{"id":4231,"date":"2025-01-23T13:19:14","date_gmt":"2025-01-23T13:19:14","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4231"},"modified":"2025-01-23T13:19:14","modified_gmt":"2025-01-23T13:19:14","slug":"dakarun-israila-sun-kai-samame-ga%c9%93ar-yammacin-kogin-jordan-a-yayin-da-suka-mamaye-jenin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4231","title":{"rendered":"Dakarun Isra&#8217;ila Sun Kai Samame Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan a Yayin da Suka Mamaye Jenin"},"content":{"rendered":"<p>Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na hu\u0257u bayan Isra&#8217;ila ta kashe Falas\u0257inawa a\u0199alla 47,161 a yankin sannan mahukuntan Isra&#8217;ila sun ci gaba da kai farmaki a Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dakarun Isra&#8217;ila suna shirin shiga Jenin da ke Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan, inda suak tsaya a \u0199auyen Muqeibila ranar 22 ga Janairu, 2025.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dakarun Isra&#8217;ila sun kai samame a sassa daban-daban na Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan, a cewar wasu majiyoyi, a yayin da suka mamaye birnin Jenin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamfanin dillacin labaran WAFA na Falas\u0257inu ya ruwaito cewa dakarun Isra&#8217;ila sun kutsa cikin garin Turmusayya da ke arewacin Ramallah, kuma sun mamaye wasu muhimman gine-ginen gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Jenin, dakarun Isra&#8217;ila sun shiga \u0199auyen Fahma inda suka ri\u0199a harba tiyagas kan mutane, lamarin da ya kai ga arangama a tsakaninsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Bethlehem, dakarun Isra&#8217;ila sun kai samame a garin al-Khader, inda suka mamaye Hanyar Birnin \u0198udus zuwa Hebron sannan suka ri\u0199a fesa barkonon-tsohuwa kan &#8216;yan kasuwa a cikin shagunansu, ko da yake ba a samu rahoton jikkata ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi magana da Firaministan Isra&#8217;ila Benjamin Netanyahu domin jaddada goyon bayan Amurka a gare su, sannan mutanen biyu sun tattauna game da Iran da kuma yahudawan Isra&#8217;ila da ake garkuwa da su a Gaza, a cewar Ma&#8217;aikatar Harkokin Wajen Amurka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan shi ne karon farko da Rubio ya yi magana da jami&#8217;an Isra&#8217;ila tun bayan da aka rantsar da Donald Trump ranar Litinin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Trump da mutumin da ya gabace shi, tsohon shugaban \u0199asa Joe Biden, sun bayyana goyon ya\u0199in kisan \u0199are-dangin da Isra&#8217;ila take yi a Gaza.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rubio ya bayyana muhimmancin matakin &#8221; Amurka na ci gaba da goyon bayan Isra&#8217;ila a matsayin babban abin da Trump ya sanya a gaba,&#8221; in ji wata sanarwa da Ma&#8217;aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rubio ya shaida wa Netanyahu cewa Washington za ta ci gaba da goyon bayan Isra&#8217;ila &#8220;ba tare da gajiyawa ba&#8221; domin ganin an ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Kazalika Sakataren Harkokin Wajen ya mi\u0199a fatansa na ganin an da\u0199ile duk wata barazana da ke fitowa daga Iran da kuma tabbatar da zaman lafiya,&#8221; a cewar sanarwar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ya yin da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na hu\u0257u bayan Isra&#8217;ila ta kashe Falas\u0257inawa a\u0199alla 47,161 a yankin sannan mahukuntan Isra&#8217;ila sun ci gaba da kai farmaki a Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.S.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na hu\u0257u bayan Isra&#8217;ila ta kashe Falas\u0257inawa a\u0199alla 47,161 a yankin sannan mahukuntan Isra&#8217;ila sun ci gaba da kai farmaki a Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan. &nbsp; Dakarun Isra&#8217;ila suna shirin shiga Jenin da ke Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan, inda suak tsaya a \u0199auyen Muqeibila ranar 22 ga [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4232,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4231","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4231","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4231"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4231\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4233,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4231\/revisions\/4233"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4232"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4231"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4231"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4231"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}