{"id":2947,"date":"2024-09-05T07:41:08","date_gmt":"2024-09-05T07:41:08","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2947"},"modified":"2024-09-05T07:41:09","modified_gmt":"2024-09-05T07:41:09","slug":"turkiyya-da-masar-suna-da-bu%c6%99atu-iri-%c9%97aya-kan-lamuran-da-suka-shafi-falas%c9%97inawa-kuma-dukkansu-suna-son-ganin-israila-ta-gaggauta-daina-kai-hare-hare-a-gaza-a-cewar-shugaba-recep-tay","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2947","title":{"rendered":"Turkiyya da Masar suna da bu\u0199atu iri \u0257aya kan lamuran da suka shafi Falas\u0257inawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra&#8217;ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan."},"content":{"rendered":"\n<p>\u201cGudunmawar da Turkiyya da Masar suke bayarwa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tana da matu\u0199ar muhimmanci,\u201d in ji Erdogan ranar Laraba, a yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai tare da takwaransa na \u0199asar Masar Abdel Fattah el Sisi, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya.<\/p>\n\n\n\n<p>Wannan ce ziyarar aiki ta farko da Sisi ya kai Turkiyya tun da ya soma mulki a 2014. Ya kai ziyarar ce sakamakon gayyatar da Erdogan ya yi masa.<\/p>\n\n\n\n<p>A wani \u0253angare na ziyarar da Sisi yake yi, shugabannin biyu sun jagoranci wani Babban Taro Kan Ha\u0257in-Kai tsakanin \u0199asashen biyu tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 a fannoni daban-daban.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Mun jaddada aniyarmu ta ha\u0257in-kai a dukkan \u0253angarori, ciki har da masana&#8217;antu da cinikayya da tsaro da kiwon lafiya da muhalli da makamashi,\u201d a cewar Erdogan, wanda ya \u0199ara da cewa \u0199asashen biyu za su kyautata ala\u0199a a tsakaninsu ta yadda kowane \u0253angare zai &#8220;ci moriyarta.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>A nasa \u0253angaren, Sisi ya ce ziyarar da ya kai Turkiyya &#8220;ta bu\u0257e sabuwar hanya a fannin tattalin arziki da cinikayya,\u201d sannan ya jaddada matsayin \u0199asashen biyu game da \u201cwajabcin tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo \u0199arshen hare-haren da Isra&#8217;ila take kai wa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.\u201d<\/p>\n\n\n\n<p>DA\u0257A\u0257\u0257EN TARIHI NA ABBATO<br>Turkiyya da Masar, wa\u0257anda suka kasance biyu daga cikin manyan \u0199asashen Gabas ta Tsakiya, suna ci gaba da \u0199arfafa ala\u0199ar da ke tsakaninsu a wani \u0253angare na shirin \u0199ara kusantar juna da suka \u0199addamar shekaru uku da suka gabata.<\/p>\n\n\n\n<p>A watan Fabarairu, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyara Masar, inda ya gana da Sisi tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi a fannin yawon bu\u0257e ido da al&#8217;adu da ilimi.<\/p>\n\n\n\n<p>Cinikayya ita ce ma\u0199asudin \u0199arfafa ala\u0199a a tsakanin Turkiyya da Masar. \u0198asashen biyu suna fatan \u0199ara cinikayya a tsakaninsu da a\u0199alla kashi 50, wato daga dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 15.<\/p>\n\n\n\n<p>Turkiyya na cikin manyan \u0199asashen da suka fi gudanar da harkokin kasuwanci da Masar a shekaru 10 da suka gabata.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198asashen biyu suna da da\u0257a\u0257\u0257en tarihi na abota. A shekara mai zuwa ne Turkiyya da Masar za su cika shekara 100 da \u0199ulla dangantakar diflomasiyya.<\/p>\n\n\n\n<p>SANARWAR HA\u0257IN-GWIWA<br>A sanarwar ha\u0257in-gwiwar da Turkiyya da Masar suka fitar bayan kammala Babban Taro Kan Ha\u0257in-Kai a tsakaninsu, Ankara da Kairo sun jaddada ha\u0257in gwiwarsu wajen goyon bayan Falas\u0257inu da kawo \u0199arshen hare-haren da Isra&#8217;ila take kai wa Gaza.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198asashen biyu sun ce Falas\u0257inawa suna da &#8216;yancin samun \u0199asa mai cin gashin kanta, wadda Gabashin Birnin \u0198udus zai kasance babban birninta, bisa iyakokin da aka shata a 1967. Kazalika sun jaddada matsayarsu ta kare &#8216;yancin Falas\u0257inawa da aka kora daga gidajensu.<\/p>\n\n\n\n<p>Haka kuma sun jaddada goyon bayan Ira\u0199i a matsayin \u0199asa mai &#8216;yancin kansa da ke neman zaman lafiya, tare da goyon bayan ci gaban Ira\u0199i da yun\u0199urin sake gina ta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kazalika Turkiyya da Masar sun jaddada goyon bayansu ga tsarin siyasar al&#8217;ummar Libya kamar yadda MDD take yi, wada zai kasance mataki na tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ha\u0257in-kai na Libya.<\/p>\n\n\n\n<p>Da suke bayyana takaicinsu kan ya\u0199in Sudan, \u0199asashen biyu sun koka kan halin rashin jin\u0199ai da take ciki, wanda suka ce zai \u0199ara ta&#8217;azzara yanayin rashin jin\u0199ai a yankin, kana suka yi maraba da yun\u0199urin tabbatar da zaman lafiya a \u0199asar cikin diflomasiyya.<\/p>\n\n\n\n<p>Mai rahoto;<br>Mujaheed Tasi&#8217;u.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u201cGudunmawar da Turkiyya da Masar suke bayarwa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tana da matu\u0199ar muhimmanci,\u201d in ji Erdogan ranar Laraba, a yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai tare da takwaransa na \u0199asar Masar Abdel Fattah el Sisi, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya. Wannan ce ziyarar aiki ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2948,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2947","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2947","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2947"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2947\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2949,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2947\/revisions\/2949"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2948"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2947"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2947"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2947"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}