{"id":3490,"date":"2024-10-22T21:31:27","date_gmt":"2024-10-22T21:31:27","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3490"},"modified":"2024-10-22T21:31:27","modified_gmt":"2024-10-22T21:31:27","slug":"gwamnatin-katsina-ta-bayar-da-umarnin-rufe-makarantun-koyon-aikin-lafiya-masu-zaman-kansu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3490","title":{"rendered":"Gwamnatin Katsina ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantun Koyon Aikin Lafiya Masu Zaman Kansu"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Radda ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun koyon kiwon lafiya masu zaman kansu da ke fa\u0257in jihar tare da soke lasisinsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya sanar da wannan mataki ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Katsina.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya \u0257auki matakin ne bayan wani bincike da Ma&#8217;aikatar Kiwon Lafiya ta gudanar da ya nuna makarantun ba su da inganci sannan da dama daga cikinsu ba su da rijista, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mammada ya ce a shekarun baya-bayan, jihar ta Katsina ta samu \u0199aruwar makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya masu zaman kansu, wa\u0257anda da dama daga cikinsu ba su da rajista kuma ba su da inganci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cKo da yake mun san muhimmiyar rawar da makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu suke takawa wajen tabbatar da lafiyar al&#8217;umma, amma yana da muhimmanci mu tabbatar da ingancinsu domin kare lafiyar al&#8217;ummarmu,&#8221; in ji Mammada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa gwamnatin jihar za ta samar da tsari mai inganci da zai tabbatar da \u0199warewar irin wa\u0257annan makarantu kafin a ba su damar ci gaba da horar da masu neman ilimin kiwon lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jihar Katsina na cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar \u0199alubale a fannin kiwon lafiya da tsaro kuma gwamnatin jihar ta sha alwashin shawo kan matsalolin, abin da ya sa masana suka yaba mata kan \u0257aukar wannan mataki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Radda ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun koyon kiwon lafiya masu zaman kansu da ke fa\u0257in jihar tare da soke lasisinsu. &nbsp; Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya sanar da wannan mataki ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a birnin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3491,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3490","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3490","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3490"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3490\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3492,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3490\/revisions\/3492"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3491"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3490"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3490"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3490"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}