{"id":3215,"date":"2024-09-24T13:20:20","date_gmt":"2024-09-24T13:20:20","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3215"},"modified":"2024-09-24T13:20:21","modified_gmt":"2024-09-24T13:20:21","slug":"lokaci-ya-yi-da-za-a-daina-biyan-tallafin-man-fetur-a-najeriya-dangote","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3215","title":{"rendered":"Lokaci ya yi da za a daina biyan tallafin man fetur a Najeriya \u2013 Dangote"},"content":{"rendered":"\n<p>Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta daina biyan ku\u0257in tallafin man fetur.<\/p>\n\n\n\n<p>Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da Blomberg a ranar Litinin, inda ya ce biyan tallafin na sa gwamnatin \u201ckashe ku\u0257a\u0257en da bai kamata ba,\u201d wanda hakan ya sa akwai bu\u0199atar a dakatar da shi, sannan ya \u0199ara da cewa ita kanta gwamnatin Najeriya ba za ta iya cigaba da biyan ku\u0257in tallafin ba.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cIna tunanin lokaci ya yi da za a daina biyan ku\u0257in tallafin nan domin dukkan \u0199asashe sun daina biya.\u201cFarashin man fetur \u0257inmu kusan kashi 60 ne farashin \u0199asashen da muke ma\u0199wabtaka da su, kuma iyakokinmu babu cikakken tsaro. <\/p>\n\n\n\n<p>Don haka ba za a iya cigaba da kashe irin ku\u0257a\u0257en nan ba,\u201d kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da Bloomberg.<\/p>\n\n\n\n<p>Dangote ya \u0199ara da cewa man fetur \u0257in da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen rage wa Naira nauyi.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce, \u201cBatun tallafin fetur magana ce babba. <\/p>\n\n\n\n<p>Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su ri\u0199a \u0199ara yawan abun domin su samu \u0199arin ku\u0257a\u0257e sannan sai nauyin ya \u0199are a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki \u0257aya.<\/p>\n\n\n\n<p>Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. <\/p>\n\n\n\n<p>Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya fa\u0257a maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi.<\/p>\n\n\n\n<p> Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. <\/p>\n\n\n\n<p>Amma mu yanzu za mu iya kididdigewa. <\/p>\n\n\n\n<p>Sannan za mu saka na\u2019urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban matatar man fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta daina biyan ku\u0257in tallafin man fetur. Dangote ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da Blomberg a ranar Litinin, inda ya ce biyan tallafin na sa gwamnatin \u201ckashe ku\u0257a\u0257en da bai kamata ba,\u201d wanda hakan ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3216,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3215","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3215","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3215"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3215\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3217,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3215\/revisions\/3217"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3216"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3215"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3215"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3215"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}