{"id":4238,"date":"2025-01-23T19:14:20","date_gmt":"2025-01-23T19:14:20","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4238"},"modified":"2025-01-23T19:14:20","modified_gmt":"2025-01-23T19:14:20","slug":"turkish-airlines-ya-koma-zirga-zirga-zuwa-syria-bayan-shafe-shekaru-11-da-dakatarwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4238","title":{"rendered":"Turkish Airlines ya Koma Z\u0131rga-z\u0131rga Zuwa Syria Bayan Shafe Shekaru 11 da Dakatarwa"},"content":{"rendered":"<p>Kamfanin jiragen saman Turkish Airlines ya ce ya koma da zirga-zirgar jiragensa zuwa \u0199asar Syria bayan shafe tsawon shekaru 11 da dakatarwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Alhamis ne jirgin farko ya tashi daga Istanbul zuwa Damascus, yayin da &#8216;yan Syria da dama suka yi ta nuna farin cikinsu da komawa \u0199asarsu bayan shafe shekaru da dama suna gudun hijira.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A\u0199alla mutane 350 ne suka samu damar shiga jirgin farko, inda wasu daga cikinsu ke \u0257auke da tutar \u0199asar Syria.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u018aaya daga cikin fasinjojin mai suna Fatma Zehra ta shaida wa manema labarai cewa ta zo Turkiyya ne tun tana &#8216;yar shekara 2 a duniya, kuma a yanzu tana matu\u0199ar farin cikin komawa tare da danginta zuwa \u0199asarsu ta asali inda aka haife ta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8221;Ban ta\u0253a ganin \u0199asata ba, ina matukar farin cikin ganinta a karon farko. Za mu tashi ne daga Damascus zuwa Aleppo. Zan ga kakata a can,&#8221; a cewar Zehra, wadda a yanzu take da shekaru 14.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kimanin &#8216;yan Syria miliyan 4 ne suka samu mafaka a ma\u0199wabciyar \u0199asar Turkiyya a lokacin ya\u0199in basasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar wani fasinjan jirgin, Ahmet Kiraz, ya zo Turkiyya ne a shekarar 2012, inda ya gina rayuwarsa ta hanyar karatu da samun aiki, kuma bai ta\u0253a tunanin komawa Syria ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8221;Mun yi tsammanin ba za mu ta\u0253a komawa ba,&#8221; in ji shi. Amma a lokaci da damar ta zo, mun yi farin ciki sosai. Zan koma \u0199asata a jirgin farko, ji nake yi kamar ina mafarki,&#8221; a cewar Kiraz.<\/p>\n<p>TRT African Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.S.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kamfanin jiragen saman Turkish Airlines ya ce ya koma da zirga-zirgar jiragensa zuwa \u0199asar Syria bayan shafe tsawon shekaru 11 da dakatarwa. &nbsp; A ranar Alhamis ne jirgin farko ya tashi daga Istanbul zuwa Damascus, yayin da &#8216;yan Syria da dama suka yi ta nuna farin cikinsu da komawa \u0199asarsu bayan shafe shekaru da dama [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4239,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4238","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4238","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4238"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4238\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4240,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4238\/revisions\/4240"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4239"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4238"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4238"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4238"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}