{"id":3651,"date":"2024-11-12T06:07:34","date_gmt":"2024-11-12T06:07:34","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3651"},"modified":"2024-11-12T06:07:34","modified_gmt":"2024-11-12T06:07:34","slug":"najeriya-ta-halarci-taron-kasashan-musulmai-na-duniya-domin-tabbatar-da-tsagaita-wuta-a-gabas-ta-tsakiya-da-kuma-tabbatar-da-kasashe-gaza-da-israila","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3651","title":{"rendered":"Najeriya ta Halarci Taron Kasashan Musulmai na Duniya Domin Tabbatar da Tsagaita Wuta a Gabas ta Tsakiya da Kuma Tabbatar da Kasashe Gaza da Isra&#8217;ila."},"content":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron \u0199oli na \u0199asashen Musulmi da Larabawa.<\/p>\n<p>Taron wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.<\/p>\n<p>Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.<\/p>\n<p>Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin ya\u0257a labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra&#8217;ila da Falas\u0257inawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar tsagaita wuta nan take, tare da neman a sake farfa\u0257o da masalahar samar da \u0199asashe biyu masu cin gasin kansu wato Falas\u0257inu da Isra&#8217;ila.<\/p>\n<p>Ministan ya\u0257a labarai Mohammed Idris ya ce Najeriya ta halarci taron ne sabo da irin da\u0257a\u0257\u0257iyar ala\u0199a mai kyau da take da ita da yankin na Gabas ta Tsakiya.<\/p>\n<p>&#8220;Dole ne mu samar da hanyar diflomasiyya domin warware wannan rikicin, saboda ya\u0199i ba shi ne mafita ba,&#8221; kamar yadda ministan ya fa\u0257a wa manema labarai a birnin Riyadh. &#8220;Wannan shi muke bu\u0199ata a yi.&#8221;<\/p>\n<p>Ya ce Najeriya za ta kuma yi amfani da lokacin taron wajen nema &#8220;da babbar murya a idon duniya&#8221; bu\u0199atar dukkan \u0199asashe su cimma matsaya \u0257aya ta warware rikicin Isra&#8217;ila da Falas\u0257inu.<\/p>\n<p>&#8220;\u0198asashen biyu da ke rikici da juna na rasa abubuwa muhimmai, don haka Najeriya na ganin cewa muddin ba a samar da mafita ta diflomasiyya ba, rikicin zai iya shafar \u0257aukacin yankin, har ma da duniya baki \u0257aya.<\/p>\n<p>&#8220;Babu yadda Najeriya za ta zauna cikin kwanciyar hankali muddin ba a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba,&#8221; in ji Idris.<\/p>\n<p>Harin da Hamas ta kai wa Isra&#8217;ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya janyo mutuwar mutum a\u0199alla 1,200, da kuma yin garkuwa da kusan 251.<\/p>\n<p>Tun bayan nan, Isra&#8217;ila ta kaddamar da mamaya kan zirin na Gaza, inda ta kashe sama da mutum 43,000, wa\u0257anda yawancinsu mata ne da kuma \u0199ananan yara.<\/p>\n<p>Isra&#8217;ila ta sha alwashin ci gaba da farmaki a Gaza har sai ta ga bayan \u0199ungiyar Hamas da ke iko a Gaza.<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron \u0199oli na \u0199asashen Musulmi da Larabawa. Taron wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya. Tinubu ya samu tarba daga [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3652,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3651","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3651","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3651"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3651\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3653,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3651\/revisions\/3653"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3652"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3651"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3651"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3651"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}