{"id":3548,"date":"2024-10-27T10:56:01","date_gmt":"2024-10-27T10:56:01","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3548"},"modified":"2024-10-27T10:56:01","modified_gmt":"2024-10-27T10:56:01","slug":"rikicin-gabas-ta-tsakiya-ya-yi-%c6%99amari-bayan-israila-ta-kai-hari-a-iran","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3548","title":{"rendered":"Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi \u0199amari Bayan Isra&#8217;ila ta Kai Hari a Iran"},"content":{"rendered":"<p>Isra&#8217;ila ta \u0199addamar da jerin hare-hare ta sama a &#8220;wuraren aikin soji&#8221; na Iran, kuma kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta tabbatar da jin \u0199arar fashewar abubuwa sannan ta ce wasu daga cikin \u0199arararrakin an ji su ne daga na&#8217;urorin kakka\u0253o makamai da ke Tehran babban birnin \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Babu bayani game da \u0253arnar da hare-haren wa\u0257anda aka kai da sanyin safiyar Asabar suka yi a Iran sai dai kafofin watsa labaran \u0199asar sun rawaito cewa an &#8220;ji manya \u0199ararraki&#8221; a Tehran da yankuna da ke gefensa sakamakon hare-hare ta sama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rundunar sojojin Isra&#8217;ila ta bayyana hare-haren a matsayin na &#8220;yankan-shakku da aka kai kan wuraren aikin sojojin Iran.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Gwamnatin Iran da \u0199awayenta sun ri\u0199a kai hare-hare a Isra&#8217;ila tun 7 ga watan Oktoba 7 \u2014 a \u0253angagori bakwai \u2014 ciki har da harin kai-tsaye daga \u0199asar Iran,&#8221; a cewar wata sanarwa daga rundunar sojoji Isra&#8217;ila.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Kamar kowace \u0199asa mai cin gashin kanta a duniya, \u0198asar Isra&#8217;ila tana da damar mayar da martani.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rundunar sojin Isra&#8217;ila ta ce ta &#8220;shiga cikakken shiri&#8221; na kare kanta. Mai magana da yawun rundunar sojojin \u0199asar Rear Admiral Daniel Hagari, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga al&#8217;ummar Isra&#8217;ila su &#8220;su sanya idanu kan abubuwan da ke wakana a kewayenku&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ba a kai hare-hare a tashoshin nukiliya ba, in ji kafar watsa labarai ta NBC News and ABC News , wadda ta ambato wani jami&#8217;in Isra&#8217;ila yana bayyana hakan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamfanin dillancin labarai na Iran Farsya ce Isra&#8217;ila ta kai hari kan sansanonin soji da dama a kudanci da kudu maso yammacin Tehran.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kamfanin dillancin labarai na Tasnimya ce an kai hari a sansanin sojojin Islamic Revolutionary Guard Corps amma ba a yi musu \u0253arna ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Iran, wadda ta sha alwashin yin ramuwar gayya, ta \u0199addamar da hare-hare biyu da makamai masu linzami a Isra&#8217;ila a watannin da suka gabata a yayin da Isra&#8217;ila take ci gaba da ya\u0199in kisan \u0199are-dangi a Gaza tun watan Oktoban 2023. Kazalika Isra&#8217;ila ta \u0199addamar da hare-hare na mamayar Lebanon.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Harin da Isra&#8217;ila ta kai wa Iran ranar Asabar na zuwa ne jin ka\u0257an bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya koma \u0199asarsa bayan ya kammala balaguro a Gabas ta Tsakiya inda shi da wasu jami&#8217;an Amurka suka garga\u0257i Isra&#8217;ila kada ta kai harin da zai ta&#8217;azzara rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da kuma tashoshin nukiliya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A gefe guda, na&#8217;urorin Syria na kakka\u0253o makamai sun &#8220;kakka\u0253o&#8221; wani makami a kusa da Damascus da sanyin safiyar Asabar, a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Na&#8217;urorinmu na kakka\u0253o makamai ta sama sun tare wasu makamai a sararin samaniyar kusa da Damascus,&#8221; in ji wani sa\u0199o da SANA ya wallafa a shafin Telegram bayan jin \u0199arar &#8220;fashewa&#8221; a babban birnin Syria.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Isra&#8217;ila ta \u0199addamar da jerin hare-hare ta sama a &#8220;wuraren aikin soji&#8221; na Iran, kuma kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta tabbatar da jin \u0199arar fashewar abubuwa sannan ta ce wasu daga cikin \u0199arararrakin an ji su ne daga na&#8217;urorin kakka\u0253o makamai da ke Tehran babban birnin \u0199asar. &nbsp; Babu bayani game da \u0253arnar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3549,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3548","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3548","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3548"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3548\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3550,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3548\/revisions\/3550"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3549"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3548"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3548"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3548"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}