{"id":4254,"date":"2025-02-10T07:01:39","date_gmt":"2025-02-10T07:01:39","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4254"},"modified":"2025-02-10T07:01:39","modified_gmt":"2025-02-10T07:01:39","slug":"babu-wani-mai-%c6%99arfin-iko-da-ya-isa-ya-tilasta-wa-falas%c9%97inawa-barin-%c6%99asarsu-erdogan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4254","title":{"rendered":"Babu Wani Mai \u0199arfin Iko da ya Isa ya Tilasta wa Falas\u0257inawa Barin \u0199asarsu- Erdogan"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa babu wani mai \u0199arfin iko da ya isa ya tilasta wa mutanen Gaza ficewa daga \u0199asarsu ta \u201cdindindin\u201d, domin kuwa yankin Gaza da Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin \u0198udus yankuna ne mallakin Falas\u0257inawa.<\/p>\n<p>&#8220;Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga \u0199asarsu, wadda aka kafa dubban shekaru. Yankin Falas\u0257inu, wanda ya ha\u0257a da Gaza, Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin \u0198udu, na Falas\u0257inawa ne,&#8221; in ji Recep Tayyip Erdogan a hira da manema labarai ranar Lahad a Istanbul kafin ya tashi zuwa \u0199asar Malaysia.<\/p>\n<p>Shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar game da da kwashe Falas\u0257inawa daga yankin Gaza, bayan shan matsin lamba daga Yahudawa masu tsaurin ra&#8217;ayi, ba batu ne da ya kamata a tattauna a kansa ba, in ji Shugaba Erdogan.<\/p>\n<p>Kazalika Erdogan ya jinjina wa \u0199ungiyar Hamas bisa cika al\u0199awuran da ta \u0257auka na yin musayar fursunoni da Isra&#8217;ila, duk kuwa da cewa ta yi \u0199o\u0199arin keta yarjejeniyar.<\/p>\n<p>Game da halin da ake ciki a Syria, Shugaba Erdogan ya ce ana ci gaba da tono manyan \u0199aburbura a sassa daban-daban na Syria, lamarin da ke \u0199ara tona asirin gwamnatin Assad.<\/p>\n<p>Shugaban Turkiyya ya bayyana fatansa na ganin an samu zaman lafiya a Syria a \u0199ar\u0199ashin jagorancin Shugaba Ahmed Alsharaa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba \u0199asar za ta samu kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Babu gurbin \u0199ungiyoyin &#8216;yan ta&#8217;adda a Syria, in ji Erdogan, wanda ya jaddada cewa shugaban Syria Ahmad Alsharaa zai yi ya\u0199i da wa\u0257annan \u0199unguyoyi.<\/p>\n<p>Mai rahoto;<br \/>\nM.B.S.Gama.<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa babu wani mai \u0199arfin iko da ya isa ya tilasta wa mutanen Gaza ficewa daga \u0199asarsu ta \u201cdindindin\u201d, domin kuwa yankin Gaza da Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin \u0198udus yankuna ne mallakin Falas\u0257inawa. &#8220;Babu wani mutum da yake da ikon fitar da mutanen Gaza daga [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4255,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4254","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4254","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4254"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4254\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4256,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4254\/revisions\/4256"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4255"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4254"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4254"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4254"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}