{"id":3194,"date":"2024-09-19T20:21:17","date_gmt":"2024-09-19T20:21:17","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3194"},"modified":"2024-09-19T20:21:18","modified_gmt":"2024-09-19T20:21:18","slug":"gwamnan-kano-abba-kabir-yusuf-ya-sauke-shugabannin-ri%c6%99o-na-kananan-hukumomin-jihar-44","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3194","title":{"rendered":"Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke Shugabannin Ri\u0199o na Kananan Hukumomin Jihar 44"},"content":{"rendered":"\n<p>Gwamanan ya \u0257auki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin da taron ban-kwana da shugabannin na ri\u0199o da aka yi a gidan gwamnatin Kano.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Abba Kabir Yusuf ya rusa kwamitocin ri\u0199o na \u0199ananan hukumomin jihar 44, kamar yadda wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamanan ya \u0257auki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin taron ban-kwana da shugabannin na ri\u0199o da aka yi a fadar gwamnatin Kano.Sanarwar ta ce an rushe kwamitocin ri\u0199on ne bayan sun cika wa&#8217;adin watanni shida da gwamnan ya ba su.<\/p>\n\n\n\n<p>Abba Kabir ya yaba wa shugabannin da aka sauke, yana mai cewa jajiricewarsu ta taimaka wajen taimakon gwamnatin gudanar da kyawawan manufofi.<\/p>\n\n\n\n<p>Gwamnan ya umarci shugabannin da aka sauke su mi\u0199a ragamar tafiyar da al&#8217;amura ga daraktocin mulki na kananan hukumomin, har zuwa lokacin da za a za\u0253i sababbin shugabanni.<\/p>\n\n\n\n<p>Halaccin shugabannin ri\u0199oA ranar 26 ga watan Oktoba ne hukumar zaben jihar mai zaman kanta za ta gudanar da za\u0253en shugabannin \u0199ananan hukumomin jihar 44, kamar yadda hukumar ta sanar.Jihar Kano da sauran mafi yawan jihohin \u0199asar dai ba su da za\u0253a\u0253\u0253un shugabanni a matakan \u0199ananan hukumomi, inda shugabannin ri\u0199o suke jagorantar matakin na gwamnati, wanda ya fi kusa da jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Yulin 2024 ne Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa na\u0257a shugabannin ri\u0199o ga \u0199ananan hukumomi ya sa\u0253a wa doka.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga nan ne jihohin \u0199asar da dama suka sanar da lokacin gudanar da za\u0253en \u0199ananan hukumomi. <\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afarka Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamanan ya \u0257auki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin da taron ban-kwana da shugabannin na ri\u0199o da aka yi a gidan gwamnatin Kano. Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Abba Kabir Yusuf ya rusa kwamitocin ri\u0199o na \u0199ananan hukumomin jihar 44, kamar yadda wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3195,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3194","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3194","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3194"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3194\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3196,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3194\/revisions\/3196"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3195"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3194"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3194"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3194"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}