{"id":4148,"date":"2025-01-06T17:16:07","date_gmt":"2025-01-06T17:16:07","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4148"},"modified":"2025-01-06T17:16:07","modified_gmt":"2025-01-06T17:16:07","slug":"an-gabatar-da-taron-farfado-da-harkokin-ilimi-na-yankin-karamar-hukumar-bagwai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4148","title":{"rendered":"An Gabatar da Taron Farfado da Harkokin Ilimi na Yankin\u00a0 Karamar Hukumar Bagwai"},"content":{"rendered":"<p>An yi kira ga Shugabannin Makarantun Firamare dana Sakandire a yankin Karamar Hukumar Bagwai da su cigaba da bada gudunmawarsu wajen ganin yara na zuwa makarantunsu akan lokaci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Karamar Hukumar Bagwai, Injiniya Bello Abdullahi Gadanya ne yayi kiran a wajen taron Farfado da harkokin ilimi na yankin wanda hukumar ilimin Bai Daya ta jihar Kano ta jagoranta a cibiyar yada addinin muslinci dake karamar hukumar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban daga nan ya Kara da cewa karamar hukumar ta samarwa da dalibai yan asalin yankin gurbin karatu su kimanin dari 100 a manyan makarantun dake jihar nan dan\u00a0 inganta rayuwar matasan yankin .<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin shugaban hukumar ilimin Bai Daya ta jihar Kano, Alhaji Yusif Kabir wanda Daraktan Kudi da Gudanarwa ta Ma&#8217;aikatar ta wakilta, Hajiya Mariya Hodi Adam ta ce akwai matsaloli da ya kamata a duba a\u00a0 fara magancesu , inda ta Kara da cewa a Mafi yawancin lokuta\u00a0 sukan kai ziyara makarantu su tarar\u00a0 babu malami da Dalibai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hajiya\u00a0 Mariya Hodi\u00a0 ta ja hankalin malamai da su mai da hankali wajen gudanar da ayyukansu na koyo da koyarwa domin sauke nauyin da ke kansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sakataren ilimin na yankin Malam Mustapha\u00a0 Lawan Majingini na daga Cikin\u00a0 wadanda suka gabatar da Jawabi a lokacin ziyarar\u00a0 a inda ya godewa shugabannin Hukumar Ilimin Bai Daya ta jihar Kano bisa wannan ziyara ta karfafa guiwa da su kawo Karamar Hukumar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Majingini ya Kuma bayar da tabbacin cewa Malaman\u00a0 Makarantun Firamare dana Sakandire dake fadin Yankin\u00a0 za suyi kyakkyawan amfani da abubuwan da suka saurara tare da ci gaba da bayar da gudunmawarsu wajen ganin ilimi na ci gaba da samin\u00a0 tagomashi a Karamar Hukumar ta Bagwai.Radio Kano.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An yi kira ga Shugabannin Makarantun Firamare dana Sakandire a yankin Karamar Hukumar Bagwai da su cigaba da bada gudunmawarsu wajen ganin yara na zuwa makarantunsu akan lokaci. &nbsp; Shugaban Karamar Hukumar Bagwai, Injiniya Bello Abdullahi Gadanya ne yayi kiran a wajen taron Farfado da harkokin ilimi na yankin wanda hukumar ilimin Bai Daya ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4149,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4148","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4148","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4148"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4148\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4150,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4148\/revisions\/4150"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4149"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4148"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4148"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4148"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}