{"id":3218,"date":"2024-09-25T03:07:07","date_gmt":"2024-09-25T03:07:07","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3218"},"modified":"2024-09-25T03:07:08","modified_gmt":"2024-09-25T03:07:08","slug":"shugaban-kasar-turkiyya-recep-tayyip-erdogan-ya-yi-kakkausan-bayanai-a-gaban-mdd-akan-irin-kisan-kare-dangi-da-israila-take-yi-a-gaza","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3218","title":{"rendered":"Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Ya Yi Kakkausan Bayanai a\u00a0 Gaban MDD Akan Irin Kisan Kare Dangi Da Isra&#8217;ila Take Yi a Gaza"},"content":{"rendered":"\n<p>Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya matsa wa shugabannin kasashen duniya lamba da su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Ina gayyatar kasashen da har yanzu ba su amince da Falasdinu ba da su tsaya kan dama ta tarihi a wannan mawuyacin lokaci da kuma amincewa da kasar Falasdinu cikin gaggawa,&#8221; in ji Shugaba Erdogan a cikin jawabinsa ga Majalisar Dinkin Duniya a New York ranar Talata.Erdo\u011fan ya kara da cewa, dole ne a daina jinkirin samar da kasar Falasdinu mai cikakken &#8216;yanci, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta da kuma tabbatar da yankinta.<\/p>\n\n\n\n<p>Shugaban na Turkiyya ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kasa daukar kwararan matakai na kawo karshen tashe-tashen hankula, yana mai jaddada cewa kungiyar ta yi kasa a gwiwa.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin &#8216;yan shekarun nan, Majalisar Dinkin Duniya ta kasa aiwatar da aikinta na tushe, sannu a hankali tana rikidewa zuwa tsarin da ba shi da inganci, mai wahala, da rashin aiki,&#8221; in ji Erdogan, yana mai jaddada bukatar yin kwaskwarima a cikin duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Da ya karkata akalarsa kan halin da ake ciki a Gaza, Shugaba Erdogan ya yi Allah wadai da matakan da Isra&#8217;ila take dauka.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Sakamakon hare-haren da Isra&#8217;ila ke kaiwa, Gaza ta zama makabartar yara da mata mafi girma a duniya,&#8221; in ji shi, yana mai jaddada munanan asarar rayukan fararen hula da ake samu.<\/p>\n\n\n\n<p>Erdogan ya kuma yi kakkausar suka ga kafafen yada labarai na kasa da kasa, inda ya zarge su da rufe ido kan kisan da sojojin Isra&#8217;ila ke yi wa &#8216;yan jarida.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ga kungiyoyin watsa labarai na kasa da kasa, ina tambaya: Shin ba a kashe &#8216;yan jaridun a shirin talabijin da ake watsawa kai tsaye ba, kuma abokan aikinku Isra&#8217;ila ne suka kai farmaki ofishinsu?&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra&#8217;ila ta yi watsi da muhimman hakkokin bil adama, tana aiwatar da kisan kiyashi a fili ga wata al&#8217;umma tare da mamaye yankunansu mataki-mataki. <\/p>\n\n\n\n<p>Falasdinawa suna amfani da halattaccen &#8216;yancinsu na tsayin daka kan wannan mamaya.&#8221;&#8221;Me kuke jira don kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza?<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;A wani kalubale kai tsaye ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya nuna shakku kan rashin daukar matakin da suka dace wajen fuskantar kisan kare dangi a Gaza.<\/p>\n\n\n\n<p>Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, me kuke jira don dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, ku ce &#8216;ya isa&#8217; ga wannan zalunci, wannan dabbanci?<\/p>\n\n\n\n<p>Erdogan ya kara da cewa, ba kananan yara kadai ba, har ma da tsarin Majalisar Dinkin Duniya na mutuwa a Gaza.. Gaskiyar dabi&#8217;un da Kasashen Yammacin Duniya ke ikirarin karewa suna mutuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma yi kakkausar suka ga wadanda ke da alhakin haddasa rashin zaman lafiya a yankin.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Me kuke jira don dakatar da wannan hanyar tsari na kisan kiyashi da ke jawo duk yankin cikin ya\u0199i don burin siyasa?&#8221; Erdogan ya tambaya.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Kamar yadda kawancen bil adama ya dakatar da Hitler shekaru 70 da suka gabata, dole ne a dakatar da Netanyahu da masu goya masa baya ta hanyar ha\u0257in gwiwar bil adama.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afarka Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya matsa wa shugabannin kasashen duniya lamba da su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. &#8220;Ina gayyatar kasashen da har yanzu ba su amince da Falasdinu ba da su tsaya kan dama ta tarihi a wannan mawuyacin lokaci da kuma amincewa da kasar Falasdinu cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3219,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3218","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3218","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3218"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3218\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3220,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3218\/revisions\/3220"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3219"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3218"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3218"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3218"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}