{"id":3174,"date":"2024-09-18T11:05:14","date_gmt":"2024-09-18T11:05:14","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3174"},"modified":"2024-09-18T11:05:15","modified_gmt":"2024-09-18T11:05:15","slug":"israila-na-amfani-da-daimon-%c9%97in-afirka-don-tallafawa-kisan-%c6%99are-nangi-a-gaza","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3174","title":{"rendered":"Isra&#8217;ila Na Amfani Da Daimon \u0257in Afirka Don Tallafawa Kisan \u0199are Nangi a Gaza."},"content":{"rendered":"\n<p>(kashi na farko)<\/p>\n\n\n\n<p>Ta hanyar wani salon cin hanci da rashawa da yaudara, Isra&#8217;ila ta tsunduma cikin kasuwancin lu&#8217;u-lu&#8217;u mai araha a cikin DRC. <\/p>\n\n\n\n<p>Ga yadda suke girbar ribar a bulusWasu masu hakar zinari suke tona wani rami a ma&#8217;adinan Chudja da ke yankin Kilomoto kusa da kauyen Kobu, mai tazarar kilomita 100 daga Bunia a arewa maso gabashin Kongo.\u00a0 Daga Zeynep ConkarIsra&#8217;ila na daga cikin kasashe biyar masu fitar da gogaggen lu&#8217;ulu&#8217;u duk da rashin albarkatun lu&#8217;u-lu&#8217;u nata na kanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Ta yaya hakan ke aiki?Wani rahoto na Kimberley Process (wani shiri na duniya na hana &#8220;lu\u2019ulu\u2019un jini&#8221; shiga kasuwa) ya bayyana cewa shida daga cikin manyan kasashe goma masu samar da lu\u2019u-lu\u2019u na Afirka ne, inda har yanzu yankuna da dama ke fama da rikici kan yankuna masu arzikin lu\u2019u-lu\u2019u.<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin shekarun da suka gabata, Isra&#8217;ila ta \u0199ara fadada kasancewarta a Afirka ta hanyar sabbin saka hannun jari kuma ta sami riba sosai daga ma&#8217;adinan lu&#8217;u-lu&#8217;u na Afirka.Kasuwancin da take yi don sayen kayan ya\u0199i na soji, ana zargin kamfanonin Isra&#8217;ila da ke da ala\u0199a da sojoji sun sami damar yin amfani da lu&#8217;u-lu&#8217;u da sauran ma&#8217;adanai a farashi mai muhimmanci, wanda ke taimaka wa masana&#8217;antar lu&#8217;u-lu&#8217;u ta Isra&#8217;ila bun\u0199asa.<\/p>\n\n\n\n<p>A sakamakon haka, masana&#8217;antar lu&#8217;u-lu&#8217;u ta Isra&#8217;ila tana da hannu dumu-dumu a cinikin lu&#8217;u-lu&#8217;u na jini\u2014kasuwancin da ke cike da wahalar \u0257awainiyar miliyoyin mutane.An bullo da kalmar &#8220;lu&#8217;u lu&#8217;un jini&#8221; ne saboda nuna yadda ake amfani da kasuwancinsa wajen take hakkin bil&#8217;adama a duniya, musamman a kasashen Afirka da ke fama da ya\u0199e-ya\u0199e.<\/p>\n\n\n\n<p>Batun lu&#8217;u-lu&#8217;u na jini da kuma hako ma&#8217;adanai masu daraja ba bisa ka&#8217;ida ba a yankunan da ake fama da rikici irin su Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) ya kasance cikin rubuce-rubuce a cikin shekaru da dama, in ji Habibu Djuma, wani mai bincike a Cibiyar Koyarwa da Horar da Harkokin Kasuwanci ta Afirka (AKEM).<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan ma&#8217;adanai galibi ana hako su ne a cikin yanayi na tashin hankali, tare da amfani da ribar da ake samu don tallafa wa \u0199ungiyoyi masu \u0257auke da makamai da ke taimakawa wajen tsawaita rikici,&#8221; in ji Djuma.<\/p>\n\n\n\n<p>DRC tana fama da kungiyoyi da dama masu dauke da makamai, musamman a yankunan gabashin kasar, musamman kungiyar M23, wadda ke da karfi a lardin Kivu ta Arewa, tare da wasu bangarori na lardin Ituri da Kudancin Kivu, a cewar Espoir Ngalukiye, wani mai fafutukar siyasa a DRC.\u201cWadannan kungiyoyi masu dauke da makamai sun yi \u0199aurin suna wajen take hakkin dan adam da suke yi. <\/p>\n\n\n\n<p>Suna da hannu cikin tashe-tashen hankula da suka hada da kashe fararen hula da cin zarafi ta hanyar jima&#8217;i, suna aikata laifukan cin zarafin bil&#8217;adama da dama,&#8221; in ji Ngalukiye.<\/p>\n\n\n\n<p>Wa\u0257annan lu&#8217;u-lu&#8217;u suna rura wutar ya\u0199in basasa kuma suna ba da gudunmawa ga ya\u0257uwar wahala, musamman a \u0199asashe kamar Saliyo, Angola, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Cango.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cLu\u2019u lu\u2019u da ke dabaibaye da rikice-rikice, wanda kuma aka fi sani da lu\u2019ulu\u2019u na jini, lu\u2019ulu\u2019u ne da ake ha\u0199owa a wuraren da ake ya\u0199i ana sayar da su don samun kudin shiga ga masu tayar da kayar baya da shugabannin yaki, ko kuma sojojin mamaya.<\/p>\n\n\n\n<p>Al&#8217;ummar duniya, ta hanyar tsarin tabbatar da tsarin Kimberley, sun dauki matakan da\u0199ile kwararar wadannan lu&#8217;u-lu&#8217;u, amma duk da haka, haramtacciyar cinikayya ta ci gaba, musamman a yankunan da ake rikici kamar DRC,&#8221; in ji Djuma.<\/p>\n\n\n\n<p>Djuma ya ambaci cewa, alal misali, Uganda da Ruwanda, a tarihi suna da hannu wajen fasa \u0199waurin ma&#8217;adanai daga DRC, kuma kasashen biyu suna da alaka ta diflomasiyya da tsaro da Isra&#8217;ila.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A cikin wannan yanayin, tasirin Isra&#8217;ila ba lallai ba ne ya kasance a bayyane. Madadin haka, yana iya yin aiki ta hanyar masu zaman kansu, kasuwanci, ko hanyoyin sadarwar sirri wa\u0257anda ke cin gajiyar rashin zaman lafiya a yankin, \u201din ji Djuma. <\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afarka Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>A biyomu zamu cigaba.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>(kashi na farko) Ta hanyar wani salon cin hanci da rashawa da yaudara, Isra&#8217;ila ta tsunduma cikin kasuwancin lu&#8217;u-lu&#8217;u mai araha a cikin DRC. Ga yadda suke girbar ribar a bulusWasu masu hakar zinari suke tona wani rami a ma&#8217;adinan Chudja da ke yankin Kilomoto kusa da kauyen Kobu, mai tazarar kilomita 100 daga Bunia [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3175,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3174","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3174","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3174"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3174\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3176,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3174\/revisions\/3176"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3175"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3174"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3174"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3174"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}