{"id":3603,"date":"2024-11-05T05:17:54","date_gmt":"2024-11-05T05:17:54","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3603"},"modified":"2024-11-05T05:18:05","modified_gmt":"2024-11-05T05:18:05","slug":"gomnatin-kano-zata-fara-yiwa-baki-rijistar-zama","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3603","title":{"rendered":"GOMNATIN KANO ZATA FARA YIWA BAKI RIJISTAR ZAMA"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano ta da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamitin \u0199wararru da zai yi aikin yiwa ba\u0199i \u01b4an \u0199asashen waje mazauna birnin rijista musamman wa\u0257anda suke gudanar da kasuwanci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnati ta ce ta \u0257auki matakin ne domin samun al\u0199aluman mutanen da suka fito daga \u0199asashen \u0199etare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, ta yadda za a ha\u0253\u0253aka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamitin wanda ke \u0199ar\u0199ashin ofishin sakataren gwamnatin Kano, zai tattara bayanan ba\u0199i \u01b4an \u0199asashen waje da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma\u2019aikata ko kuma kasuwanci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban kwamitin, Lawan Isa Kibiya ya ce aikin da za su yi zai taimaka wajen tabbatar da ganin ba\u0199in wa\u0257anda mafi yawa \u01b4an kasuwa ne su na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa hakan zai bai wa gwamnati \u0199warin gwiwar \u2018\u2018\u0199o\u0199arin ganin ta samar da yadda za ta ba su kariya ta fuskar tsaro\u2019\u2019<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinan ma\u2019aikatar ciniki ta jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya wanda manba ne a kwamtin ya ce \u2018\u2018aikin bai ta\u0199aita ga bu\u0199atar tattara haraji ka\u0257ai ba, duk duniya akwai \u0199a\u2019idoji da aka kafa a doka, wa\u0257anda idan ba\u0199o ya je zai yi kasuwanci ga \u0199a\u2019idojin da ya kamata ya bi, sannan su ma \u01b4an gari ga \u0199a\u2019idojin da ya kamata su bi.\u2019\u2019<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa \u2018\u2018idan ka shiga wannan manyan kasuwannin namu, musamman kantin kwari, za ka ga ba\u0199in su ne mafi yawa ke \u0199erawa, su yi packaging su kuma yi kasuwanci kai tsaye.\u2019\u2019<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Adamu Kibiya, ya kara da cewa ire-iren wa\u0257annan abubuwan gwamnati ta kalla shi yasa ake \u0199o\u0199arin fito da tsarin da zai taimaki al\u2019umma musamman wajen samar da ayyuka da kare martabar kasuwanci: \u2018\u2018Idan muka zura ido mu ka yi gaba to zai zamo nan gaba mun koma maula, mutanen mu sun koma bara. Don haka gwmanati ta duba, ta ga dole wannan abubuwa a taka masu birki.\u2019\u2019<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa tsarin zai tsaftace harkokin kasuwanci a jihar, musamman yadda aka saba samun masu yi wa \u01b4an kasuwa zambo domin kwashe masu ku\u0257i, kuma ana samun irin wa\u0257annan bata gari masu aikata daga kowanne \u0253angare.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u2018\u2018Za ka ga ana kar\u0253ar kayansu da yawa ana cinyewa, kuma su ma daga cikin su ana samun masu cinye wa \u01b4an kasuwar Kano kaya ko ku\u0257insu, to gwamnati ta ga cewa dole ta shiga tsakani domin a kawo kyakkyawan yanayi na kasuwanci\u2019\u2019<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamitin dai ya tabbatar da cewa rijistar ba ta shafi \u01b4an wasu jihohin da suke zaune a jihar Kano ba, sannan kwamitin ya kunshi jami\u2019an tsaro na \u01b4an sanda da DSS da hukumar kula da shige da fice da \u01b4an kasuwa da kuma shugabannin kungiyar \u01b4an China masu kasuwanci a jihar Kano, inda ake fatan nan da makonni biyar kwamitin ya mikawa gwamnati rahotansa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Rahoto<\/p>\n<p>Mujahid Muhammad Tasiu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano ta da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamitin \u0199wararru da zai yi aikin yiwa ba\u0199i \u01b4an \u0199asashen waje mazauna birnin rijista musamman wa\u0257anda suke gudanar da kasuwanci. &nbsp; Gwamnati ta ce ta \u0257auki matakin ne domin samun al\u0199aluman mutanen da suka fito daga \u0199asashen \u0199etare kuma suke gudanar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3604,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3603","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3603","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3603"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3603\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3605,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3603\/revisions\/3605"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3604"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3603"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3603"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3603"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}