{"id":4136,"date":"2025-01-02T11:28:39","date_gmt":"2025-01-02T11:28:39","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4136"},"modified":"2025-01-02T11:28:39","modified_gmt":"2025-01-02T11:28:39","slug":"mece-ce-makomar-sansanonin-sojin-rasha-a-syria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4136","title":{"rendered":"Mece ce Makomar Sansanonin Sojin Rasha a Syria?"},"content":{"rendered":"<p>Tun watan Satumban 2015, aka jibge dakarun sojin Rasha da dama a \u0199asar, domin taimakawa gwamnatin Assad kare kanta a ya\u0199i da \u01b4an tawaye wa\u0257anda a lokacin suka yi ta dannawa zuwa babban birnin \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sansanonin sojojin Rasha da ke Syria wa\u0257anda suka kasance masu girma sun kasance a birnin Tartous da kuma na sojojin sama da ke Hmeimim, mai nisan kilomita 20 a kudu maso gabashin birnin Latakia.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004.jpg\"><img loading=\"lazy\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter size-medium wp-image-4137\" src=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004-300x169.jpg 300w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004-1024x576.jpg 1024w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004-768x432.jpg 768w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004-860x483.jpg 860w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0004.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/a><\/p>\n<p>Yanzu Assad ya tsere ya bar Syria kuma gwamnatinsa ta fa\u0257i &#8211; a yanzu kafofin ya\u0257a labaran Rasha sun cika ta aza ayar tambaya kan makomar kayayyakin soji, jiragen ruwa da ababen hawa da kuma dakaru 7,500.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin da kiyasi ya bambanta kan ainihin yawan jami&#8217;ai da kuma kayan aiki da ke can Syria, maganar gaskiya ita ce Rasha tana cikin matsala &#8211; me za ta yi, da kuma yadda za ta kare kadarorinta a cikin yanayi da ba a san me zai faru ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A 2017, Moscow da Damascus suka ratta\u0253a hannu kan yarjejeniya ta shekara 49 da ta bai wa Rasha damar amfani da sansanonin soji a Tartous da Hmeimim, har zuwa 2066. Sai dai, a yanzu yana da wuya a yi hasashen cewa ko sansanonin za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon Rasha.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002.jpg\"><img loading=\"lazy\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter size-medium wp-image-4138\" src=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002-300x186.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"186\" srcset=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002-300x186.jpg 300w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002-1024x636.jpg 1024w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002-768x477.jpg 768w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002-860x534.jpg 860w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0002.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/a><\/p>\n<p>Rasha ta bayyana cewa ba ta tsara ci gaba da amfani da sansanonin biyu ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Litinin, sakataren ya\u0257a labaran shugaban Rasha, ya bayyana cewa Moscow za ta tattauna kan makomar sansanoninsu da ke Syria karkashin sabon jagoranci a Damascus.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan za a yi duba ga kalaman Peskov, hakan na nuna cewa Rasha ba ta yanke hukunci kan makomar sansanonin sojinta ba da ke biranen Tartous da Latakia, don haka za ta iya shirin kwashe dakarunta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan ba aiki bane mai ka\u0257an. A \u0257aya gefen, sojojin Rasha 7,500 sun kunshi masu \u0257auke da makamai da dama da kuma kayan ya\u0199i, musamman wa\u0257anda ke sansanin sojin sama a Hmeimim.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kayayyakin sun kunshi motoci masu sulke da tsarin makamai masu linzami da kuma sauran abubuwa. Idan suka yi niyyar kwashe dakarun da kuma kayayyakin, abin zai janyo hankali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A shekarun baya, rahotanni sun nuna cewa kayayyakin sojojin Rasha da ke Syria sun ha\u0257a da manyan tankokin ya\u0199i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan har za a kwashe tankokin su ma, to sai an yi amfani a An-124, \u0257aya daga cikin manyan jirage a duniya, ta hanyar amfani da sansanin sojin sama na Hmeimim.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan Rasha ta fara aikin kwashe sojojinta cikin gaggawa daga Syria, hakan zai \u0257auki amfani da \u0257aruruwan jirage na An-124 da kuma Il-76 a cikin kankanin lokaci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A \u0257aya gefen, amfani da hanyar ruwa ta sansanin sojoji da ke birnin Tartous shi ma ba mai sauki bane.