{"id":4216,"date":"2025-01-23T06:57:10","date_gmt":"2025-01-23T06:57:10","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4216"},"modified":"2025-01-23T06:57:10","modified_gmt":"2025-01-23T06:57:10","slug":"adadin-wa%c9%97anda-israila-ta-kashe-a-gaza-ya-kusan-kai-47200-an-gano-%c6%99arin-gawawwaki-53","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4216","title":{"rendered":"Adadin Wa\u0257anda Isra&#8217;ila ta Kashe a Gaza ya Kusan kai 47,200, an Gano \u0199arin Gawawwaki 53"},"content":{"rendered":"<p>Likitocin Falasdinawa sun gano gawawwakin Falasdinawa 53 daga karkashin baraguzan gine-gine a Gaza, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra&#8217;ila ke yi a yankin tun daga watan Oktoban 2023 zuwa 47,161, in ji ma&#8217;aikatar lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar da ma&#8217;aikatar ta fitar ta ce, an kuma kwantar da mutane 19 da suka jikkata a asibitoci cikin sa&#8217;o&#8217;i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 111,166 a harin da Isra&#8217;ila ta kai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto ba su iya isa gare su,&#8221; in ji ta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sojojin Isra&#8217;ila sun kashe wani Bafalas\u0257ine magidanci a gaban matarsa da &#8216;ya&#8217;yansa uku yayin da yake tu\u0199a mota a birnin Jenin citda ke arewacin Ga\u0253ar Yamma da Kogin Jordan a yayin da Isra&#8217;ila ke ci gaba da kutsawa yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wani bidiyo da iyalan mutumin suka \u0257auka wanda aka ri\u0199a watsawa a shafukan intanet ya nuna mawuyacin halin da Ahmed Nimer Obeidi Shayeb lokacin da aka harbe shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A yayin da yake tattaunawa da Anadolu Agency, Bashir Matahen, Daraktan Watsa Labarai na Birnin Jenin, ya ce Ahmed Shayeb yana tare da iyalansa matarsa da &#8216;ya&#8217;ya uku suna hanyar komawa gida yayin da wani sojan Isra&#8217;ila gwanin harbi daga \u0253oye ya bu\u0257e masa wuta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A gefe guda, Matahen ya ce Falas\u0257inawa fiye da 600 sun tsere daga sansanin &#8216;yan gudun hijira na Jenin a yayin da dakarun Isra&#8217;ila suke ci gaba da kutsawa birnin na Jenin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Isra&#8217;ila ta \u0199addamar da jerin hare-hare a birnin Jenin na Ga\u0253ar Yammacin Kogin Jordan inda ta kashe Falas\u0257inawa a\u0199alla tara da jikkata a\u0199alla mutum 40, in ji jami&#8217;in kiwon lafiyar Falas\u0257inu, a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra&#8217;ila ta \u0199ulla da Hamas ta shiga kwana na hu\u0257u a Gaza.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Tel Aviv, an jikkata mutum hu\u0257u a wani hari da aka kai musu da wu\u0199a ko da yake jami&#8217;an tsaro sun kashe mutumin da ya kai harin, a cewar &#8216;yan sandan Isra&#8217;ila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumomi sun ce mutumin da ya kai harin &#8220;\u0257an \u0199asar waje&#8221; kuma yana da shekaru 28 suna masu cewa harin na ta&#8217;addanci ne. TRT African Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.S.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Likitocin Falasdinawa sun gano gawawwakin Falasdinawa 53 daga karkashin baraguzan gine-gine a Gaza, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra&#8217;ila ke yi a yankin tun daga watan Oktoban 2023 zuwa 47,161, in ji ma&#8217;aikatar lafiya. &nbsp; Sanarwar da ma&#8217;aikatar ta fitar ta ce, an kuma kwantar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4217,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4216","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4216","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4216"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4216\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4218,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4216\/revisions\/4218"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4217"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4216"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4216"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4216"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}