{"id":3487,"date":"2024-10-22T21:30:01","date_gmt":"2024-10-22T21:30:01","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3487"},"modified":"2024-10-22T21:30:01","modified_gmt":"2024-10-22T21:30:01","slug":"shugaba-paul-biya-ya-koma-kamaru-bayan-shafe-makonni-ba-ya-nan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3487","title":{"rendered":"Shugaba Paul Biya ya Koma Kamaru Bayan Shafe Makonni ba ya nan"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sauka a babban filin jiragen sama na Yaounde a ranar Litinin, bayan da ya shafe makwanni da barin kasar, inda aka yi ta jita-jita game da lafiyarsa, kamar yadda gidan talabijin na kasar CRTV ya nuna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An nuna shugaban kasar mai shekara 91 a gidan talabijin a lokacin da yake sauka daga jirgi, inda ya dinga musabaha da jami&#8217;an da ke kusa da matarsa Chantal, a daidai lokacin da jama&#8217;a ke ta murna suna jiran tarbarsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Magoya bayansa da suke jeru a titi sun yi ta buga ganguna da rera wa\u0199o\u0199i \u0257auke da hotunansa, a lokacin da shugaban ke wucewa don tafiya fadarsa, kamar yadda kafar yada labarai ta CRTV ta bayyana, a yayin da take watsa yadda saukar tasa ta kasance.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An yi ta kokwanto kan halin lafiyar Biya da kuma inda ya tafi bayan da aka daina jin \u0257uriyarsa tun bayan taron da ya halarta na \u0199asashen Afirka da China a birnin Beijing a watan Satumba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na CRTV ya ce &#8220;A yau shugaban kasa na kan hanyarsa ta dawowa, kuma hakan zai kawo \u0199arshen jita-jitar da ake ya\u0257awa.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shafin da ke bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama ya nuna jirgi \u0199irar Boeing mai lamba CMR001, wanda shi ne Biya ke hawa, ya bar birnin Geneva na Switzerland a ranar Litinin, inda a can shugaban yake tsawon makonni, in ji majiyoyin hukuma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An mammanna manyan fastocin shugaban \u0199asar wanda ya shafe shekara 40 yana mulki ba hamayya a babban birnin kasar ana yi masa maraba gabanin komawar tasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wajen ya ce an rubuta a \u0257aya daga cikin allunan cewa &#8220;Barka da dawowa gida, Shugaban Kasa.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar 8 ga watan Oktoba ne gwamnatin \u0199asar ta fitar da sanarwa bayan da aka yi ta ya\u0257a jita-jita, inda ta ce Shugaban \u0198asar ya kusa komawa gida.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sannan a hukumance gwamnati ta haramta wa kafafen yada labarai na cikin gida tattaunawa kan yanayin lafiyarsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Har ila yau shugaban na Kamaru bai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York ba, da kuma taron kasashe masu magana da harshen Faransanci a birnin Paris.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sauka a babban filin jiragen sama na Yaounde a ranar Litinin, bayan da ya shafe makwanni da barin kasar, inda aka yi ta jita-jita game da lafiyarsa, kamar yadda gidan talabijin na kasar CRTV ya nuna. &nbsp; An nuna shugaban kasar mai shekara 91 a gidan talabijin a lokacin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3488,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3487","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3487","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3487"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3487\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3489,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3487\/revisions\/3489"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3488"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3487"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3487"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3487"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}