{"id":4413,"date":"2025-05-14T17:23:07","date_gmt":"2025-05-14T17:23:07","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4413"},"modified":"2025-05-14T17:23:07","modified_gmt":"2025-05-14T17:23:07","slug":"rundunar-sojan-nijeriya-ta-magantu-kan-hare-haren-yan-taadda-a-borno","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4413","title":{"rendered":"Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu\u00a0 kan Hare-haren \u2018Yan Ta\u2019adda a Borno"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu\u00a0 kan Hare-haren \u2018Yan Ta\u2019adda a Borno<\/p>\n<p style=\"text-align: center\">\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da jerin hare-haren da aka kai kan sansanoninta tare da kwantar da hankulan \u2018yan \u0199asar cewa tana da \u0199arfin iya mur\u0199ushe \u2018yan ta\u2019addan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan na zuwa ne bayan \u2018yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare kan fararen hula da sojoji a \u0199asar kwanan nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamandan runduna ta musamman, Operation Hadin Kai, da ke ya\u0199i da \u2018yan ta\u2019adda a yankin, Manjor Janar Abdulsalam Abubakar, ya tabbatar da hare-haren a wani taron manema labarai a birnin Maiduguri ranar Talata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce hare-haren da \u2018yan ta\u2019addan suka kai kan garuruwan Dikwa da Gajiram ba su yi nasara ba, yayin da dakarun Nijeriya da \u2018yan ta\u2019addan suka fafata a garin Rann, fadar \u0199aramar hukumar Kala Balge.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sababbin dabarun ya\u0199i da ta\u2019addanci<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A lokacin taron manem labaran, kwamandan rundunar ya tabbatar da hare-haren da aka kai kan sansanoni sojin uku tare da mutuwar sojoji hu\u0257u a Rann.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cA cikin wata biyu da suka wuce, mun kasance muna sake dabaru, muna sake tsare-tsare. Babban hafsan sojin \u0199asan Nijeriya ya ziyarci wajen a makonni biyu da suka gabata, kuma an yi wasu sauye-sauye a filin dagan. Ni ma ina \u0257aya daga cikin sauye-sauyen, cikin makonni uku da suka wuce na kar\u0253i ragamar jagorantar ya\u0199in,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cAna \u0199ara yawan kafafe da jami\u2019ai a filin daga. Abin da \u2018yan ta\u2019addan suka koma yi shi ne kai hare-hare kan \u0257ai\u0257aikun wurare da ke da rauni suna amfani da shi wajen ya\u0257a farfaganda wanda shi ya sa muke sake nazari kan yadda muke tura jami\u2019ai. A jiya kawai, an kai hare-hare Rann da Dikwa da kuma Gajiram. Mun mur\u0199ushe dukkan wa\u0257annan hare-haren, idan ban da Rann, inda suka yi nasarar kutsewa zuwa wani mataki, lamarin da ya janyo mutuwar jami\u2019ai [soji] hu\u0257u,\u201d in ji kwamandan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin da yake tabbatar wa mutane jajircewar sojin wajen kawar da ta\u2019addanci a yankin, Janar Abubakar ya bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan ba sa nuna cewa Boko Haram za ta koma irin yadda take da \u0199arfi a da.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u2018Yan ta\u2019adda na amfani da jirage marsa matu\u0199a<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Janar Abubakar ya bayyana ta\u0253ar\u0253arewar lamarin tsaro yankin Sahel a matsayin muhimmin dalilin da ke taimaka wa sabbin hare-haren.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa sace makamai daga barikin sojoji da kuma ya\u0257uwar makamai a kan iyakokin Nijeriya na \u0199ara wa \u2018yan ta\u2019addan \u0199arfi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kazalika ya ce rundunar sojin \u0199asar ta lura da wani abin damuwa game da yadda \u2018yan ta\u2019addan ke sauya salon hare-harensu, musamman fara amfani da jirage mara matu\u0199i masu makamai tun watan Nuwamban bara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamandan ya bayyana wahalar iya gano jirage mara matu\u0199an ta hanyar amfani da fasahar gano tafiyar jirgi da aka saba da ita, inda ya kwatanta lamarin da yadda ake amafani da jirage mara matu\u0199a a rikicin Isra\u2019ila da kuma rikicin Yukrain.<\/p>\n<p>[5\/14, 6:18 PM] MUSA BADAMASI GAMA: \u201cA shekaru biyun da suka wuce, mun shirya yin shelar cewa ya\u0199in ya \u0199are, amma ta\u0253arbarewar tsaro a \u0199asashen Sahel ta shafe mu,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Majalisar dattawan Nijeriya ta nemi a tura \u0199arin sojoji Borno da Yobe<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198udurin ya biyo bayan \u0199arin hare-haren \u2018yan ta\u2019addan ne a arewa maso gabashin Nijeriya, ciki har da kisan sojoji a garin Marte.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa an samu ci-gaba sosai wajen tabbatar da zaman lafiya idan aka kwatanta da shekaru biyar zuwa goma da suka wuce, inda ya yi ishara da komawar kimanin mutum 200,000 zuwa Malam Fatori da Kukawa a matsayin nasarori na baya bayan nan. Ya bayyana cewa sama da \u2018yan ta\u2019adda 20 ne aka kashe kuma aka \u0199wato makamai cikin makon da ya gabata kawai<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa cikin watanni biyun da suka wuce sojin \u0199asar sun fara sake dabaru da kuma sake tsare-tsare domin tinkarar sabuwar bazaranar da ke kunno kai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babban hafsan sojin \u0199asan Nijeriya, Lutanan Janar Olufemi Olatunbosun ya ziyarci fagen dagan kwanan nan, lamarin da ya janyo wasu sauye-sauye ciki har da kama aikin kwamandan rundunar da ke ya\u0199i da \u2018yan ta\u2019addan mako ukun da suka wuce. Ana \u0199ara tura yawan jami\u2019ai da kayayyaki zuwa yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamandan ya ce duk da \u0199alubalen da sojojin ke fuskanta, rundunar sojin \u0199asar ta shirya domin mur\u0199ushe ta\u2019addanci a cikin \u0199an\u0199anin lokaci, inda ya bu\u0199aci \u2018yan Nijeriya su ci gaba goya wa sojojin baya. TRT African Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.S.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar Sojan Nijeriya ta Magantu\u00a0 kan Hare-haren \u2018Yan Ta\u2019adda a Borno &nbsp; Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da jerin hare-haren da aka kai kan sansanoninta tare da kwantar da hankulan \u2018yan \u0199asar cewa tana da \u0199arfin iya mur\u0199ushe \u2018yan ta\u2019addan. &nbsp; Wannan na zuwa ne bayan \u2018yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare kan fararen [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4414,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4413","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4413","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4413"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4413\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4415,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4413\/revisions\/4415"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4414"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4413"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4413"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4413"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}