{"id":3209,"date":"2024-09-23T20:48:02","date_gmt":"2024-09-23T20:48:02","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3209"},"modified":"2024-09-23T20:48:04","modified_gmt":"2024-09-23T20:48:04","slug":"an-kashe-jagoran-yan-bindigar-kaduna-a-rikicin-yan-fashin-daji","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3209","title":{"rendered":"An Kashe Jagoran \u2019Yan Bindigar Kaduna a Rikicin \u2019Yan Fashin Daji"},"content":{"rendered":"\n<p>Wani fitaccen jagoran \u2019yan bindiga a Jihar Kaduna, Kachalla Tukur Sharme, ya gamu da ajalinsa a rikicin da ya barke tsakanin kungiyoyin \u2019yan ta\u2019adda masu gaba da juna.<\/p>\n\n\n\n<p>Kachalla Tukur Sharme shi ne wanda ya jagranci sace dalibai 121 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kujama a ranar 5 ga Yuli, 2021.<\/p>\n\n\n\n<p>Shi da yaransa da dama sun sheka lahira ne a wani \u0199azamin fada tsakaninsu da abokan gabansu \u2019yan bindiga a Dajin Rijana da ke Jihar Kaduna, a cewar kwamishinan tsaro, Samuwal Aruwan, a ranar Litinin.<\/p>\n\n\n\n<p>Kwamishin ya ce an kashe \u2019yan bindiga biyu daya bangaren, a musayar wutar wadda majiyoyin leken asiri suka ruwaito cewa \u2019yan bindiga biyar sun jikkata, kuma a halin yanzu suna buya a yankin, inda suke neman agajin jinyar raunukan da suka samu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cSharme, wani dan bindiga da ya garkuwa da daruruwan mutane, ya kuma yi awon gaba da shanun da ba za su kirgu ba, amma ya gamu da ajalinsa a yakin da aka yi tsakanin kungiyarsa da wasu \u2019yan fashin daji.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cRikicin ya faru ne a karshen mako a wani wuri da ake kira \u2018Hambakko\u2019, a cikin Dajin Rijana da Kaso, wanda ya hada da Kachia da wasu sassan kananan hukumomin Chikun da Kajuru,\u201d inji shi.<\/p>\n\n\n\n<p>Aruwan ya kara da cewa, Sharme ya sha guje wa jami\u2019an tsaro da kyar, kuma ana nemansa ruwa a jallo kafin a harbe shi har lahira.<\/p>\n\n\n\n<p>Kwamishinan ya kara da cewa, Sharme da yaransa ne ke da alhakin kai hare-hare, kashe-kashe, da kuma garkuwa da mutane a yankunan Millennium City, Maraban Rido, Kujama, Kajuru, Maro, da kauyukan da ke yankin Kateri, da kuma wasu kananan hukumomin Kagarko, Kachia da Birnin Gwari.<\/p>\n\n\n\n<p>Har ila yau ayyukan ta\u2019addancin da ya aikata sun tsallaka har zuwa jihohin Katsina da Nijar da ke makwabtaka da Kaduna, wadanda su ma suke fama da ta\u2019addanci.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya bayyana cewa daya daga cikin munanan ayyukan da Kachalla Sharme akwai sace dalibai 121 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kujama a ranar 5 ga Yuli, 2021.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya kuma gargadi mazauna garuruwan Rijana, Kaso, Kasarami, Jaka da-Rabi, Kajuru, da kuma Dutse da kada su taimaka wa duk wani mutum da ke dauke da raunin harbin bindiga.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya bukace su da su tuntubi jami\u2019an tsaro mafi kusa ko kuma su isa dakin aikin tsaro na jihar Kaduna.<\/p>\n\n\n\n<p>Mai rahoto;<br>Salihu Garba.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wani fitaccen jagoran \u2019yan bindiga a Jihar Kaduna, Kachalla Tukur Sharme, ya gamu da ajalinsa a rikicin da ya barke tsakanin kungiyoyin \u2019yan ta\u2019adda masu gaba da juna. Kachalla Tukur Sharme shi ne wanda ya jagranci sace dalibai 121 daga makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke Kujama a ranar 5 ga Yuli, 2021. Shi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3210,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3209","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3209","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3209"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3209\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3211,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3209\/revisions\/3211"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3210"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3209"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3209"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3209"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}