{"id":3451,"date":"2024-10-19T21:08:37","date_gmt":"2024-10-19T21:08:37","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3451"},"modified":"2024-10-19T21:08:37","modified_gmt":"2024-10-19T21:08:37","slug":"ga-dukkan-alamu-za-a-gwabza-ya%c6%99i-tsakanin-israila-da-iran-fidan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3451","title":{"rendered":"Ga dukkan alamu za a gwabza ya\u0199i tsakanin Isra&#8217;ila da Iran \u2014 Fidan"},"content":{"rendered":"<p>Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi garga\u0257i da cewa dole Turkiyya da ma yankinsu su shirya fuskantar ya\u0199in da za a iya gwabzawa tsakanin Isra&#8217;ila da Iran saboda &#8220;akwai yiwuwar hakan ta faru matu\u0199a&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Dole ne a kalli ya\u0199i tsakanin Isra&#8217;ila da Iran a matsayin abu da zai iya yiwuwa sosai,&#8221; in ji Fidan a wata tattaunawa a tashar talabijin a ranar Alhamis.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa &#8220;Na yi amanna cewar wannan lamari zai iya faruwa kuma matakin farko da \u0199asashen yankin za su \u0257auka shi ne su shirya tunkarar wannan yanayi, a matsayin \u0199asa da kuma yanki. Wannan ba abu ne da muke bu\u0199atar ya ya\u0257u ba. Ya\u0257uwar ya\u0199i da tayar da tarzoma a yankin ba su ne abin da muke son gani ko fata ba.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Turkiyya ba ta goyon bayan &#8220;duk wani rikici da za a yi da Iran wanda zai riki\u0257e ya koma ya\u0199i,&#8221; Ankara na adawa da hakan, inda ya yi tsokaci da cewar Tehran na da ha\u0199\u0199in kare kanta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake bayani kan manufofin Turkiyya na \u0199asashen waje da harkokin tsaro, Fidan ya ce Turkiyya &#8220;ba ta sanya idanuwanta a kan ko da ta\u0199i \u0257aya na \u0199asar wani ba, kuma tana son \u0199ulla ala\u0199a ta ci-gaban yankin da zaman lafiya da walwala.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ya yi nuni da cewar adawar da ke tsakanin China da Amurka za ta \u0199ara \u0199amari, yana mai nuni da gogayyar tattalin arziki tsakanin \u0199asashen biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8216;Bu\u0257a\u0257\u0257iyar ma\u0199abarta&#8217;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Game da i\u0199irarin mutuwar shugaban \u0253angaren siyasa na Hamas Yahya Sinwar, Fidan ya ce Ankara na jiran tabbatar da hakan daga Hamas, yana mai \u0199arawa da cewar babu wani labarin musanta hakan da suka samu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Abin takaici Gaza ta zama bu\u0257a\u0257\u0257iyar ma\u0199abarta inda ake kashe dubban wa\u0257anda ba su ji ba ba su gani ba, ana aikata kisan kiyashi,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yi tsokaci da cewar Ankara ta auna ta ga yadda Isra&#8217;ila &#8220;ta shirya \u0257aukar matakin soji na \u0257aya bayan \u0257aya ta kawar da duk wani da ya fuskance ta, ciki har da Hamas, Hezbollah, Houthi da ke Yemen, da sauransu,&#8221; ya kuma bayyana fatan Turkiyya na hana yiwuwar bu\u0257e sabon babi na ya\u0199in.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake bayyana yadda sauran \u0199asashen yankin ba sa nuna wa Lebanon irin damuwar da suke nuna wa Falas\u0257inawa, Fidan ya ce &#8220;Akwai dalili a nan. Wannan dalili shi ne, tabbas mai girma da ma&#8217;ana. Muna bu\u0199atar kallon dalilan da suka janyo hakan.&#8221; TRT Afarka Hausa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi garga\u0257i da cewa dole Turkiyya da ma yankinsu su shirya fuskantar ya\u0199in da za a iya gwabzawa tsakanin Isra&#8217;ila da Iran saboda &#8220;akwai yiwuwar hakan ta faru matu\u0199a&#8221;. &nbsp; &#8220;Dole ne a kalli ya\u0199i tsakanin Isra&#8217;ila da Iran a matsayin abu da zai iya yiwuwa sosai,&#8221; in [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3452,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3451","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3451","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3451"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3451\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3453,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3451\/revisions\/3453"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3452"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3451"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3451"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3451"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}