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ga Vladimir Putin, aika dubban dakaru a 2015 zuwa Syria don taimakon Assad, wata hanya ce ta nuna matsayar Rasha a matsayin mai karfi a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin da jiragen ruwa za su iya \u0257aukar jami&#8217;ai da kuma kayayyaki da dama, ba za su iya bi ta garuruwan Bosphorus da kuma Dardanelles na \u0199asar Turkiyya ba, da ya ratsa tekun Bahar Rum.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan kaddamar da mamaya kan Ukraine da Rasha ta yi, Turkiyya ta rufe hanyar ga jiragen ruwan ya\u0199i na Rasha da Ukraine karkashin tsarin taron Montreux.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rufe hanyar na nufin cewa ko da Rasha ta samar da jiragen ruwa domin kwashe dakarunta daga birnin Tartous, sai sun \u0257auki hanya mai tsawo ta tekun Mediterranean, da \u0199asar Gibraltar da kuma fa\u0257in Turai sannan zuwa ko tekun Baltic ko kuma tashoshin jiragen ruwa da ke arewaci zarcewa ta Norway da kuma tekun Barents.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan Rasha ta yanke shawarar kwashe sojojinta daga Siriya, aikin zai lakume makudan ku\u0257a\u0257e da kuma kasancewa mai girma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Me Rasa Sansanonin Syria ke Nufi ga Rasha?<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sansanonin soji a Syria na da muhimmanci ga Rasha ba wai ga mara wa gwamnatin Assad ka\u0257ai ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sun tabbatar da kasancewar sojojin Rasha a Gabas Ta Tsakiya da kuma taimakawa wajen kai jami&#8217;ai da kayayyaki zuwa Afrika, inda Rasha ke samun gagarumin goyon baya a \u01b4an shekarun nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Rasha ta hakikance cewa kayan sojinta da ke birnin Tartous ba za a ce masa babban sansani ba &#8211; kuma bai fi karfin jirgi \u0257aya ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakan kuma ya \u0199ara nuna kasancewar sojojin ruwan Rasha a tekun Mediterranean.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sansanin sojin sama na Hmeimim yana da muhimmancin gaske, inda ya zama wuri mai muhimmanci ga dukkan ayyukanta a Afrika, ciki har da sojojin hayar Rasha na Wagner.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar wata kididdiga da ba a hukumance ba, akwai sama da sojojin Rasha 7,500 a Syria, sai dai ba dukkansu bane suka fafata a ya\u0199i<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan Rasha ta samu tattaunawa da sabon gwamnati a Syria don ci gaba da iko da sansanonin, yarjejeniyar za ta zama ta daban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Bashar al-Assad ta dogara kacokan kan Rasha da kuma sojojinta da ke \u0199asar. Yanzu, Moscow za ta bu\u0199aci bayar da wani abu na daban domin samun goyon bayan Damascus.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ana ganin aika dubban dakaru a 2015 zuwa Syria domin taimakawa Assad a matsayin hanyar tabbatar da matsayin Rasha na mai karfi a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kasancewar Rasha a Gabas Ta Tsakiya, shi ne kalubalen Putin na farko daga \u0199asashen yamma da kuma iko a fa\u0257in tsohuwar tarayyar Soviet.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wani lokaci, ya zama kamar Rasha ta cimma burinta a Syria. Yanzu, alfanun sojoji da kuma hul\u0257ar diflomasiyya na tsawon shekaru da Rasha ke bai wa Syria na cikin kila-wa-kala.<\/p>\n<p>B.B.C. News.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tun watan Satumban 2015, aka jibge dakarun sojin Rasha da dama a \u0199asar, domin taimakawa gwamnatin Assad kare kanta a ya\u0199i da \u01b4an tawaye wa\u0257anda a lokacin suka yi ta dannawa zuwa babban birnin \u0199asar. &nbsp; Sansanonin sojojin Rasha da ke Syria wa\u0257anda suka kasance masu girma sun kasance a birnin Tartous da kuma na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4139,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4136","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4136","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4136"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4136\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4140,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4136\/revisions\/4140"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4139"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4136"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4136"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4136"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}