{"id":4133,"date":"2025-01-02T11:25:57","date_gmt":"2025-01-02T11:25:57","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4133"},"modified":"2025-01-02T11:25:57","modified_gmt":"2025-01-02T11:25:57","slug":"zan-%c6%99ara-bawa-yan-nijeriya-da-kamfanoni-hanyoyin-samun-bashi-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4133","title":{"rendered":"Zan \u0199ara Bawa \u2018Yan Nijeriya da Kamfanoni Hanyoyin Samun Bashi-Tinubu"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Nijeriya ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar ha\u0253aka noma da tallafa wa masana&#8217;antu don ha\u0257a muhimman magunguna a cikin gida.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta \u0199ara bu\u0257e hanyoyin samun bashi ga \u2018yan \u0199asar da ma masana\u2019antu domin \u0199arfafa tattalin arzi\u0199in \u0199asar a cikin sabuwar shekarar 2025.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jawabinsa ga \u2018yan \u0199asar wanda ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi wannan ne ta hanyar kafa wani kamfani da zai kasance asusun tabbatar da biyan bashi na \u0199asa wato National Credit Gurantee Company domin rage hatsarin ba da bashi ga bankuna da kamfanoni.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cKamfanin da ake sa ran zai fara aiki kafin tsakiyar shekara zai kasance na ha\u0257in-gwiwa ne tsakanin ma\u2019aikatun gwamnati kamar bankin masana\u2019antu da hukumar ba da bashi ga mutane (Nigerian Consumer Credit Corporation) da kamfanin zuba jari na Nijeriya da ma\u2019aikatar ku\u0257i ta Nijeriya da \u2018yan kasuwa da kuma hukumomin \u0199asa da-\u0199asa,\u201d in ji shugaban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Alkaluma sun nuna tattalin arzikin Nijeriya na bunkasa da jan hankalin masu zuba jari<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cWannan matakin zai \u0199arfafa aminci a tsarin ku\u0257in \u0199asar tare da \u0199ara hanyar samun bashi da kuma tallafa wa wa\u0257anda ba su cika samun dama ba irin su mata da matasa. Zai kawo ci-gaba da farfa\u0257o da masana\u2019antu da kuma inganta rayuwar al&#8217;umarmu,\u201d a cewar Tinubu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kazalika shugaban ya ce gwamnati za ta yi \u0199o\u0199arin tabbatar da cewa hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.6 cikin 100 zuwa kashi 15 a cikin 100 a shekarar 2025 ta hanyar ha\u0253aka harkar noma tare da inganta ha\u0257a muhimman magunguna a cikin gida.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban, da ya nemi \u2018yan \u0199asar su goya masa baya wajen tabbatar da cewa tattalin arzi\u0199in \u0199asar ya kai na dala tiriliyon \u0257aya, ya ce dole \u2018yan \u0199asar su inganta biyayyarsu ga \u0199asar domin ta iya cim ma muradunta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cGaskiyar \u2018yan \u0199asa da kuma amincewarsu da \u0199asar na da muhimmanci wajen nasarar Muradun Sabon Fata,\u201d in ji shugaban wanda ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama\u2019a game da halayen da suka kamata \u2018yan \u0199asar su kasance suna da su.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa shi zai \u0199addamar da wani shrin wayar da kan jama\u2019a a shekarar 2025 wanda zai mayar da hankali kan kishin \u0199asa da kuma son \u0199asa ta yadda wa\u0257anda suke gwamnati da sauran \u2018yan \u0199asa za su yarda da juna tare da ha\u0257a kai. TRT Africa Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Nijeriya ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar ha\u0253aka noma da tallafa wa masana&#8217;antu don ha\u0257a muhimman magunguna a cikin gida. &nbsp; Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta \u0199ara bu\u0257e hanyoyin samun bashi ga \u2018yan \u0199asar da ma masana\u2019antu domin \u0199arfafa tattalin arzi\u0199in \u0199asar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4134,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4133","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4133","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4133"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4133\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4135,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4133\/revisions\/4135"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4134"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4133"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4133"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4133"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}