{"id":3412,"date":"2024-10-16T20:47:47","date_gmt":"2024-10-16T20:47:47","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3412"},"modified":"2024-10-16T20:47:47","modified_gmt":"2024-10-16T20:47:47","slug":"an-sami-mutuwar-mutane-94-a-karamar-hukumar-taura-ta-jahar-jigawa-sanadiyar-kwacewar-tankar-mai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3412","title":{"rendered":"An Sami Mutuwar Mutane 94 a Karamar Hukumar Taura ta Jahar Jigawa Sanadiyar Kwacewar Tankar Mai"},"content":{"rendered":"<p><span style=\"color: #00ff00\">Hukumomi a Nijeriya sun tabbatar da mutuwar kusan mutum 100 sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin \u0199asar.<\/span><\/p>\n<p><span style=\"color: #ff0000\"><strong>Tankar ta tashi ne daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa garin Nguru na jihar Yobe amma ta yi hatsari a yankin \u0199aramar hukumar Taura ranar Talata da daddare.<\/strong><\/span><\/p>\n<p><span style=\"color: #0000ff\"><em>Mai magana da yawun rundunar &#8216;yan sandan jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya ce mutum a\u0199alla 94 ne suka mutu sannan fiye da 50 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi bayan tankar man ta fa\u0257i.<\/em><\/span><\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa lamarin ya faru ne yayin da mutane suke rige-rigen kwasar fetur daga cikin tankar, abin da ya haddasa gobara.<\/p>\n<p>DSP Lawan Shiisu Adam ya ce: &#8220;A jiya Talata da misalin 11:30 na dare muka samu labarin hatsarin wata tanka da ta taso daga Kano za ta je Nguru. A lokacin da ta zo Taura kusa da Khadija University, sai motar ta \u0199wace daga hannun direban hakan ya sa tankar ta fa\u0257i.<\/p>\n<p>&#8220;Sai mai ya ri\u0199a malala yana shiga magudanar ruwa da kwatoci. Wannan dalili ne ya sa mutane sun ga banza ta fa\u0257i suka fito suna \u0257iban mai. A lokacin ne wuta ta tashi. A nan-take an samu mutum 94 da wuta ta \u0199one su \u0199urmus, sai kuma mutum 50 da aka \u0257iba aka kai su asibitin garin Ringim inda suke karbar magani,&#8221; in ji kakakin &#8216;yan sandan.<\/p>\n<p>Wasu rahotanni dai su ce mutanen da suka mutu sun zarta 150, kuma ana sa rai adadin zai \u0199aru.<\/p>\n<p>Ana yawan fuskantar hatsarin mota a Nijeriya sakamakon tu\u0199in ganganci da rashin bin dokoki lamarin da kan haddasa asarar rayuka.<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumomi a Nijeriya sun tabbatar da mutuwar kusan mutum 100 sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin \u0199asar. Tankar ta tashi ne daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa garin Nguru na jihar Yobe amma ta yi hatsari a yankin \u0199aramar hukumar Taura ranar Talata [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3413,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3412","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3412","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3412"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3412\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3414,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3412\/revisions\/3414"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3413"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3412"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3412"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3412"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}