{"id":3954,"date":"2024-12-04T19:43:47","date_gmt":"2024-12-04T19:43:47","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3954"},"modified":"2024-12-04T19:43:47","modified_gmt":"2024-12-04T19:43:47","slug":"tirka-tirkar-gyaran-dokar-haraji-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3954","title":{"rendered":"TIRKA- TiRKAR GYARAN DOKAR HARAJI (2)"},"content":{"rendered":"<p>Daga karatunmu na jiya da gwamnoni da wasu &#8216;yan majalisa an samu sabani a fahimtar dokokin harajin da shugaban kasa yake son aiwatarwa. Daga bangaren PBAT suna son a yi muhawarar komai a majalisa, su kuma gwamnoni suna son a janye maganar kwata-kwata a sake dubawa idan na za a dawo da ita sai a sake gabatarwa. Duka raayoyin za a iya amfani da su.<\/p>\n<p>A fahimtar dana yi nan ne mutanen da suke ganin baiken Sanata BARAU I Jibrin suke da korafi. Tun da kuma a zamanin siyasa ne, dole a samu lauya magana. Tilas a samu yarfe, ka shiga ban dauka ba, ba ta hana zargin sata ga barawo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A hakikar magana laifin bangaren shugaban kasa ne. Alhakinsu ne su dauki duk wani mataki na wayar da kai da jawabi mai gamsarwa da saka duk wanda abin zai shafa cikin shaanin. Amma ba a yi ba, dole kuwa hakan ya jawo kace-nace. A&#8217; al&#8217;adar dimokuradiyya mai murhu guda uku, wata goma sha biyar kacal, ba a fita daga radadin cire Subsidy na PMS, haka kuma har zuwa yau, farashin dala karuwa yake, ita kuma Naira na dada karyewa, duk wani Policy na gwamnati in aka zo da shi sai a Slow.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A irin wannan yanayin Sanata BARAU ya taka sawun barawo. In BARAU bai dauki mataki ba na holistic Damage Control, an gama da shi a lissafin siyasa. Marigayi Atiku Abubakar ba dan ya mutu ba shi ne abin da ya gamu da shi a siyasa a 2002\/2003. A irin wannan yanayin mutanen arewa suka wanke Buhari da soso da sabulu har sai da suka dawo da shi da karfi kan mulkin Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Na karanta duk sadarorin da mutane suke da jayayya akansu, kuma na saurari jawaban masanan harajin da tattalin arziki kuma na nazarci yanayin da muke ciki a tsakanin Kudu da arewa ta fuskar siyasa da zamantakewa, dokokin suna da alfanu mai tarin yawa, akwai bukatar dokar ta wuce, amma sai an yi mata kwaskwarima mai yawan gaske, sai an tsince tsaba mai kyau sosai daga cikin, an ingantata, an watsar da tsakuwa mai hadari da ke cikinta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babban abin da yake bukatar mu sani shi ne, gwamnoni Najeriya da gudunmawar sarakai da suka fara tada kayar baya, babbar bukatarsu ta samun karin kudin shiga ita ce ta cewa zasu shiga damuwa a jihohinsu, an kara musu kudin Subsidy, an biyo ta wata hanyar za a kwace, dole kuwa su dau mataki suka yi caa da cincirindo lallai sai an dakatar da ita. Mun sani a baya ba haka suka yi ba a lokacin da aka cire Subsidy na PMS. A bara 2023 dukansu shiru suka yi suka kame bakunansu. Ta kai har zanga-zanga aka yi mummuna, amma babu wani a cikinsu da ya dagawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu hankali ko ya taka masa birki. Mu gane fa sarai Harajin VAT a shekarar 2017 yana kan 5% tsohon shugaban kasa Buhari ne ya mayar da shi 7.5% hakan ya jawo tashin farashin komai. Yanzu kuma a 2025 zai koma 10%, idan shekara ta zo ta 2026 zai koma 12.5%, daga nan har zuwa 2030 zai tafi har zuwa 15% sannan ya tsaya cik. BA wannan ce damuwar gwamnoni ba, a&#8217;a jihar Lagos da Rivers da Abuja sune zasu fi amfana ba jama&#8217;armu ta Najeriya ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>YAU MA MU KWANA NAN<\/p>\n<p>insha&#8217;Allah zan yi bayanin sosai akan me dokokin suka kunsa, ina alfanunsu kuma me ye abin zai shafe mu. Ku yi hakuri ku sake biyoni. Na yi jinkiri, jikin ne ya motsa. Ku saka ni cikin addua<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>@ Bello Muhammad Sharada<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid News<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga karatunmu na jiya da gwamnoni da wasu &#8216;yan majalisa an samu sabani a fahimtar dokokin harajin da shugaban kasa yake son aiwatarwa. Daga bangaren PBAT suna son a yi muhawarar komai a majalisa, su kuma gwamnoni suna son a janye maganar kwata-kwata a sake dubawa idan na za a dawo da ita sai a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3934,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3954","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3954","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3954"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3954\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3955,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3954\/revisions\/3955"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3934"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3954"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3954"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3954"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}