{"id":4407,"date":"2025-05-14T17:09:16","date_gmt":"2025-05-14T17:09:16","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4407"},"modified":"2025-05-14T17:09:16","modified_gmt":"2025-05-14T17:09:16","slug":"karnuka-yan-bindiga-sunyi-kalace-da-jarirai-a-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4407","title":{"rendered":"KARNUKA YAN BINDIGA SUNYI KALACE DA JARIRAI A ZAMFARA"},"content":{"rendered":"<p>KARNUKA YAN BINDIGA SUNYI KALACE DA JARIRAI A ZAMFARA<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u018aan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda \u2019yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani \u0199auye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, \u2019yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yadda \u2019yan bindiga suka kashe jarirai, suka bai wa karnuka namansu a Zamfara<\/p>\n<p>\u018aan majalisar ya ce a yanzu Zamfara ta zama tarkon mutuwa a wajen jama&#8217;ar gari.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da muna kan mulki ni da Lamido da mun \u0199alubalanci Tinubu \u2014 Amaechi<\/p>\n<p>Za\u0253en 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa \u2014 Sule Lami\u0257o<\/p>\n<p>Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani \u0199auye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, \u2019yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfa\u0257iya ya mutu bayan da ya fa\u0257i a dajin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce \u2019yan bindigar sun nemi mahaifin yaron da ya mi\u0199a musu shi, gudun ka da ya rasa sauran yaransa ya umarci yaron ya je wajensu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yaron ya yarda ya tafi, kuma nan take suka harbe shi har lahira.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u018aan majalisar ya ce irin wa\u0257annan abubuwa na nuna cewa gwamnati ta kasa kare mutane a Zamfara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci Gwamnatin Tarayya da ta \u0257auki matakin gaggawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana yadda ya yi al\u0199awari kafin za\u0253en 2023, inda ya fa\u0257a wa jama\u2019a cewa sabuwar gwamnati za ta bai wa tsaro muhimmanci, amma yanzu al\u2019amura sun \u0199ara lalacewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cMun cuci mutanenmu. Ba sa iya zuwa gonakinsu. Tattalin arzi\u0199insu ya rushe. Mutane da dama sun rasa matsuguninsu, kuma babu wani taimako daga gwamnati,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce ya gana da wasu shugabannin tsaro har da Ministan Tsaro, amma babu wani canji da aka samu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cZamfara tana cikin aminci. Yanzu kuwa, tana daga cikin wuraren da rikici ya fi \u0199amari. Kundin tsarin mulki ya ce gwamnati na da alhakin kare rayuka da dukiyoyi, amma hakan ba ya faruwa a yanzu.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da aka tambaye shi game da bai wa jama\u2019a dama su kare kansu, sai ya ce doka ta fi komai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cMu \u2019yan majalisa ne, ba ma\u2019aikatan tsaro ba. Ba za ce mutane su \u0257auki makami ba. Amma gaskiya ne, mutane suna ganin yadda aka bar su,\u201d in ji Jaji.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n<p>AT-TAJDID NEWS<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>KARNUKA YAN BINDIGA SUNYI KALACE DA JARIRAI A ZAMFARA &nbsp; \u018aan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda \u2019yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. &nbsp; Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4408,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4407","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4407","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4407"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4407\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4409,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4407\/revisions\/4409"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4408"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4407"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4407"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4407"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}