{"id":2989,"date":"2024-09-07T10:55:03","date_gmt":"2024-09-07T10:55:03","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2989"},"modified":"2024-09-07T10:55:04","modified_gmt":"2024-09-07T10:55:04","slug":"cbn-zai-sayar-wa-yan-canji-dala-kan-1580","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2989","title":{"rendered":"CBN zai sayar wa &#8216;yan canji dala kan 1,580"},"content":{"rendered":"\n<p>Babban Bankin Nijeriya CBN ya ce zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane \u0257an canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike gi\u0253in da ake da shi na dala a kasuwar hada-hadar ku\u0257a\u0257en waje.Wannan matakin da CBN \u0257in ya \u0257auka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya \u0257auka domin daidaita farashin dala da naira a kasuwar canji. <\/p>\n\n\n\n<p>Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewa zai sayar wa \u2018yan canji dala kan naira 1,580.<\/p>\n\n\n\n<p>Bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma\u2019a a daidai lokacin da ake fuskantar \u0199arancin dalar a kasuwannin bayan fage.<\/p>\n\n\n\n<p>Bankin ya sanar da cewa zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane \u0257an canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike gi\u0253in da ake da shi.Sai dai bankin ya ce bai amince ga \u2018yan canjin su sayar da dalar sama da kashi \u0257aya cikin 100 na kan yadda suka same ta daga CBN ba.<\/p>\n\n\n\n<p>CBN \u0257in ya bu\u0199aci \u2018yan canjin da suke da rajista kuma suka cancanta da ke bu\u0199atar wa\u0257annan ku\u0257a\u0257e kan su biya ku\u0257insu a naira ga asusun saka ku\u0257i na babban bankin.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakazalika bankin ya ce hada-hadar biyan ku\u0257in da bayar da shaida da kar\u0253a dala 20,000 \u0257in duka \u2018yan canjin za su iya zuwa ofisoshin babban bankin da ke Abuja ko Awka ko Kano ko kuma Legas.Wannan matakin da CBN \u0257in ya \u0257auka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya \u0257auka domin daidaita farashin dala da naira a kasuwar canji.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka kuma matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka rin\u0199a sayar da dalar a kan naira 1,670 a kasuwannin bayan fage a fa\u0257in \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>A baya CBN \u0257in ya ta \u0257aukar jerin matakai domin tabbatar da cewa naira ta samu tagomashi a kasuwar hada-hadar ku\u0257a\u0257en waje, sai dai lamarin ya ci tura, inda dalar ke ci gaba da tashi.<\/p>\n\n\n\n<p> TRT Afrika Hausa.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Babban Bankin Nijeriya CBN ya ce zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane \u0257an canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike gi\u0253in da ake da shi na dala a kasuwar hada-hadar ku\u0257a\u0257en waje.Wannan matakin da CBN \u0257in ya \u0257auka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya \u0257auka domin daidaita farashin dala [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2990,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2989","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2989","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2989"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2989\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2991,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2989\/revisions\/2991"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2990"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2989"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2989"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2989"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}