{"id":4506,"date":"2025-05-16T19:21:52","date_gmt":"2025-05-16T19:21:52","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4506"},"modified":"2025-05-16T19:21:52","modified_gmt":"2025-05-16T19:21:52","slug":"shugaban-%c6%99asa-bola-ahmed-tinubu-ya-bu%c6%99aci-sojojin-najeriya-su-%c6%99ara-jajircewa-wajen-ya%c6%99ar-matsalolin-tsaro-da-ke-addabar-%c6%99asar-nan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4506","title":{"rendered":"Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu, ya bu\u0199aci sojojin Najeriya su \u0199ara jajircewa wajen ya\u0199ar matsalolin tsaro da ke addabar \u0199asar nan."},"content":{"rendered":"<p>Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu, ya bu\u0199aci sojojin Najeriya su \u0199ara jajircewa wajen ya\u0199ar matsalolin tsaro da ke addabar \u0199asar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce zaman lafiya, dimokura\u0257iyya, da ci gaban tattalin arzi\u0199i duk suna dogara ne da tsaron \u0199asa.<\/p>\n<p>Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin \u0199addamar da sabbin jiragen sama guda biyu \u0199irar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bikin ya kasance wani \u0253angare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mataimakin shugaban \u0199asa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce Najeriya na bu\u0199atar ingantaccen tsaro domin \u2019yan \u0199asa su samu damar yin harkokin rayuwa cikin kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cDimokura\u0257iyya da tattalin arzi\u0199in Najeriya na bu\u0199atar cikakken tsaro. Dole ne a mur\u0199ushe wa\u0257anda ke barazana ga zaman lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u2019Sojoji masu \u0199arfi da kayan aiki masu inganci na da muhimmanci ga makomar \u0199asar nan,\u201d in ji Tinubu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sabunta kayan aikin soji tare da saka hannun jari a fannin tsaro don tunkarar barazanar \u2018yan ta\u2019adda da sauran matsalolin tsaro.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cWannan ci gaban zai taimaka wajen jawo saka hannun jarin a cikin gida da waje, sannan ya samar da cikakken tsaro a \u0199asa,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma bu\u0199aci rundunar soji da ta kasance a shirye don samar da zaman lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya bayyana cewa sabbin jiragen suna da amfani matu\u0199a ga harkokin soji da na jin-\u0199ai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, tuni aka kar\u0253i sabbin jirage tara tun daga shekarar 2024, kuma ana sa ran samun wasu 49 cikin shekaru biyu masu zuwa, ciki har da jiragen ya\u0199i na zamani da na \u0257aukar kaya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abubakar, ya bayyana cewa an riga an horar da matu\u0199a jirage takwas da injiniyoyi 18 don aiki da sabbin jiragen, yayin da wasu ke ci gaba da karatu a \u0199asashen waje.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tinubu, ya bu\u0199aci rundunar sojin sama da ta kula da sabbin jiragen da \u0199warewa domin amfanin \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto<\/p>\n<p>Mustapha Garba Usman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu, ya bu\u0199aci sojojin Najeriya su \u0199ara jajircewa wajen ya\u0199ar matsalolin tsaro da ke addabar \u0199asar nan. &nbsp; Ya ce zaman lafiya, dimokura\u0257iyya, da ci gaban tattalin arzi\u0199i duk suna dogara ne da tsaron \u0199asa. Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin \u0199addamar da sabbin jiragen sama guda biyu \u0199irar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4507,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4506","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4506","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4506"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4506\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4508,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4506\/revisions\/4508"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4507"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4506"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4506"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4506"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}