{"id":2940,"date":"2024-09-04T20:47:07","date_gmt":"2024-09-04T20:47:07","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2940"},"modified":"2024-09-04T20:47:08","modified_gmt":"2024-09-04T20:47:08","slug":"za-mu-tabbatar-da-cewa-babu-wanda-ya-sha-gabanmu-wajen-samar-da-ingantaccen-fetur-inji-dangote-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2940","title":{"rendered":"Za Mu Tabbatar Da Cewa Babu Wanda Ya Sha Gabanmu Wajen Samar Da Ingantaccen Fetur Inji Dangote"},"content":{"rendered":"\n<p>Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa sabuwar matatar da ke Legas za ta soma fitar da man fetur mai inganci a farashi mai rahusa haka kuma babu wanda zai sha gabansu wajen samar da ingantaccen fetur.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan ta shafe sama da shekara guda tana aiki, matatar ta Dangoten a halin yanzu ta soma samar fetur.<\/p>\n\n\n\n<p>Matatar wadda a baya take iya tace gangar mai 350,000 a duk rana, a halin yanzu ana sa ran za ta iya tace iya \u0199arfinta da aka sanar na ganga 650,000 a kullum zuwa \u0199arshen shekara.<\/p>\n\n\n\n<p>Hakan zai zama wani babban ci gaba ga \u0253angaren makamashi na Nijeriya. <\/p>\n\n\n\n<p>Dangoten ya \u0199ara shaida wa manema labarai cewa \u201cwannan ranar murna ce ga \u2018yan Nijeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201d\u201cDa zarar mun kammala warwarewa da NNPCL, kayayyakinmu za su soma shiga kasuwa. Za mu taimaka wurin farfa\u0257o da masana\u2019antu.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201dWannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu \u0199arin ku\u0257in mai a Nijeriya, lamarin da ya \u0199ara saka \u2018yan \u0199asar da dama \u0199orafi.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar Talata ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun \u0199ara farashin da ake sayar da man fetur \u0257in.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayanai daga sassan Nijeriya daban-daban na cewa sabon farashin ya bambanta, inda ake sayar da lita daya a Legas a kan naira 855 yayin da a wani bangare na shiyyar arewa maso yamma kuma ake sayar da shi a kan naira 904.<\/p>\n\n\n\n<p>A can bangaren arewa maso gabas kuma farashin fetur din ya kai naira 924 a kan kowace lita daya.<\/p>\n\n\n\n<p>Mai rahoto Mustapha Garba Usman<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kamfanin mai na Dangote ya sanar da cewa sabuwar matatar da ke Legas za ta soma fitar da man fetur mai inganci a farashi mai rahusa haka kuma babu wanda zai sha gabansu wajen samar da ingantaccen fetur. Bayan ta shafe sama da shekara guda tana aiki, matatar ta Dangoten a halin yanzu ta soma [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2916,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2940","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2940","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2940"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2940\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2941,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2940\/revisions\/2941"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2916"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2940"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2940"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2940"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}