{"id":3995,"date":"2024-12-11T13:32:42","date_gmt":"2024-12-11T13:32:42","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3995"},"modified":"2024-12-11T13:32:42","modified_gmt":"2024-12-11T13:32:42","slug":"abun-da-ya-faru-a-kasar-suriyah-dalilan-sa-siyasar-sa-da-yadda-ya-kamata-a-fahimce-shi-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3995","title":{"rendered":"ABUN DA YA FARU A KASAR SURIYAH &#8211; DALILAN SA, SIYASAR SA DA YADDA YA KAMATA A FAHIMCE SHI (2)."},"content":{"rendered":"<ol>\n<li>SIYASAR KASASHEN WAJE A CIKIN SURIYAH A ZAMANIN HAFIZ ASSAD DA DAN SA BASSHAR.<\/li>\n<\/ol>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babban abin da ya yi sanadiyyar wannan juyin juya hali na yanzu a Suriyah shine abubuwan da suka faru a lokacin guguwar neman sauyi ta Ar-rabi&#8217;ul Arabi ta 2011.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Su kuma abubuwan da muka yi bayani na siyasar cikin gida a darasi da ya gabata su ne suka yi sanadiyyar yunkurin Ar-rabi&#8217;ul Arabi a Suriyah.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kafin mu yi bayanin yunkurin Rabi&#8217;ul Arabi za mu yi bayani game da irin siyasar da kasashen waje ke takawa a cikin Suriyah kafin shi, domin ita ce abinda ya sa yunkurin Rabi&#8217;ul Arabi ya karata yadda ya karata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>FARANSA: kamar yadda muka yi bayani a baya, Faransa ita ce ta yiwa kasar Suriyah mulkin mallaka bayan yanke ta daga jikin sauran kasashen Larabawa . Siyasar kasar Faransa ita ce ta daukaka alawiyyawa wadanda suke kashi goma cikin dari ko kasa da haka bisa ga musulmi Sunni wadanda su ke 74% na jama&#8217;ar kasar. Wannan shi ya haifar da mulkin Hafiz Assad da dansa Basshar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>MASAR: Masar a zamanin Jamal Abdun Nasir ita ce ta shigar da siyasar jam&#8217;iyyar Ba&#8217;ath cikin Suriyah. Wannan ya haifar da mulkin jam&#8217;iyya daya tilo wadda ta ke fada da Addinin musulunci. Mulkin jam&#8217;iyya daya tilo kuma shine ya haifar da mulkin kama karya da gado da danniyar wasu jama&#8217;ah a kan wasu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>RASHA: Tsarin jam&#8217;iyyar Ba&#8217;ath shi ya jawo dangantaka ta kut da kut tsakanin Suriyah da Rasha. Da ake yakin ruwan sanyi (cold war) tsakanin Rasha da kasashen yamma Suriyah tana gefen Rasha. Ko da Rasha ta rushe sauran kasashen Larabawa suka rabu da ita amma Hafiz da dansa sun ci gaba da dangantaka da Rasha har zuwa yanzu da Basshar ya fadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>AMERIKA DA ISRA&#8217;ILA: Tun lokacin da yahudawa suka kwace Falasdin a shekarar 1948 Suriyah tana tare da sauran kasashen Larabawa karkashin jagorancin Masar domin yakar yahudawa da &#8216;yanto Falasdin. Amma wadannan yakoka sun yi su ba da sunan addini ba sai dai don kishin kabilar Larabawa. Ita kuma Amerika tare da sauran kasashen Turai suka shigar wa Isra&#8217;ila. Sai dai a cikin wadannan yakoka Larabawa sun kwashi kashinsu a hannun. A yakin 1967 Suriyah ta yi hasarar yankin ta na tsaunukan Julan (Golan Heights) ga yahudawa. Don haka Hafiz da dansa Basshar sun dauki Isra&#8217;ila makiyiyarsu ta dindindin, tare da duk masu taimaka mata, irin Amerika da kasashen Turai, amma ba don kishin musulunci ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>IRAN: A shekarar 1978 Ayatullahi Kumaini ya yi juyin juya hali a Iran. Kumaini ya dauki matakai biyu da suka sa dangantakar shi da Suriyah ta yi karfi. Na farko ya nuna yardar shi da &#8216;yan Alawiyya cewa su ma bangare ne na shi&#8217;ah sabanin matsayin Malaman shi&#8217;ah inda aka fito cewa su gullatu ne (wadanda suka wuce gona da iri). Na biyu fadan shi da Amerika ya sa ya yi yekuwar yin fada da Isra&#8217;ila wadda ita ce wakiliyar Amerika a Gabas ta tsakiya. Kumaini ya yi yekuwar &#8216;yanto masjidul Aksa, inda ya umarci kasashe da su kafa rundunar Hizbullahi domin wannan aiki. A wannan fada da Isra&#8217;ila sai manufar Iran da ta Suriyah ta zo daya. Wannan ya sa Suriyah ta yarda Iran ta yi amfani da kasarta domin fada da Isra&#8217;ila da Amerika, ita kuma Iran ta dauki nauyin ba da kariya ga gida da mulkin Hafiz da dansa Basshar. Rikicin Iran da Amerika ya jawo sauran kasashen Larabawa wadanda duk mabiya Amerikar ne suka shiga rikici da Iran din a madadin ita Amerikar, amma suna yin hakan ne da sunan fada da yaduwar shi&#8217;anci. Wannan ya sa ita Iran ta yi kokarin hada karfin duk &#8216;yan shi&#8217;ar da ke cikin yankin tekun Fasha da basu makamai da horo don ta yi amfani da su a cikin wannan jayayya. Kasar Suriyah ta taka wa Iran rawa mai karfi a cikin hakan, domin ita ce kawai kasar da ke hannun gwamnatin &#8216;yan shi&#8217;a gaba daya a lokacin in ban da ita Iran din. Sai daga baya ne kasar Irak da rabin kasar Yaman suka koma karkashin mulkin shi&#8217;ah yayin da Iran din, tare da goyon bayan Suriyah, ta taimaka wa kungiyar Hizbullahi a Lebanon ta zama gwamnati cikin gwamnati .<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wadannan su ne siyasoshin kasashen waje da ke taka rawa a cikin Suriyah ya zuwa lokacin da guguwar Rabi&#8217;ul Arabi ta kada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Zamu ci gaba in sha Allahu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>9\/6\/1445.<\/p>\n<p>11\/12\/2024.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>SIYASAR KASASHEN WAJE A CIKIN SURIYAH A ZAMANIN HAFIZ ASSAD DA DAN SA BASSHAR. &nbsp; Babban abin da ya yi sanadiyyar wannan juyin juya hali na yanzu a Suriyah shine abubuwan da suka faru a lokacin guguwar neman sauyi ta Ar-rabi&#8217;ul Arabi ta 2011. &nbsp; Su kuma abubuwan da muka yi bayani na siyasar cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3996,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3995","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3995","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3995"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3995\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3997,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3995\/revisions\/3997"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3996"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3995"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3995"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3995"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}