{"id":3502,"date":"2024-10-25T03:18:14","date_gmt":"2024-10-25T03:18:14","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3502"},"modified":"2024-10-25T03:18:14","modified_gmt":"2024-10-25T03:18:14","slug":"abin-da-ya-kamata-ku-sani-kan-%c6%99ungiyar-da-putin-ke-kar%c9%93ar-ba%c6%99uncinta-brics","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3502","title":{"rendered":"Abin da ya Kamata ku Sani Kan \u0199ungiyar da Putin ke Kar\u0253ar Ba\u0199uncinta: BRICS"},"content":{"rendered":"<p>Shugabannin \u0199asashen duniya 24 sun hallara a \u0199asar Rasha a ranar Talata don bu\u0257e taron kwanaki uku na \u0199ungiyar BRICS, na kawancen \u0199asashe masu tasowa da ke fatan ganin Kremlin za ta kalubalanci &#8220;mulkin \u0198asashen Yamma&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mecece BRICS?<\/p>\n<p>\u0198asashen Brazil da Rasha da Indiya da kuma China ne suka kafa \u0199ungiyar ta raya tattalin arziki a shekarar 2009 inda a hukumance suka yi maraba da Afirka ta Kudu cikin \u0199ungiyar a sherakar 2009, kana suka fa\u0257a\u0257a sunanta zuwa BRICS wanda ke nuna harafin farko na sunayen \u0199asashen biyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>BRICS dai ta ku\u0257uri aniyyar kalubalantar karfin ikon Amurka da wasu \u0198asashen Yamma a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Cikin sauri ta fa\u0257a\u0257a bayan Iran, da Masar da Habasha da Hadadiyyar Daular Larabawa suka shiga cikin watan Janairu. Kazalika Turkiya da Azerbaijan da Malaysia da sun gabatar da takardar neman shiga.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>BRICS tana da burin fa\u0257a\u0257a muryar manyan \u0199asashen masu tasowa don \u0199alubalantar tsarin duniya da \u0199asashen yamma ke jagoranta. Mambobin da suka kafa ta sun yi kira kan a samar da tsarin adalci a duniya da kuma gyara cibiyoyin \u0199asa da \u0199asa kamar Majalisar Dinkin Duniya, da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tare da \u0199arin sabbin mambobi hu\u0257u a wannan shekara, a yanzu \u0199ungiyar za ta kunshi kasashe tara kenan, wadanda ke kara taka rawa a tattalin arzikin duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198asahshen \u0199ungiyar BRICS sun \u0199unshi kashi 30 cikin 100 na fa\u0257in \u0199asa a duniya, da kuma kashi 45 cikin 100 na yawan al&#8217;ummar duniya sannan da kashi 45 na yawan arzikin man fetur da ake hakowa a duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A tare, suna sau\u0199a\u0199e kusan kashi \u0257aya bisa hu\u0257u na kasuwancin duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wasu muhimman batutuwa ne taron na Rasha zai fi mayar da hankali a kai?<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Manyan batutuwan da ke cikin ajandar sun ha\u0257a da matsayar Shugaban Rasha Vladmir Putin na tsarin biyan ku\u0257i da kungiyar BRICS ke jagoranta ga abokiyar hamayyarta SWIFT, cibiyar hada-hadar ku\u0257i ta \u0199asa da \u0199asa da aka cire bankunan Rasha daga ciki a shekarar 2022, da kuma tashe-tashen hankula da suka mamaye yankin gabas ta tsakiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rasha dai ta bayyana taron a matsayin gagarumin mataki na diflomasiyya da zaitaimaka mata kulla kawance don kalubalantar &#8220;mulkin kasashen yamma&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gabanin taron, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yaba taron yana mai kiransa da &#8220;abokan ha\u0257in gwiwa na musamman&#8221; tsakanin Moscow da New Delhi, ya kuma ce za a tattauna kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi a cikin ajanda.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugabannin \u0199asashen duniya 24 sun hallara a \u0199asar Rasha a ranar Talata don bu\u0257e taron kwanaki uku na \u0199ungiyar BRICS, na kawancen \u0199asashe masu tasowa da ke fatan ganin Kremlin za ta kalubalanci &#8220;mulkin \u0198asashen Yamma&#8221;. &nbsp; Mecece BRICS? \u0198asashen Brazil da Rasha da Indiya da kuma China ne suka kafa \u0199ungiyar ta raya tattalin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3503,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3502","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3502","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3502"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3502\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3504,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3502\/revisions\/3504"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3503"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3502"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3502"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3502"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}