{"id":4012,"date":"2024-12-12T11:07:43","date_gmt":"2024-12-12T11:07:43","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4012"},"modified":"2024-12-12T11:07:43","modified_gmt":"2024-12-12T11:07:43","slug":"abun-da-ya-faru-a-kasar-suriyah-dalilan-sa-siyasar-sa-da-yadda-ya-kamata-a-fahimce-shi-3","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=4012","title":{"rendered":"ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH &#8211; DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (3)."},"content":{"rendered":"<p>GUGUWAR NEMAN SAUYI TA AR &#8211; RABI&#8217;UL ARABI<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mun yi bayani cewar wannan juyin juya hali da ya faru a kasar Suriyah ya faro ne daga guguwar neman sauyi da ta kada a cikin kasashen Larabawa a shekarar 2011.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan guguwar ta fara ne daga kasar Tunisiya inda matasa suka fara zanga &#8211; zangar neman sauyi da &#8216;yanci daga mulkin kama karya da danniya da shugabannin kasar ke yi masu, da kuma neman mafita daga matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta fada ciki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matasan sun yi amfani da kafofin sadarwa na social media wurin zaburar da magoya baya a ko ina a cikin kasar. To kuma ta wadannan kafafen ne, da kuma tashohin talabijin da ke kan satellite duniya ta rika bibiyar abun da ke faruwa a Tunisiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da haka ne matasa a sauran kasashen Larabawa su ma suka fara zanga &#8211; zangar neman sauyi, kamar a Libya, Morokko, Aljeriya, Masar, Suriyah da Oman.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A kowace kasa matasa su ne suka fara zanga &#8211; zangar amma daga baya kungiyoyi masu kishin addini suka shiga ciki 1suka samar da jam&#8217;iyyun siyasa, musamman a karkashin jagorancin kungiyar Ikhwanul Muslimun, in banda a Oman inda &#8216;yan shi&#8217;ar kasar suka yi jagoranci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamar yadda muka sani wannan yunkurin ya yi nasarar kafa gwamnati a Tunisiya da Masar, ya samu rinjaye a majalisun dokokin kasashen Morokko, Jordan da Kuwait. A Aljeriya ya samu wakilai da yawa a cikin gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai kasantuwar masu kishin addini ne suka kafa gwamnati a Tunisiya da Masar bai yiwa turawa dadi ba. Su ma shugabannin kasashen Larabawa ba su ji dadin a ce wasu sun yi zanga &#8211; zanga sun kifar da gwamnati ba, balle a ce masu kishin addini ne.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan shi ya sa turawa da shugabannin kasashen Larabawa suka hada karfi suka yi amfani da soja domin yin juyin mulki, suka yi amfani da wasu malamai domin yakar fikirorin masu kishin addini , musamman Ikhwanul Muslimun, tare da kiransu &#8216;yan ta&#8217;adda da khawarijawa, suka rusa gwamnatin da aka samu a Masar, sannan a Tunisiya. A Morokko kuma aka tarwatsa rijayensu a majalisa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Suriyah masu zanga &#8211; zangar lumana sun fito domin neman gwamnatin Basshar Assad ta daina kama karya da danniyar da marasa rinjaye suke yiwa masu rinjaye, a ba mutane dama su zabi shugabannin da su ke so a zabe na gaskiya da babu magudi a cikin shi. Su ma a Suriyah kungiyoyi ne na Ahlus Sunnah suka fito domin neman &#8216;yanci daga danniyar &#8216;yan Alawiyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Nan take kuwa sai Basshar Assad ya umarci jami&#8217;an tsaro da su yi amfani da karfin tsiya domin murkushe wadanda ya kira &#8216;yan tawaye. A duk kasashen da aka yi yunkurin Rabi&#8217;ul Arabi gwamnatocinsu sun yi amfani da karfi domin su murkushe yunkurin, su ceci kansu. Amma babu inda aka yi amfani da karfin tsiya wanda ya jawo hasarar rayukka masu yawa kamar Suriyah.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai wadannan &#8216;yan adawa ga gwamnatin Basshar Assad ba shirye suke a fi karfinsu ba. Shi kuma Basshar Assad ba shirye ya ke ya yi ko da wasu canje -canje ba, balle ya sauka daga mulki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga karshe dai da tsanani ya yi yawa a kan &#8216;yan adawa sai su ma suka dauki makamai, abun ya tashi daga yunkurin lumana ya zama yakin basasa. Ba da jimawa ba &#8216;yan adawar suka dauko hanyar yin nasara a kan sojojin Basshar Assad, sai dai siyasar kasashen duniya da ke gudana a kasar ba ta bari hakan ta faru ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan siyasa da ta faru a cikin yakin basasar Suriyah ita ce zamu yi magana a kai a darasi na gaba in sha Allahu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>10\/06\/1446.<\/p>\n<p>12\/12\/2024.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>GUGUWAR NEMAN SAUYI TA AR &#8211; RABI&#8217;UL ARABI &nbsp; Mun yi bayani cewar wannan juyin juya hali da ya faru a kasar Suriyah ya faro ne daga guguwar neman sauyi da ta kada a cikin kasashen Larabawa a shekarar 2011. &nbsp; Wannan guguwar ta fara ne daga kasar Tunisiya inda matasa suka fara zanga &#8211; [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3996,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-4012","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4012","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4012"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4012\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4013,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4012\/revisions\/4013"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3996"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4012"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4012"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4012"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}