{"id":3609,"date":"2024-11-05T17:34:46","date_gmt":"2024-11-05T17:34:46","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3609"},"modified":"2024-11-05T17:34:46","modified_gmt":"2024-11-05T17:34:46","slug":"soke-yunkurin-gyara-kundin-tsarin-mulki-domin-karfafa-shariah-da-majalisar-wakilai-ta-yi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3609","title":{"rendered":"SOKE YUNKURIN GYARA KUNDIN TSARIN MULKI DOMIN KARFAFA SHARI&#8217;AH DA MAJALISAR WAKILAI TA YI."},"content":{"rendered":"<p>Ranar 24\/10\/2024 rana ce ta bakin cikin ga kasar nan. Rana ce da ta nuna cewar shekaru ashirin da biyar da aka yi na demokoradiyya ba su iya samar da hakuri da juna da kasar nan ta ke bukata ba game da bambancin addini, wanda zai samar mata da zama lafiya mai dorewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wannan rana ce aka yi waje da kudurin da Hon. Aliyu Misau, dan majalisar PDP mai wakiltar mazabar Misau\/Dambam da ke Jihar Bauchi a Majalisar Wakilai ta kasa ya gabatar. Kudurin ya bukaci ne a yi kwaskwarima ga gyararren kundin tsarin mulki na 1999, domin a fadada hurumin kotunan daukaka kara na Shari&#8217;ar musulunci a matakin kasa da jihohi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kudurin ya bukaci a yi gyara ga sassa na 24, 262, 277 da 288 na tsarin mulkin domin a cire kalmar &#8220;personal&#8221;, daga jumlar da ke cewa &#8220;Islamic Personal Law&#8221;, duk inda aka kawo ta a cikin kundin tsarin mulkin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ma&#8217;ana shi tsarin mulkin ya bayar da dama ne kawai a yi wa musulmi hukunci da Shari&#8217;ar musulunci a abubuwan da suka shafi al&#8217;amurran zamantakewa da iyali, watau aure da hakkokin miji da mata da reno da saki da rabon gado. Wadannan su ake kira &#8220;Islamic Personal Law&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kudurin Hon. Aliyu Misau ya na kira da a ce &#8220;Islamic Law&#8221; kawai, a cire &#8220;Personal&#8221;. Idan aka yi haka zai zama kenan kotun Garandakadi tana da damar sauraren karar da aka daukaka zuwa gareta wadda ta shafi kowace matsala ta musulmi idan dai ba ta laifi ba ce (criminal case), ta yi hukunci na musulunci, a madadin a ce sai dai High Court kawai ke da wannan hurumin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ho. Aliyu Misau ya kawo misali cewar irin bankin Ja&#8217;iz da bankin Taj da ke kokarin bin tsarin kasuwanci na musulunci suna bukatar su kai karar rikice &#8211; rikicensu ga kotun Shari&#8217;ar musulunci. Amma idan akwai wannan kalmar &#8220;personal&#8221; ba za su iya ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abinda lura a nan shine: duk inda aka yi maganar Shari&#8217;ar musulunci a cikin dokokin kasar nan ana magana ne a kan musulmi kawai. Ba a taba kokarin yin wata doka ba da ta yi yunkurin dankara Shari&#8217;ar musulunci a kan wanda ba musulmi ba. Rashin yin aiki da cikakkar Shari&#8217;ar musulunci a kasar nan tauyewa ne ga hakkin mu musulmi na yin Addinin mu. Babu lokacin da yi wa musulmi Shari&#8217;ar musulunci za ta cutar da wadanda ba musulmi ba, ko ta jawo ma kasa wata illa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma dai a hakan wani gungu na kiristoci, karkashin jagorancin wani da ya yi ridda daga musulunci ya koma kirista, wai shi Bamidele Salam suka nace sai da aka yi watsi da wannan kuduri karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar wanda shi ma kirista ne mai suna Beni Kalu ta hayar kawai cewa &#8220;e&#8221; da &#8220;a&#8217;a&#8221;. Babu yadda za a dubi wannan aiki in ban da a ce kiyayyaya ce ta addini da tsaurin ra&#8217;ayi da rashin kulawa da bukatun abokan zama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>To amma ya kamata mu yi tambaya a nan. Musulmi sun fi kirista yawa ko da da kadan ne a Majalisar Wakilai. To duk ina wadannan musulmin lokacin da aka yi wannan ta&#8217;asar? Ina shugaban majalisar wanda shi musulmi ne?<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan ya sa ni na ke da ra&#8217;ayin cewa ba ma kirista ne suka yi mana yankan kauna ba, musulmi ne &#8216;yan uwanmu, wakilan mu, suka yi mana, ko dai saboda sun tafi harkokin gaban kansu sun ki halartar zaman majalisa har aka fi su yawa, ko kuma su ma sun goya baya ne a yi watsi da wannan kuduri.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Modibbon Gusau.<\/p>\n<p>5\/11\/2024<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ranar 24\/10\/2024 rana ce ta bakin cikin ga kasar nan. Rana ce da ta nuna cewar shekaru ashirin da biyar da aka yi na demokoradiyya ba su iya samar da hakuri da juna da kasar nan ta ke bukata ba game da bambancin addini, wanda zai samar mata da zama lafiya mai dorewa. &nbsp; A [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3607,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[62,59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3609","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-books-journal","8":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3609","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3609"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3609\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3610,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3609\/revisions\/3610"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3607"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3609"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3609"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3609"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}