{"id":3235,"date":"2024-09-26T16:19:27","date_gmt":"2024-09-26T16:19:27","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3235"},"modified":"2024-09-26T16:19:28","modified_gmt":"2024-09-26T16:19:28","slug":"rikici-yana-cigaba-da-barkiwa-a-babban-birnin-%c6%99asar-sudan-khartoum","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3235","title":{"rendered":"Rikici Yana Cigaba Da Barkiwa a Babban Birnin \u0199asar Sudan (Khartoum)"},"content":{"rendered":"\n<p>Sojojin kasar Sudan sun \u0199addamar da hare-hare ta sama a babban birnin kasar a jiya Alhamis a wani samame mafi girma na sake samun galaba a can a yakin da suka kwashe watanni 17 suna yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF) kamar yadda shaidu da majiyoyin soji suka bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p>Yunkurin da sojojin suka yi, wadanda suka rasa iko da galibin babban birnin kasar a farkon rikicin, ya zo ne gabanin jawabin da kwamandansu, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya yi, a taron Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a yammacin jiya.<\/p>\n\n\n\n<p>Shaidu sun ba da rahoton tashin bama-bamai da fa\u0257ace-fa\u0257ace a lokacin da dakarun soji ke \u0199o\u0199arin \u0199etara gadojin kogin Nilu da ke hade garuruwa uku da ke ma\u0199wabtaka da su da suka \u0199unshi babban birnin kasar, Khartoum, Omdurman da Bahri.<\/p>\n\n\n\n<p>Ko da yake sojojin sun sake \u0199wace wani yanki a Omdurman a farkon wannan shekara, sun dogara ne a kan manyan bindigogi da hare-hare ta sama kuma sun kasa kakkabe ingantattun dakarun RSF na kasa da suka jibge a wasu sassan babban birnin kasar.<\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau, kungiyar ta RSF ta ci gaba da samun ci gaba a wasu sassan kasar Sudan a &#8216;yan watannin baya-bayan nan, a rikicin da ya haifar da bala&#8217;in jin\u0199ai, wanda ya raba mutane sama da miliyan 10 da muhallansu, tare da jefa sassan kasar cikin matsananciyar yunwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Yunkurin diflomasiyya na Amurka da sauran manyan kasashen duniya ya ci tura, inda sojojin suka \u0199i halartar tattaunawar a watan da ya gabata a kasar Switzerland.<\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afrika Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sojojin kasar Sudan sun \u0199addamar da hare-hare ta sama a babban birnin kasar a jiya Alhamis a wani samame mafi girma na sake samun galaba a can a yakin da suka kwashe watanni 17 suna yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF) kamar yadda shaidu da majiyoyin soji suka bayyana. Yunkurin da sojojin suka yi, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3236,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3235","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3235","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3235"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3235\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3237,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3235\/revisions\/3237"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3236"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3235"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3235"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3235"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}