tun daga wa&#8217;azi har zuwa yaki da kafa daula sai da ya rubuta a kalla littafi daya domin bayyana manufofinsa da hujjojinsa na Addinin Musulunci na daukar wannan matakin. Dukkan wadannan littafai da ya rubuta da wadanda mabiyan sa suka rubuta duk suna nan a kasuwa, kowa zai iya samun su har zuwa yau din nan. Maganar Tajdidi magana ce ta ilimi da hujjojin Addini. Ba dole ne wani ya yarda da hujjojin Shehu ba, amma hakan ba zai ba kowa damar ya kautar masa da manufofin sa ba zuwa wani abu daban, kamar a ce manufar ta&#8217;addanci ya ke da ita, ko ta neman mulki ko ta kabilanci, ba tare da kawo ko wace irin hujja ba in banda shaci fadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>3 . A yau Tajdidin Shehu yana da shekaru dari biyu da ashirin da daya (221) da wucewa. Bayan shi ma har turawa sun shigo sun rusa daular da ya samar, sun yi mulki na a kalla shekaru sittin (60) sun wuce da tsawon shekaru sittin da biyar (65). A Najeriyar yau, da Nijar din yau, ba daular Shehu ce ke mulki ba, sannan Bafulatani ko da shi Sarkin gargajiya ne ba bu abunda ya ke iya hana Bahaushe ko Bazabarme ko Buzu samu don kawai su ba Fulani bane. To tambaya a nan ita ce: su masu yunkurin raba kan Fulani da Hausawa a Najeriya da Nijar, me suke son cimmawa? In banda sarautar gargajiya wane abu ne Fulani suka tare ma wasunsu daga samu? Idan sarautar gargajiyar ta komai hannun Hausawa wane ci gaba ne za ta kawo muna a matsayin mu na musulmi, ko &#8216;yan arewacin Najeriya, ko &#8216;yan Najeriyar, ko &#8216;yan Nijar, ko ma a matsayinmu na Hausawa?<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>12\/11\/1446<\/p>\n<p>H.<\/p>\n<p>10\/05\/2025M.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO &#8211; TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2). &nbsp; DAIDAITA FAHIMTA: &nbsp; Kafin mu tsunduma a cikin munakashar da zamu yi yana da kyau mu daidaita fahimtar jama&#8217;a kan wasu manyan shubuhohi da ke tattare da wannan tattaunawa. &nbsp; Daga cikin abubuwan da tarihi ingantacce ya tabbatar akwai cewar: &nbsp; [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4525,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[62],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4524","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-books-journal"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4524","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4524"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4524\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4526,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4524\/revisions\/4526"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4525"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4524"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4524"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4524"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}