{"id":4172,"date":"2025-01-10T06:13:09","date_gmt":"2025-01-10T06:13:09","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4172"},"modified":"2025-01-10T06:13:09","modified_gmt":"2025-01-10T06:13:09","slug":"masu-shiga-tsakani-sun-samu-ci-gaba-a-tattaunawar-tsagaita-wuta-a-gaza-amma-har-yanzu-ba-a-cim-ma-matsaya-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4172","title":{"rendered":"Masu Shiga Tsakani Sun Samu ci-gaba a Tattaunawar Tsagaita Wuta a Gaza, Amma har Yanzu ba a Cim ma Matsaya ba"},"content":{"rendered":"<p>Majiyoyin Falas\u0257inawa da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi sun ce Amurka da masu shiga tsakani na Larabawa sun samu ci-gaba a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, amma ci-gaban bai kai yadda za a cim ma matsaya ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin da ake ci gaba da tattaunawar a Qatar, sojojin isra\u2019ila sun kai hare-hare a fa\u0257in yankin Falas\u0257inu da aka mamaye, inda suka kashe a\u0199alla mutane 17, a cewa cibiyoyin lafiya na Falas\u0257inu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kashe-kashen sun kawo adadin wa\u0257anda hare-haren Isra\u2019ila suka yi sanadiyyar mutuwarsu zuwa 70 a fa\u0257in Gaza cikin sa\u2019o\u2019i 24, kamar yadda ma\u2019aikatar lafiyar yankin ta bayyana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Qatar da Amurka da Masar suna wani gagrumin yun\u0199uri na ganin an cim ma matsaya don dakatar da ya\u0199in da Isra\u2019ila take yi a Gaza da kuma sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su kafin Joe Biden ya bar ofis.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi garga\u0257in cewa \u201cza a ga balbalin bala\u2019i\u201d idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba zuwa lokacin da za a rantsar da shi ranar 20 ga Janairu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Alhamis, jami\u2019an Falas\u0257inawa da ke kusa da tattaunawar sun ce, rashin cin ma matsaya kawo yanzu ba ya nufin cewa tattaunawar ba ta kai ko ina ba, kuma wannan ne yun\u0199urin da ya fi kowanne mayar da hankali kawo yanzu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cAkwai muhimmiyar tattaunawa da ake yi, masu shiga tsakani da masu tattaunawa suna yin magana sosai akan kowace kalma da kowane batu. An samu nasara idan aka duba yadda aka warware wasu batutuwa da suka zama kiki-kaka a baya, amma dai har yanzu ba a cim ma matsaya ba,\u201d kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ba tare \u0199arin bayani ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An shafe fiye da shekara guda \u0253angarorin biyu sun ma\u0199ale a wajen \u0257aya kan muhimman batutuwa biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hamas ta ce za ta saki sauran fursunonin ne kawai idan Isra\u2019ila ta amince da kawo \u0199arshen ya\u0199in ta kuma janye duka sojojinta daga Gaza.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majiyoyin Falas\u0257inawa da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi sun ce Amurka da masu shiga tsakani na Larabawa sun samu ci-gaba a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, amma ci-gaban bai kai yadda za a cim ma matsaya ba. &nbsp; Yayin da ake ci gaba da tattaunawar a Qatar, sojojin isra\u2019ila sun kai hare-hare [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4173,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4172","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4172","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4172"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4172\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4174,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4172\/revisions\/4174"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4173"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4172"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4172"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4172"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}