{"id":4027,"date":"2024-12-14T10:51:09","date_gmt":"2024-12-14T10:51:09","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4027"},"modified":"2024-12-14T10:52:11","modified_gmt":"2024-12-14T10:52:11","slug":"abun-da-ya-faru-a-kasar-suriyah-dalilan-sa-siyasar-sa-da-yadda-ya-kamata-a-fahimce-shi-4","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4027","title":{"rendered":"ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH &#8211; DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (4)."},"content":{"rendered":"<p>KUNGIYOYIN DA SUKA YI ADAWAR KIFAR DA BASSHAR ASSAD A 2011.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mun yi bayanin yadda yakin basasa ya barke a 2011 tsakanin gwamnatin Basshar Assad da &#8216;yan adawar shi masu neman sauyi na siyasa da na tattalin arziki. Yakin ya barke ne saboda Basshar ya ki aminta da yin kowane irin gyara da &#8216;yan adawar suka bukata, sannan ya dauki matakin amfani da karfin tsiya don kawo karshensu, har ta sa su ma suka dauki makamai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ba da dadewa ba da fara yakin sai ta bayyana cewar &#8216;yan adawa za su fi karfin gwamnati su yi nasara a kanta. Daga nan ne kasashen waje suka shigo cikin yakin, kowace kasa da irin tata kalar siyasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kafin mu duba wadannan kasashen da siyasarsu zamu fara duba yanayin &#8216;yan adawar:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8216;YAN ADAWA: Kungiyoyin adawa da suka hadu suka daura yaki da gwamnatin Basshar su ne kamar haka:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>1 . Kungiyar Sojoji &#8216;Yan Tawaye: Duk da yake manyan kwamandodin sojan kasar Suriyah &#8216;yan Alawiyya ne, mafi yawan sauran sojojin kasar Ahlus Sunnah ne. Wannan ya sa suka gaji da umarnin da ake ba su kullum a lokacin zanga &#8211; zangar &#8216;yan adawa, na kashewa da raunata &#8216;yan uwansu. Wannan ya sa suka fara tawaye suna kaurace wa aikin soja. Da suka fara yawa sai suka hada kungiya da sunan &#8221; &#8216;Yantattun Sojojin Suriyah&#8221;. Kasar Turkiya ta ba su mafaka, daga inda suka fara kai hari da makamai ga kasar ta Suriyah. A hankali suka kwaci wani bangare na kasar, suka dawo nan suka kafa hedikwata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>2 . Jam&#8217;iyyar Neman &#8216;Yancin Suriyah: Wannan Jam&#8217;iyyar siyasa ce da ta kunshi mafi yawan kungiyoyin adawa na Suriyah masu son kawar da Basshar daga mulki, wadanda suka hada da kungiyoyin &#8216;yan kishin kasa da masu kishin addini kamar &#8216;yan Ikhwanul Muslimun. Sun yi meeting na farko a kasar Katar. Da yake ba su da makamai sai suka amince da hadewa da kungiyar sojoji &#8216;yan tawaye domin kayar da Basshar daga mulki. A nan ne suka sanar wa duniya cewar sun kafa sabuwar gwamnatin Suriyah mai gudun hijira, suka kafa hedikwatarsu a Turkiya kafin daga baya su dawo cikin Suriyah. Wannan sabuwar gwamnatin &#8216;yan tawaye ta samu amincewa da taimako daga kasar Turkiya da kasar Amerika da dukkan kasashen Turawa da dukkan kasashen Larabawa, kowa ya yarda a kifar da Basshar a maye gurbin shi da wannan sabuwar gwamnatin. A taron kasashen Larabawa da aka yi a Saudi Arabia a lokacin an hana wakilin gwamnatin Basshar halarta, aka maye gurbin sa da wakilin gwamnatin &#8216;yan tawaye nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>3 . Jam&#8217;iyyar Demokoradiyya ta Kurdawa: Su ma Kurdawan kasar Suriyah sun yi amfani da wannan yanayin na rashin zama lafiya a kasar suka shiga gwagwarmayar neman gwamnatin Basshar ta fadi, kasar ta waste su samu &#8216;yancin kafa tasu kasa ta Kurdawa zalla.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>4 . ISIS: Sai kuma kungiyar ISIS karkashin jagorancin Abubakar Al &#8211; Bagdadi wadda ta yi amfani da wannan yanayin ta kwace wani yanki mai girma na Suriyah, ta hada da wani yanki na Irak, ta samar da sabuwar kasa da ta kira &#8220;Daular Musulunci&#8221;. Duk yankunan da ISIS ta karbe a Suriyah da Irak din bangaren Kurdawa ne na Suriyah da na Irak.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>5 . Kungiyar An &#8211; Nusrah: Da farko wannan kungiya ta na tare da kungiyar Al &#8211; Ka&#8217;idah, sai ta koma tare da ISIS. Daga nan ta yanke ta koma cin gashin kanta. Tana karkashin jagorancin Abu Muhammad Al &#8211; Jolani, wanda shine yanzu ya jagoranci wannan yunkurin da ya kifar da Basshar. Da kungiyar ta koma cin gashin kanta sai ta canja sunan ta zuwa &#8220;Hai&#8217;atu Tahriris Sham&#8221;, watau Kungiyar Neman &#8216;Yancin kasar Sham (ma&#8217;ana Suriyah) kenan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wadannan su ne manyan kungiyoyin da suka hada adawar kasar Suriyah a 2011 domin kifar da gwamnatin Basshar Assad, tare da kananan kungiyoyi da yawa da suka shige cikinsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai kuma rawar da kasashen waje suka taka, amma sai a darasi na gaba in sha Allahu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>11\/06\/1446<\/p>\n<p>13\/12\/2024<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>KUNGIYOYIN DA SUKA YI ADAWAR KIFAR DA BASSHAR ASSAD A 2011. &nbsp; Mun yi bayanin yadda yakin basasa ya barke a 2011 tsakanin gwamnatin Basshar Assad da &#8216;yan adawar shi masu neman sauyi na siyasa da na tattalin arziki. Yakin ya barke ne saboda Basshar ya ki aminta da yin kowane irin gyara da &#8216;yan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3996,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[62,59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4027","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-books-journal","8":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4027","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4027"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4027\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4028,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4027\/revisions\/4028"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3996"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4027"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4027"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4027"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}