{"id":3436,"date":"2024-10-19T21:01:03","date_gmt":"2024-10-19T21:01:03","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3436"},"modified":"2024-10-19T21:01:03","modified_gmt":"2024-10-19T21:01:03","slug":"arzikin-%c9%97angote-ya-ninka-zuwa-dala-biliyan-28-bayan-fara-aikin-matatar-mansa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3436","title":{"rendered":"Arzikin \u018aangote ya ninka zuwa dala biliyan 28 bayan fara aikin matatar mansa"},"content":{"rendered":"<p>Hamsha\u0199in attajirin Afirka, Alhaji Aliko \u018aangote ya samu \u0199aruwar arziki, inda dukiyarsa ta ninku a sanadiyar fara aikin matatar mansa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yanzu arzikin attajirin ya ninku zuwa dala biliyan 27.8, kamar yadda rahoton mujallar \u2018Bloomberg Billionaire Index\u2019 \u2013 mai nazarin masu arziki na duniya \u2013 ya nuna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matatar man ta \u018aangote, wadda aka bu\u0257e a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, ita ce irinta na farko, wadda ke iya tace kusan kowane nau\u2019in \u0257anyan mai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matatar za ta iya kawo gagarumin sauyi a \u0253angaren tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar mayar da \u0199asar mai dogaro da kanta a \u0253angaren man fetur.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Game da \u0199alubalen da ya fuskanta wajen gina matatar, Dangote ya ce ba zai yi wa ko da babban ma\u0199iyinsa fatan shiga irin damuwar ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201dBan san muna gina wani abu ba ne da zai zo ya dame mu,\u201d in ji \u018aangote mai shekara 67 a wata ziyara da ya kai New York.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cMatsalolin sun zo daga \u0253angarori da dama, mutane da yawa suna ta ru\u0257ar da mu cewa ba za mu iya ba, kuma ko da mun yi \u0257in, ba za mu samu nasara ba,\u201d kamar yadda kafar Bloomberg ta ruwaito.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun bayan da matatar ta fara aiki a watan Janairu, an samu sa\u0253ani daban-daban tsakaninta da gwamnati da kuma kamfanin man fetur na \u0199asar, da kuma amfaninta ga \u01b4an \u0199asa da ma tasirinsa ga muhalli.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wajen Dangote \u2013 wanda ya fara zama biloniya da kasuwancin siminti \u2013 bu\u0257e matatar man wani gagarumin aiki ne a rayuwarsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gina matatar ya \u0257auki shekara 11, ta kuma ci dala biliyan 20, kuma mafi yawancin aikin, shi ya \u0257auki nauyinsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yanayin kasuwancin Dangote<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u018aangote, wanda ya fara furfura yanzu saboda shekaru, hamsha\u0199in \u0257ankasuwa ne.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Asalin kasuwancinsa na kayayyakin masarufi ne, yawanci siminti ne da sukari da gishiri da fulawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Arzikinsa abin ban mamaki ne kasancewar a \u0199asar da yake, kashi 40 na mutanenta suna rayuwa ne cikin talauci, kuma yawancin arzikin \u0199asar a man fetur ne.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai a \u0253angaren bu\u0257e matatar man, ya shiga matsaloli.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An \u0199wace asalin wurin da ya so ya bu\u0257e matatar, bayan ya sha fama da rikice-rikice da \u01b4an \u0199auyen.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga baya sai ya koma kudancin jihar Legas, inda can ma ya fuskanci wasu \u0199alubalen da mutane.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan an ba shi sabon filin, sai ya kasance kwari ne, inda dole ya yi aikin yashewa sannan ya yi ciko na kusan \u0199afa biyar (mita 1.5) domin kiyaye aukuwar ambaliya. Kamfanin ya gina dam da tashar jirgin ruwa domin aikin matatar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shekara biyu bayan fara ginin, sai annobar korona ta \u0253arke.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wasu daga cikin kamfanonin da suke kawo masa kayayyaki sai suka samu matsalar ku\u0257i, suka dakata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sannan a wani \u0253angaren kuma, \u018aangote yana biyan dala miliyan 50 zuwa dala miliyan 60 duk shekara a matsayin ku\u0257in ruwa na bashin dala biliyan 5.5 da ya kar\u0253a daga bankunan cikin gida.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma bayan bu\u0257e matatar a bana, dole ta fara neman \u0257anyen mai daga \u0199asashen Turai, wanda wannan ya \u0199ara masa tsada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A yawancin harkokin kasuwancinsa, \u018aangote yana samun ala\u0199a mai kyau da shugabannin Najeriya, wanda hakan ke taimakon harkokinsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai bai samu wannan ba da shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idongari.ng<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>Salihu Garba.<\/p>\n<p>At&#8217;tajdid news<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hamsha\u0199in attajirin Afirka, Alhaji Aliko \u018aangote ya samu \u0199aruwar arziki, inda dukiyarsa ta ninku a sanadiyar fara aikin matatar mansa. &nbsp; Yanzu arzikin attajirin ya ninku zuwa dala biliyan 27.8, kamar yadda rahoton mujallar \u2018Bloomberg Billionaire Index\u2019 \u2013 mai nazarin masu arziki na duniya \u2013 ya nuna. &nbsp; Matatar man ta \u018aangote, wadda aka bu\u0257e [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3437,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3436","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3436","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3436"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3436\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3438,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3436\/revisions\/3438"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3437"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3436"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3436"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3436"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}