{"id":4111,"date":"2024-12-30T16:57:55","date_gmt":"2024-12-30T16:57:55","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4111"},"modified":"2024-12-30T16:57:55","modified_gmt":"2024-12-30T16:57:55","slug":"aljeriya-ta-bu%c6%99aci-faransa-ta-amince-ta-aikata-laifuka-a-lokacin-mulkin-mallaka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4111","title":{"rendered":"Aljeriya ta Bu\u0199aci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya \u0199addamar da wata sabuwar caccaka kan Faransa dangane da tasirin da mulkin mallakar da \u0199asar ta yi wa Aljeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya caccaki Faransar ne a lokacin da ya gudanar da jawabi ga \u0199asar a gaban duka majalisun \u0199asar inda ya gabatar da irin nasarorin da ya samu a wa&#8217;adinsa na farko na shugabancin \u0199asar tsakanin 2019 zuwa 2024 da kuma \u0199ara fitar da manufofinsa a wa&#8217;adinsa na biyu wanda ya fara a wata Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tebboune ya bayyana cewa Aljeriya na so Faransa ta amince da irin laifukan da ta aikata a lokacin mulkin mallaka tsakanin 1830 zuwa 1962, inda ta jaddada cewa \u0199asar ba ta bu\u0199atar wata diyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Muna neman dawo da mutuncin kakanninmu,&#8221; in ji shi<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8216;Yan Aljeriya da aka kashe<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Adadin &#8216;yan Aljeriya da aka kashe a tsawon shekara 132 na mulkin mallaka ya kai miliyan 5.6, kuma babu adadin ku\u0257in da za a biya da za su kasance diyyar ko da mutum \u0257aya da aka kashe a lokacin gwagwarmayar,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa da ya \u0253arke tsakanin Aljeriya da Faransa, lamarin da ya kai ga janye jakadan Aljeriya tare da kiran jakadan Faransa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumomin Aljeriya sun danganta wannan tashin hankalin da &#8220;mugayen ayyuka da jami&#8217;an leken asirin Faransa na kasashen waje suka aikata a kasar Aljeriya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tebboune ya kuma tuno da irin ta&#8217;asar da sojojin Faransa &#8216;yan mulkin mallaka suka aikata, musamman a karkashin Janar Thomas Robert Bugeaud, gwamnan-Janar na Aljeriya daga 1841-1847, wanda ya bayyana a matsayin &#8220;kisan kare dangi.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa har yanzu Faransa na ri\u0199e da kawunan \u0199warangal fiye da 500 na &#8216;yan Aljeriya wa\u0257anda ta fille wa kai a \u0199arni na 19 inda aka kai kawunan Paris.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mun yi \u0199o\u0199arin kar\u0253o kawuna 24 kacal,&#8221; kamar yadda ya bayyana.TRT Africa Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>M.B.Gama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya \u0199addamar da wata sabuwar caccaka kan Faransa dangane da tasirin da mulkin mallakar da \u0199asar ta yi wa Aljeriya. &nbsp; Ya caccaki Faransar ne a lokacin da ya gudanar da jawabi ga \u0199asar a gaban duka majalisun \u0199asar inda ya gabatar da irin nasarorin da ya samu a wa&#8217;adinsa na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":4112,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4111","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4111","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4111"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4111\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4113,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4111\/revisions\/4113"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4112"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4111"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4111"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4111"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}