{"id":3536,"date":"2024-10-27T10:48:21","date_gmt":"2024-10-27T10:48:21","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3536"},"modified":"2024-10-27T10:48:21","modified_gmt":"2024-10-27T10:48:21","slug":"gwamnatin-nijar-za-ta-gina-sabuwar-matatar-man-fetur","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3536","title":{"rendered":"Gwamnatin Nijar za ta gina sabuwar matatar man fetur"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da wani kamfanin \u0199asar Canada, Zimar, sun sa hannu kan wata yarjejeniya domin gina sabuwar matatar mai a yankin Dosso da ke makwabtaka da Benin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin ta Nijar da kamfanin mai na Zimar sun saka hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Alhamis 24 ga Oktoba inda yarjejeniyar ta \u0199unshi batun yadda za a tsara aikin ginin matatar da ku\u0257in da za a kashe wurin ginin da yadda matatar za ta yi aiki da kuma kula da ita bayan kammala gininta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sabuwar matatar da za a gina a Nijar \u0257in ana sa ran za ta rin\u0199a tace ganga 100,000 a kullum.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban Mulkin Sojin Nijar Salifou Mody wanda shi ne ya bayar da sanarwar ya bayyana cewa wannan aikin zai kasance babbar dama ga Nijar haka kuma sakamakon wannan yarjejeniya da \u0199asar ta \u0199ulla da kamfanin na Canada, \u2018yan \u0199asar na Nijar za su samu ayyuka da kuma dama iri daban-daban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mista Mody ya kuma bayyana cewa idan Nijar ta rin\u0199a tace man da take da shi da kanta, hakan zai taimaka wurin rage dogaro da shigar da mai \u0199asar da kuma ha\u0253aka tattalin arzi\u0199in \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Nijar ta zama \u0199asar da ke samar da mai a shekarar 2011 bayan gano mai a Goumeri da Sokor da Agadi da ke yankin Diffa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A Janairun 2012, Nijar \u0257in ta \u0199addamar da matatar manta ta farko wadda ke da \u0199arfin tace ganga 20,000 a duk rana a yankin Zinder.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A watan Janairun bana, \u0199asar ta soma fitar da \u0257anyen manta zuwa kasuwannin duniya ta hanyar wani bututun mai wanda ke da nisan kilomita 2,000, wanda ya tashi tun daga Nijar \u0257in zuwa cikin Benin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ana kallon wannan matakin da Nijar \u0257in ta \u0257auka a matsayin ci gaba ta \u0253angaren tattalin arzi\u0199inta da kuma rage dogaro wurin shigar da mai cikin \u0199asarta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da wani kamfanin \u0199asar Canada, Zimar, sun sa hannu kan wata yarjejeniya domin gina sabuwar matatar mai a yankin Dosso da ke makwabtaka da Benin. &nbsp; Gwamnatin ta Nijar da kamfanin mai na Zimar sun saka hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Alhamis 24 ga Oktoba inda yarjejeniyar ta \u0199unshi batun yadda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3537,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3536","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3536","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3536"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3536\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3538,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3536\/revisions\/3538"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3537"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3536"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3536"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3536"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}