{"id":3756,"date":"2024-11-19T06:24:08","date_gmt":"2024-11-19T06:24:08","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3756"},"modified":"2024-11-19T06:24:08","modified_gmt":"2024-11-19T06:24:08","slug":"sa%c6%99on-da-mahamat-deby-ya-ce-mu-kawo-wa-tinubu-game-da-ya%c6%99i-da-boko-haram-nuhu-ribadu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3756","title":{"rendered":"Sa\u0199on da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da ya\u0199i da Boko Haram &#8211; Nuhu Ribadu"},"content":{"rendered":"<p>Sa\u0199on da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da ya\u0199i da Boko Haram &#8211; Nuhu Ribadu<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Chadi game da aikin ha\u0257in gwiwa a ya\u0199i da \u0199ungiyoyi masu i\u0199irarin jihadi a yankin Tafkin Chadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya fa\u0257a wa BBC cew a ya jagoranci tawagar ta&#8217;aziyya zuwa ga Shugaban Chadi Mahamat Idris Deby kan sojojinsa da \u0199ungiyar Boko Haram ta kashe a baya-bayan nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kisan sojojin kusan 40 ya sa Shugaba Deby ya yi barazanar ficewa daga rundunar Mutlinational Joint Taske Force (MNJTF) yayin da ya kai ziyara sansanin Barkaram &#8211; wani tsauni da ke yankin na Tafkin Chadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mun kai sa\u0199o ne daga shugabanmu Bola Tinubu, ya ba mu takarda mu kai wa shugaban Chadi domin mu jajanta masa saboda duk abin da ya samu Chadi ya shafi Najeriya,&#8221; a cewar Nuhu Ribadu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198asashen Najeriya, da Nijar, da Chadi, da Kamaru, da Benin ne ke yin karo-karon dakaru a rundunar, kuma masana na cewa barazanar da shugaban Chadi ya yi ka iya yin illa ga \u0199ungiyar mai shekara 10 da kafuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ribadu ya ce sun shafe kusan awa uku suna tattaunawa da shugaban na Chadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mun yi maganganu masu ma&#8217;ana \u0199warai, kuma za mu zauna da Shugaba Tinubu domin duba abubuwan da ya fa\u0257a mana, amma dai abin bai kai a ce za su janye ba. Za mu \u0199ara gyarawa.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ha\u0257akar sojin ta \u0199asashe biyar wadda ke da babban ofishinta a Chadi tana da dakaru kusan 10,000 a shekarar 2022.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A 2018 lokacin da \u0199ungiyar take da dakaru 8,000, Chadi ta bayar da 3,000 &#8211; mafi yawa bayan Najeriya wadda ta bayar da 3,250. Kamaru na da 2,250, sai Nijar mai sojoji 200, yayin da Benin ta kasance ta \u0199arshe da sojoji 150, kamar yadda wani rahoto na makarantar nazarin harkokin soji ta \u0199asa da \u0199asa da ke Kamaru ta fitar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Game da barazanar, Mahamat ya ce \u0199ungiyar ta hadin gwiwar soji ba ta da wani &#8220;kyakkyawan tsari&#8221; na gudanar da ayyukanta tare wajen ya\u0199ar Boko Haram &#8211; saboda haka ne ya ce \u0199asar na duba yuwuwar ficewa daga ha\u0257akar da ke aikin tabbatar da tsaro a yankin da ya kasance wata cibiya da \u0199ungiyoyi masu makamai ke addabar \u0199asashen hu\u0257u.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai Ribadu ya ce Najeriya za ta \u0199ara \u0199aimi a ya\u0199i da \u0199ungiyar Boko Haram.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Da yawansu [&#8216;yan Boko Haram] sun gudu sun shiga Chadi da Nijar, kuma na ga can ma an yi \u0199o\u0199ari sosai. Mu ma Najeriya muna shiri, abin ya isa haka &#8211; da yardar Allah ba za mu bari ba.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Farfesa Oumar Ba na cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya da dabaru a Faransa ya fa\u0257a wa BBC cewa yun\u0199urin Chadi na ficewa daga ha\u0257akar na nuna tarin matsalolin da \u0199ungiyar ke fuskanta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sa\u0199on da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da ya\u0199i da Boko Haram &#8211; Nuhu Ribadu &nbsp; Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Chadi game da aikin ha\u0257in gwiwa a ya\u0199i da \u0199ungiyoyi masu i\u0199irarin jihadi a yankin Tafkin Chadi. &nbsp; Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3757,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3756","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3756","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3756"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3756\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3758,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3756\/revisions\/3758"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3757"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3756"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3756"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3756"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}