{"id":3517,"date":"2024-10-25T03:26:18","date_gmt":"2024-10-25T03:26:18","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3517"},"modified":"2024-10-25T03:26:18","modified_gmt":"2024-10-25T03:26:18","slug":"shugabannin-duniya-sun-yi-allah-wadai-da-harin-taaddanci-da-aka-kai-turkiyya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3517","title":{"rendered":"Shugabannin Duniya Sun yi Allah Wadai da Harin Ta&#8217;addanci da Aka Kai Turkiyya"},"content":{"rendered":"<p>Shugabanni daga \u0199asashen duniya sun yi tur da Allah wadai da harin ta&#8217;addanci da aka kai masana&#8217;antar \u0199era kayayyakin jiragen sama a babban birnin Turkiyya, inda mutum biyar suka yi shahada sannan wasu 22 suka jikkata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da harin na hedkwatar Masana&#8217;antar \u0198era Jiragen Sama ta TAI a birnin Ankara a ranar Laraba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Erdogan ya ce &#8220;Ina Allah wadai da wannan \u0257anyen aikin da aka kai kan cibiyoyin masana&#8217;antun \u0199era jiragen sama na Turkiyya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Rasha) :Shugaban Rasha Vladimir Putin shi ma ya yi Allah wadai da harin a yayin taron kungiyar BRICS da Erdogan ya halarta a matsayin ba\u0199o a can \u0199asar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Ya mai girma Shugaban \u0198asa da abokan aiki, muna matukar farin cikin maraba da kai zuwa Kazan, amma kafin mu fara aiki, ina so in jajanta maka dangane da harin ta&#8217;addancin da ya faru. Rahotannin da ke fitowa daga kafafen ya\u0257a labarai sun nuna cewa an kai harin ta&#8217;addanci a Turkiyya. &#8221; in ji Putin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Amurka) :Ita ma Amurka ta yi Allah wadai da harin ta&#8217;addancin, inda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce, &#8220;Amurka tana tare da \u0199awarmu Turkiyya, kuma tana matu\u0199ar yin Allah wadai da harin ta&#8217;addancin da ya faru a yau. Muna jajantawa wadanda abin ya shafa da iyalansu,&#8221; in ji Blinken a sa\u0199on da ya wallafa a shafin X.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shi ma mai magana da yawun Majalisar Tsaro ta Fadar White House John Kirby ya yi Allah wadai da harin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cA safiyar yau, addu\u2019o\u2019inmu na tare da dukkan wadanda abin ya shafa da iyalansu, da ma al\u2019ummar Turkiyya a wannan mawuyacin lokaci,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(NATO) :Shi ma Sakataren \u0198ungiyar Tsaro ta NATO Mark Rutte ya yi Allah wadai da harin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Muna yin Allah wadai da ta&#8217;addanci a kowane salo kuma muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa,&#8221; in ji Rutte.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;NATO tana tare da \u0199awarta Turkiyya,&#8221; ya \u0199ara da cewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Tarayya Turai) :Babban jami&#8217;in kula da Harkokin Waje na Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi Allah wadai da harin ta&#8217;addanci ta kowane \u0253angare, a cikin wani sa\u0199on da ya wallafa a shafin X bayan kai harin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce &#8221; EU na nuna goyon baya ga Turkiyya a wannan mawuyacin lokaci.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Azerbaijan) : Ita ma Azabaijan ta yi Allah-wadai da harin, inda ta \u0199ara da cewa Baku tana tare da &#8220;&#8216;yar&#8217;uwarta Turkiyya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Faransa) :Shugaban Faransa Emmanuel Macron shi ma ya yi Allah wadai da &#8220;harin ta&#8217;addancin da aka kai Ankara cikin kakkausar murya,&#8221; a wani sakon da ya wallafa a shafin X.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, al&#8217;ummar Faransa sun ji takaici tare da tausaya wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin sun kuma jajanta musu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Jamus) : Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana a shafin X cewa: &#8220;Na yi matu\u0199ar ka\u0257uwa da rahotannin mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata a Ankara, muna yin Allah wadai da ta&#8217;addanci ta kowace siga kuma muna goyon bayan abokiyar hul\u0257armu Turkiyya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(The Netherlands) : Shi ma firaministan kasar Holland Dick Schoof ya mi\u0199a sakon ta&#8217;aziyyarsa ga Shugaba Erdogan, yana mai cewa kasar Netherlands ta yi Allah wadai da duk wani nau&#8217;in ta&#8217;addanci. Muna tausaya wa Turkiyya kuma muna sa ido sosai kan lamarin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Austria) Shugaban kasar Austriya Karl Nehammer shi ma ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa: &#8220;Ta&#8217;addanci da tashin hankali ba su da gurbi a cikin al&#8217;ummarmu.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Kosovo) :Ita ma Kosovo ta yi Allah wadai da harin, inda ta bayyana goyon bayanta ga Turkiyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Muna tare da \u0199awayarmu, Turkiyya, biyo bayan harin ta&#8217;addancin da aka kai yau a Ankara, muna mi\u0199a ta&#8217;aziyyarmu ga iyalai da &#8216;yan&#8217;uwan wadanda abin ya shafa. Ta&#8217;addanci da tashin hankali ba su da gurbi a duniyarmu!&#8221; in ji Shugaba Vjosa Osmani a sa\u0199onsa a shafin X.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Slovenia) :Slovenia ma ta bi sahun yin Allah wadai da &#8221;mummunan&#8221; harin, inda mataimakin firaministan kasar Tanja Fajon ya ja hankali kan adadin fararen hula da suka mutu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Na yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai &#8211; wanda ya yi sanadin rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba &#8211; a Turkiyya a yau. Ta&#8217;addanci da kowane irin tashin hankali ba su da waje &#8211; a cikin al&#8217;ummomin dimokuradiyya. Muna ta&#8217;azaiyar wadanda aka kashe da kuma jajanta wa &#8216;yan&#8217;uwansu,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Ireland) :Ma&#8217;aikatar Harkokin Wajen Ireland ta fada a shafin X cewa &#8220;Ireland ta yi tir da mummunan harin da aka kai a Turkiyya a yau.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Serbia) :Shugaban Sabiya Aleksandar Vucic ya bayyana &#8220;damuwa&#8221; game da harin ta&#8217;addanci da aka kai a Ankara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Serbiya ta yi Allah wadai da duk wani nau&#8217;in ta&#8217;addanci, kuma tana goyon bayan Turkiyya da al&#8217;ummarta,&#8221; in ji shi, yana mai mi\u0199a sa\u0199on ta&#8217;aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, &#8220;kuma ina yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>(Canada) :Ofishin Jakadancin Canada a Turkiyya ya fitar da irin wannan bayanai da kakkausar murya, inda ya kara da cewa Ottawa na goyon bayan Turkiyya, &#8220;abokiyarmu kuma aminiyarmu, a wannan mawuyacin lokaci.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugabanni daga \u0199asashen duniya sun yi tur da Allah wadai da harin ta&#8217;addanci da aka kai masana&#8217;antar \u0199era kayayyakin jiragen sama a babban birnin Turkiyya, inda mutum biyar suka yi shahada sannan wasu 22 suka jikkata. &nbsp; Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da harin na hedkwatar Masana&#8217;antar \u0198era Jiragen Sama ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3518,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3517","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3517","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3517"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3517\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3519,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3517\/revisions\/3519"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3518"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3517"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3517"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3517"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}