{"id":3403,"date":"2024-10-15T13:34:05","date_gmt":"2024-10-15T13:34:05","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3403"},"modified":"2024-10-15T13:34:05","modified_gmt":"2024-10-15T13:34:05","slug":"shugaban-kasar-turkiyya-erdogan-ya-bayyana-fishinsa-kan-jamioin-yan-koran-yahudawan-sahyoniyya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3403","title":{"rendered":"Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami&#8217;o&#8217;in &#8216;Yan Koran Yahudawan sahyoniyya\u00a0"},"content":{"rendered":"<p><em><strong>Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami&#8217;o&#8217;in &#8216;Yan Koran Yahudawan sahyoniyya\u00a0<\/strong><\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Babu tantama cewa &#8216;yan koren Isra&#8217;ila ne ke ri\u0199e da iko da manyan jami&#8217;o&#8217;in duniya da sunan bayar da tallafin ku\u0257i,&#8221; in ji shugaban Turkiyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta&#8217;annatin da Isra&#8217;ila ke aikatawa a yankin Gaza na Falas\u0257inu ya bayar da gudunmawa wajen fitowa fili a fahimci yadda &#8216;yan koren Isra&#8217;ila ke da iko kan manyan jami&#8217;o&#8217;in duniya, in ji shugaban \u0199asar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Mun shaida irin wannan abin kunyar inda &#8216;yan sanda suka dinga musguna wa \u0257aliban da suka ce &#8216;ana aikata kisan kiyashi a Gaza&#8217;, shugaba Erdogan ya bayyana haka a ranar Talata a yayin taron sabuwar shekarar karatu ta 2024\/2025 a Ankara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma ja hankali kan yadda aka tursasawa shugabannin jami&#8217;o&#8217;i da suka bayar da damar yin zanga-zangar adawa da kisan Falas\u0257inawa yin murabus, aka azabtar da su tare da titsiye su a gaban majalisar dokokin Amurka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa &#8220;Babu wani suka ko bayyana ra&#8217;ayi game da Falas\u0257inawa aka yarda da shi. Ya zama babu tantamar cewa &#8216;yan koren Isra&#8217;ila ne ke ri\u0199e da iko da manyan jami&#8217;o&#8217;in duniya inda suke fakewa da bayar da tallafin ku\u0257a\u0257e.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban na Turkiyya ya kuma soki gwamnatocin \u0199asashen Yammacin duniya bisa gazawa wajen kawo \u0199arshen kisan kiyashi a Gaza tsawon shekara guda, yana mai cewa sun zubar da \u0199imarsu &#8220;a \u0199o\u0199arin da suke yi na kare Isra&#8217;ila&#8221;.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya\u0199i da dukkan &#8216;yan adam<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da take ci gaba da sa\u0253awa matakin da Kwamitin Tsaro na Majalisar \u018ainkin Duniya ya \u0257auka na kiran da a tsagaita wuta a Gaza, Isra&#8217;ila na ci gaba kai munanan hare-hare Gaza, tana mai fakewa da harin da \u0199ungiyar tirjiya ta Falas\u0257inawa Hamas ta kai mata a ranar 7 ga Oktoban 2023.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hare-haren na Isra&#8217;ila sun tsugunar da kusan dukkan jama&#8217;ar yankin da ci gaba da fuskantar mamayar da ta janyo karancin abinci, tsaftataccen ruwan sha, da magunguna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u0198o\u0199arin shiga tsakani da Amurka, Masar da Qatar ke jagoranta don a tsagaita wuta a Gaza da yin musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra&#8217;ila ya ci tura saboda yadda Firaministan Isra&#8217;ila Benjamin Netanyahu ya dakatar da ya\u0199in.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yaki na tsawon shekara guda da yahudawan\u00a0 sahyoniyya suke yi a Gaza ya yi ajalin mutane 42,000. Isra&#8217;ila na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa saboda ta&#8217;annatin da ta aikata a yankin, da ke da Falasdinawa sama da miliyan biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A gefe guda, hare-haren Isra&#8217;ila a Lebanon tun daga 2023 zuwa yau sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 2,000 inda aka raba wasu milayan 1.2 da matsugunansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai rahoto;<\/p>\n<p>Mustapha Garba usman.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami&#8217;o&#8217;in &#8216;Yan Koran Yahudawan sahyoniyya\u00a0 &nbsp; &#8220;Babu tantama cewa &#8216;yan koren Isra&#8217;ila ne ke ri\u0199e da iko da manyan jami&#8217;o&#8217;in duniya da sunan bayar da tallafin ku\u0257i,&#8221; in ji shugaban Turkiyya. &nbsp; Ta&#8217;annatin da Isra&#8217;ila ke aikatawa a yankin Gaza na Falas\u0257inu ya bayar da gudunmawa wajen [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3404,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3403","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3403","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3403"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3403\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3405,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3403\/revisions\/3405"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3404"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3403"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3403"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3403"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}