{"id":3266,"date":"2024-09-28T12:15:30","date_gmt":"2024-09-28T12:15:30","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3266"},"modified":"2024-09-28T12:24:47","modified_gmt":"2024-09-28T12:24:47","slug":"duniya-ba-za-ta-iya-jiran-amincewar-israila-don-aiwatar-da-yarjejeniyar-samar-da-%c6%99asa-biyu-ba-a-yankin-kasar-palastinu-fidan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3266","title":{"rendered":"Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra&#8217;ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da \u0199asa biyu ba a yankin kasar Palastinu \u2014 Fidan"},"content":{"rendered":"<p><a href=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004.jpg\"><img loading=\"lazy\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"aligncenter size-medium wp-image-3267\" src=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004-300x169.jpg 300w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004-1024x576.jpg 1024w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004-768x432.jpg 768w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004-860x483.jpg 860w, https:\/\/attajdidnews.com.ng\/wp-content\/uploads\/2024\/09\/IMG-20240928-WA0004.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/a>Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki matakin Isra&#8217;ila na \u0199in aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, ya kuma yi gargadin cewa matsalar Falasdinu da ba a warware ta ba na barazana ga zaman lafiyar yankin baki daya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ya bayyana a ranar alhamis yayin wani taron ministoci kan Gaza a gefen babban Taron MDD a birnin New York, wanda \u0199ungiyoyi hadin Kan \u0198asashen Musulmi ta OIC da na hadin Kan \u0198asashen Larabawa da ta tuntuba ta Gaza da tarayyar turai da kuma Norway suka shirya, inda ya ce: &#8220;Ba za mu jira fatan alherin Isra&#8217;ila don aiwatar da shawarwarin samar da kasashe biyu masu cin gasin kansu ba.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce matakin da majalisar dokokin Isra&#8217;ila ta \u0257auka na \u0199in amincewa da kafa kasar Falasdinu da samar da kasashe biyu a fili yake.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Wannan ha\u0257ama ce tsantsa wadda bai kamata a amince da ita ba.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ta bayyana cewa kisan gilla da Isra&#8217;ila ke yi a Zirin Gaza na ci gaba da wanzuwa ba tare da an kawo karshensa ba, Fidan ya ce tattaunawar tsagaita wuta ta yi tsami ne saboda (Firaministan Isra&#8217;ila Benyamin Netanyahu) yana yi musu \u0199afar ungulu a duk lokacin da ake ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce Isra&#8217;ila ta fara fa\u0257a\u0257a hare-harenta zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin \u0198udus, yanzu kuma ta kai kasar Lebanon.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kasashen duniya sun yi gargadi kan hare-haren da ake kai wa kasar Labanon, yayin da ake ya\u0257a ya\u0199in Gaza a yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ce, \u0199asarsa ta da\u0257e tana bayyana cewa idan har ba a warware batun Falasdinawa ba, to hakan zai jefa \u0257aukacin yankin cikin &#8220;ba\u0199in rami.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Haka ne abin da ke faruwa a Lebanon a yanzu haka, yankinmu na ci da wuta saboda Netanyahu,&#8221; in ji Fidan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Muna cikin wani lokaci na ko-ta-kwana. Ta&#8217;addancin kisan kiyashin da Isra&#8217;ila ke yi ya \u0199ara wayar da kan jama&#8217;a game da gaskiyar lamarin,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma tunatar da cewa, a baya-bayan nan wasu kasashe tara sun amince da kasar Falasdinu, inda ya bayyana \u0199warin gwiwar cewa sauran kasashen ma za su bi sahun.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ta ce &#8220;Kasar Falasdinu an lalata. Gaskiya ne abokaina, ya kamata mu rungumi wannan a cikin labarinmu da kuma ayyukanmu,&#8221; in ji Fidan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ya ce ra&#8217;ayin ba da shawara na kotun kasa da kasa da kuma kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai kwanan wata 10 ga Mayun 2024, ya bude wata sabuwar hanya tare da kara da cewa: &#8220;Yanzu, mun kasance abu \u0257aya ne ba mu kai ga samu ba a kan manufarmu.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Ya kamata kasar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba ta Majalisar Dinkin Duniya,&#8221; ya jaddada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya kuma ce mamayar da Falasdinu ke yi ba ta ta\u0253a samar da zaman lafiya ko \u0199arin tsaro a Isra&#8217;ila ba, yana mai cewa &#8220;aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu zai kuma tabbatar da tsaro mai \u0257orewa ga kowa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Fidan ya kuma tunatar da cewa, Turkiyya ta ba da shawarar kafa wata hanyar tabbatar da tsaro don magance bukatun tsaron kasashen biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<blockquote><p>Ya kara da cewa &#8220;Batun kasashe biyu karshen magana ne, kuma ya kamata a aiwatar da shi tun kafin lokaci ya \u0199ure.&#8221;TRT Afarka Hausa.<\/p><\/blockquote>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki matakin Isra&#8217;ila na \u0199in aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, ya kuma yi gargadin cewa matsalar Falasdinu da ba a warware ta ba na barazana ga zaman lafiyar yankin baki daya. &nbsp; Fidan ya bayyana a ranar alhamis yayin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3267,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3266","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3266","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3266"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3266\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3268,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3266\/revisions\/3268"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3267"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3266"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3266"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3266"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}