{"id":3672,"date":"2024-11-12T17:11:26","date_gmt":"2024-11-12T17:11:26","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3672"},"modified":"2024-11-12T17:11:26","modified_gmt":"2024-11-12T17:11:26","slug":"tai-da-baykar-na-turkiyya-na-daga-cikin-manyan-kamfanonin-%c6%99era-jiragen-sama-50-na-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3672","title":{"rendered":"TAI da Baykar na Turkiyya na daga cikin manyan kamfanonin \u0199era jiragen sama 50 na duniya"},"content":{"rendered":"<p>Kamfanonin \u0199era Jiragen Sama na Turkiyya TAI da Baykar sun shiga cikin jerin manyan kamfanoni 50 mafi girma a duniya bisa kuda\u0257en shigarsu na shekarar 2023, a cewar rahoton FlightGlobal.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sashen kula da sararin samaniyar Turkiyya ya samu wani gagarumin ci gaba mai cike da tarihi, inda kamfanonin \u0199asar biyu da ke \u0199era jiragen sama wato TAI da Baykar suka shiga jerin manyan kamfanonin jiragen sama 50 na duniya, bisa ga ki\u0257iddigar ku\u0257a\u0257en shigarsu ta shekarar 2023 wadda hukumar le\u0199en asiri ta Counterpoint Market na FlightGlobal ta fitar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamfanin TAI na matsayi na 38, inda ya ba da rahoton samun dala biliyan 2.67 na ku\u0257a\u0257en shigarsa, yayin da Baykar ke a matsayi na 49 da dala biliyan 1.8.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matsayin TAI na 38 na nuna irin ci gaba da ya ke samu, inda ya samar jiragen masu saukar angulu \u0199irar ANKA lll, da HURJET da kuma jirgin ya\u0199i na KAAN.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>TAI ya fice wajen samar da manyan fasahohi na zamanin tare da ci gaba a fannin bincike, da kuma mayar da hankali wajen fitarwa da kuma samar da tsarin samfuran fasahohi ga manyan kamfanonin jiragen sama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ha\u0257in gwiwar kamfanin tare da fitattun kamfanoni a harkar kusawancin jiragen sama masu zaman kansu da na sojoji a duniya ya karfafa masa yin fice.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Baya ga manyan samfuran kayayyakin tsaro da yake samarwa, ha\u0257in gwiwar TAI da sauran kamfanoni masu zaman kansu a fannin jiragen sama ya \u0199arfafa rawar da ya ke takawa a matsayin mai mahimmanci wajen samar da manyan fasahohi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matsayin Baykar na farko a jerin<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Baykar, wani babban kamfani ne a fannin kasuwanin kera jirage marasa matu\u0199i (UAV), yana matsayi na 49 a jerin inda kudaden shigar da ya samu a 2023 ya kai dala biliyan 1.8.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107.jpg\"><img loading=\"lazy\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter size-medium wp-image-3674\" src=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107-300x161.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"161\" srcset=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107-300x161.jpg 300w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107-1024x548.jpg 1024w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107-768x411.jpg 768w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107-860x460.jpg 860w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/11\/IMG-20241112-WA0107.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/a><\/p>\n<p>Ya yi fice a samfurin jirginsa na Bayraktar TB2, kazalika kamfanin ya yi suna wajen fitar da jiragen yaki marasa matuki a duniya, tare da fasaharsa da ake bu\u0199ata a duk fa\u0257in duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Baykar ya sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da kayayyakinsu zuwa kasashe 35 kan samar da jiragensa \u0199irar Bayraktar TB2 da Bayraktar AKINCI UAVs\u0199<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fiye da kashi 90 cikin 100 na kuda\u0257en da kamfanin ya samu ya fito ne daga fitar da kayayyakinsa zuwa \u0199asashen duniya, Baykar ba kawai ya tsaya wajen fayyace fannin tsaron Tukiyya ba ne, yana ri\u0199e da matsayinsa na babban kamfanin da ke fitar da kayyaykin tsaro na \u0199asar mai fitar a tsawon shekaru uku a jere.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dukka kamfanonin biyu, TAI da Baykar suna ci gaba da saka hannun jari a sabbin fasahohi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>TAI yana ci gaba da \u0199era jiragen yakinsa na KAAN, yayin da Baykar ke mai da hankali wajen samar da jiragen yaki marasa matuka \u0199irar Bayraktar TB3, da jirgin ruwa mai saukar ungulu \u0199irar UAV, da kuma Bayraktar Kizilelma da ake sa rai samarwa wato jirgin yaki na sama na farko na Turkiyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ci gaba a kasuwanin duniya<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matsayin dai, ya sanya TAI da Baykar a cikin jerin manyan kamfanoni kamar Boeing da Airbus, wa\u0257anda bi da bi suke kan gaba a jerin kuda\u0257en shigar kamfanonin \u0199era jiragen samana duniya da dala biliyan 77.8 da kuma dala biliyan 70.8.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Manyan kamfanonin da ke kan gaba a jerin sun fito ne daga Amurka da \u0199asashen Turai, yanayin da ke nuni da irin rinjayen da kamfanonin Amurka da na Turai a fannin sararin samaniya, musamman wa\u0257anda suka mayar da hankali wajen samar da fasahohin tsaro da na farar hula.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A bana dai, manyan kamfanoni irin su RTX, da Lockheed Martin, da Northrop Grumman suna ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin masana&#8217;antar tsaron Amurka a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ko da yake, bayyanar kamfanoni irin su Baykar da TAI na nuna sauyin da ake samu a wannan \u0253angare, inda kamfanonin wa\u0257anda ba na \u0199asashen Yammacin Turai ba suke shiga jerin da kamfanonin \u0199asashen Yamma suka mamaye.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kamfanonin \u0199era Jiragen Sama na Turkiyya TAI da Baykar sun shiga cikin jerin manyan kamfanoni 50 mafi girma a duniya bisa kuda\u0257en shigarsu na shekarar 2023, a cewar rahoton FlightGlobal. &nbsp; Sashen kula da sararin samaniyar Turkiyya ya samu wani gagarumin ci gaba mai cike da tarihi, inda kamfanonin \u0199asar biyu da ke \u0199era jiragen [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3673,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3672","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3672","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3672"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3672\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3675,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3672\/revisions\/3675"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3673"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3672"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3672"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3672"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}