{"id":4130,"date":"2025-01-02T11:24:22","date_gmt":"2025-01-02T11:24:22","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4130"},"modified":"2025-01-02T11:24:22","modified_gmt":"2025-01-02T11:24:22","slug":"shugaban-gwamnatin-sudan-ya-ce-ba-zai-yiwu-rsf-ta-koma-matsayinta-na-baya-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4130","title":{"rendered":"Shugaban Gwamnatin Sudan ya ce ba Zai Yiwu RSF ta Koma Matsayinta na Baya ba"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban gwamnatin ri\u0199on \u0199waryar Sudan ya ce ba zai yiwu ba rundunar RSF ta koma matsayin da take kafin a fara ya\u0199i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abdel Fattah al-Burhan ya yi wannan kalaman ne ranar Talata a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na \u0199asar Sudan domin murnar cika shekara 69 da samun \u2018yancin kan \u0199asar daga Birtaniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai kuma ya bayyana cewa zai &#8220;shiga duk wani shiri da zai kawo \u0199arshen ya\u0199in tare da tabbatar da dawowar fararen-hula gidanjensu cikin aminci.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Yanayin ba zai koma yadda yake kafin ranar 15 ga watan Afrilu 2023 ba kuma ba za mu yarda da kasancewar wa\u0257annan masu kisan kai da laifuka da magoya bayansu a cikin al&#8217;ummar Sudan ba,&#8221; a cewar Burhan a lokacin da yake magana kan RSF.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa maya\u0199an RSF suna gana wa mutanen Sudan u\u0199ubar kisa da yunwa da kuma gudun hijira.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya\u0199in basasar Sudan<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kimanin mutane 25,000 ne aka kashe kuma aka raba miliyan goma da gidajensu tun watan Afrilun shekarar 2023 a lokacin da aka fara ya\u0199in neman iko tsakanin sojin Sudan \u0199ar\u0199ashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da rundunar RSF \u0199ar\u0199ashin mataimakinsa a wancan lokacin, Mohamed Hamdan Dagalo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya\u0199in ya watsu zuwa jihohi 13 cikin 18 na \u0199asar Sudan, lamarin da ya janyo bala\u2019in lalata abubuwa da kuma tura miliyoyin mutane cikin yunwa da mutuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jerin \u0199o\u0199arin shiga-tsakani da wasu \u0199asashe suka jagoranta ciki har da Amurka da Saudiyya bai yi nasarar tabbatar da tsagaita wuta ba tukunna yayin da \u0253angarorin sojin Sudan da RSF ke zargin juna da yi wa yun\u0199urin sulhu zagon \u0199asa. TRT Africa Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban gwamnatin ri\u0199on \u0199waryar Sudan ya ce ba zai yiwu ba rundunar RSF ta koma matsayin da take kafin a fara ya\u0199i. &nbsp; Abdel Fattah al-Burhan ya yi wannan kalaman ne ranar Talata a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na \u0199asar Sudan domin murnar cika shekara 69 da samun \u2018yancin kan \u0199asar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4131,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4130","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4130","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4130"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4130\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4132,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4130\/revisions\/4132"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4131"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4130"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4130"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4130"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}