{"id":3028,"date":"2024-09-09T16:55:10","date_gmt":"2024-09-09T16:55:10","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3028"},"modified":"2024-09-09T16:55:11","modified_gmt":"2024-09-09T16:55:11","slug":"an-yi-janaizar-baturkiyya-baamurkiya-yar-gwagwarmaya-da-aka-kashe-a-gabar-yammacin-kogin-jodan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=3028","title":{"rendered":"An Yi Jana&#8217;izar Baturkiyya-Ba&#8217;amurkiya &#8216;Yar Gwagwarmaya Da Aka Kashe a Gabar Yammacin Kogin Jodan"},"content":{"rendered":"\n<p>\u00a0Ya\u0199in Isra\u2019ila a Gaza ya shiga rana ta 339, inda ta kashe kusan Falas\u0257inawa 41,000 \u2013 yanwacinsu mata da yara \u2013 tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani \u0199iyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-ginen da aka rusa.\u018aaruruwan Falas\u0257inawa a birnin Nablus da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan sun yi jana\u2019izar Baturkiya Ba\u2019amurkiya \u2018yar gwagwaryma Aysenur Ezgi Eygi wadda sojojin Isra\u2019ila suka harbe a ranar Juma\u2019a.<\/p>\n\n\n\n<p>\u018aumbin mutane sun raka gawarta tun daga asibitin gwamnati na Rafidia da ke Nablus inda suka ratsa tituna da dama na \u0199asar inda suka rin\u0199a Allah wadai da zaluncin da Isra\u2019ila ke yi tare da jinjina wa \u0199asashen da ke taimaka musu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.<\/p>\n\n\n\n<p>Masu makoki sun gudanar da sallar jana&#8217;izar, karkashin jagorancin gwamnan Nablus Ghassan Daghlas, tare da halartar shugabanni daga bangarori daban-daban na Falasdinu da kuma dimbin jama&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>Sannan manyan ayyukan soja da Isra&#8217;ila ke yi a Ga\u0253ar Yamma da aka mamaye suna mummunan ta&#8217;azzara al&#8217;amura a yankin da dama tuni yake ciki &#8220;mawuyacin&#8221; yanayi, wanda ya \u0199ara ta&#8217;azzara irin ta&#8217;annatin da &#8216;yan kama-wuri-zauna ke yi, a cewar babban jami&#8217;in kare ha\u0199\u0199in \u0257an adam na Majalisar \u018ainkin Duniya (MDD).<\/p>\n\n\n\n<p>Da yake bu\u0257e wani taro na Hukumar Kula da Ha\u0199\u0199in Dan Adam ta Majalisar \u018ainkin Duniya a Geneva, Volker Turk ya koka kan yadda ake \u0199ara aikata ta&#8217;annati a Ga\u0253ar Yamma, a lokacin da Isra&#8217;ila ke ci gaba da kai manyan hare-hare.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>A Ga\u0253ar Yamma, mummunan ayyukan da ake yi, wasu a wani irin mataki da ba a ta\u0253a gainin irinsa ba a cikin shekaru 20, suna ta&#8217;azzara yanayin da ake ciki, wanda dama tuni ya ta\u0253ar\u0253are, saboda ta&#8217;annatin da &#8216;yan kam-wuri-zauna suke yi, kamar yadda Turk ya shaida wa Majalisar.<\/p>\n\n\n\n<p>A wani Karin kai harin Sojojin Isra&#8217;ila, sun kai farmaki a garin Tulkarem da sansanin &#8216;yan gudun hijira na Balata da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan.<\/p>\n\n\n\n<p>Dakarun mamaya na Isra&#8217;ila sun mamaye Tulkarem bayan tsakar dare, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinawa Wafa ya bayyana.<\/p>\n\n\n\n<p>Rahoton ya kara da cewa, wasu motocin sojojin mamaya tare da rakiyar manyan buldoza guda biyu sun shiga birnin daga bangarensa na yammacin kasar, inda suka fara rusa ababen more rayuwa a yankin Al-Alemi, yayin da wani jirgin sama mara matuki na sa ido ya yi ta shawagi ta saman birnin.<\/p>\n\n\n\n<p>Wafa ya kuma ruwaito cewa, sojojin Isra&#8217;ila sun kai farmaki sansanin &#8216;yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus tare da rakiyar buldoza ta soji, lamarin da ya kai ga arangama da dakarun gwagwarmayar Falasdinawa.Shaidun gani da ido sun ce an yi arangama tsakanin Falasdinawa da sojoji a kofar shiga sansanin.<\/p>\n\n\n\n<p>Masu fafutuka sun yada bidiyon da ke nuna motocin soji da kuma buldoza yayin farmakin.<\/p>\n\n\n\n<p>\u00a0Majalisar ministocin tsaron Isra&#8217;ila ta yi taro don magance tashe-tashen hankula a Gabar Yammacin Kogin JordanMa&#8217;aikatar tsaron Isra&#8217;ila karkashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu, ta yi taro domin tattauna muhimman batutuwa da dama, musamman tabarbarewar yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda hukumar yada labaran kasar ta sanar.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumar ta yi nuni da cewa Netanyahu ya bude zaman, inda aka tattauna batutuwa da dama, tare da mai da hankali kan yadda al&#8217;amura ke kara tabarbarewa a yankin Falasdinu da aka mamaye.<\/p>\n\n\n\n<p>Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gaza, sojojin Isra&#8217;ila sun fadada ayyukansu tare da kara kai hare-hare a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, lamarin da ya yisanadin mutuwar Falasdinawa 692 tare da jikkata wasu kimanin 5,700, baya ga wadanda aka kama a cewar majiyoyin hukumomin Falasdinu.<\/p>\n\n\n\n<p>A yayin ganawar, Netanyahu ya kuma tabo ziyarar da ministocin gwamnati ke yawan kaiwa Masallacin \u0198udus.<\/p>\n\n\n\n<p>TRT Afrika Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u00a0Ya\u0199in Isra\u2019ila a Gaza ya shiga rana ta 339, inda ta kashe kusan Falas\u0257inawa 41,000 \u2013 yanwacinsu mata da yara \u2013 tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani \u0199iyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-ginen da aka rusa.\u018aaruruwan Falas\u0257inawa a birnin Nablus da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan sun [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3029,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-3028","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3028","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3028"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3028\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3030,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3028\/revisions\/3030"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/3029"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3028"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3028"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3028"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}