{"id":2887,"date":"2024-09-02T17:12:42","date_gmt":"2024-09-02T17:12:42","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2887"},"modified":"2024-09-02T17:12:43","modified_gmt":"2024-09-02T17:12:43","slug":"israila-ta-cigaba-da-ruwa-bama-bamai-kan-fararen-hula-a-gaza","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2887","title":{"rendered":"Isra&#8217;ila Ta Cigaba Da Ruwa Bama-bamai Kan Fararen hula A Gaza"},"content":{"rendered":"\n<p> A ya\u0199in da Isra&#8217;ila ta kwashe kwana 332 tana yi a Gaza ta kashe Falas\u0257inawa fiye da 40,738 yawancinsu mata da yara sannan ta jikkata mutum fiye da 94,154, kuma ana da tabbacin mutum 10,000 na danne a \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-gine da ta rusa.<\/p>\n\n\n\n<p>Ma&#8217;aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka ma\u0199ale a \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-gine, yayin da Isra&#8217;ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024 dakarun Isra&#8217;ila sun kashe fararen-hula biyu tare da jikkata wasu bayan sun jefa bama-bamai a wani gida da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falas\u0257inu WAFA.<\/p>\n\n\n\n<p>Rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce ta \u0257auko gawawwaki guda biyu da kuma mutanen da suka jikkata daga gidan iyalan Araj da ke Jalaa Street bayan Isra&#8217;ila ta kashe su.<\/p>\n\n\n\n<p>Daga bisani adadin mutanen da suka mutu ya \u0199aru zuwa 11 bayan jiragen ya\u0199in Isra&#8217;ila sun kai hari a Makarantar Safad da ke kudu maso gabashin Gaza, inda &#8216;yan gudun hijira suka sami  mafaka.<\/p>\n\n\n\n<p>Ma&#8217;aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka ma\u0199ale a \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-gine, yayin da Isra&#8217;ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.Ministan harkokin wajen Saudiyya na yun\u0199urin ganin an daina kai hare-hare a Gaza. <\/p>\n\n\n\n<p>Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Turkiyya, Masar, Jordan, Bahrain da Gambia ranar Lahadi a yun\u0199urin ganin Isra&#8217;ila ta daina kai hare-hare a Gaza da kuma bai wa Falas\u0257inawa &#8216;yanci.<\/p>\n\n\n\n<p>Bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan game da bayanai na baya-bayan nan halin da Falas\u0257inawa suke ciki, inda ya mayar da hankali kan yun\u0199urin \u0199asashen Musulmai na ganin sun maido da martabar Falas\u0257inawa da kuma ha\u0257a-kai don kawo \u0199arshen hare-hare da keta hakkin da Isra&#8217;ila take yi wa Falas\u0257inawa.<\/p>\n\n\n\n<p>Da yake tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty, ya mayar da hankali kan halin da yankunan Falas\u0257inawa suke ciki da kuma bu\u0199atar \u0257aukar matakan gaggawa domin dakatar da rashin mutuncin da Isra&#8217;ila take yi wa Falas\u0257inawa, yayin da kuma ya jaddada bu\u0199atar samar da \u0199asar Falas\u0257inu mai cin gashin kanta.<\/p>\n\n\n\n<p>Kazalika a yayin da yake magana da Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya bayyana bu\u0199atar gagauta tsagaita wuta da kuma ha\u0257in-kan dukkan \u0199asashen Larabawa da na Musulmai wajen ganin an yi wa Falas\u0257inawa adalci, ciki har da \u0199ir\u0199iro musu \u0199asa mai cin gashin kanta. <\/p>\n\n\n\n<p>A cewar majiyarmu daga &#8216;yankin gabas ta tsakiya.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ya\u0199in da Isra&#8217;ila ta kwashe kwana 332 tana yi a Gaza ta kashe Falas\u0257inawa fiye da 40,738 yawancinsu mata da yara sannan ta jikkata mutum fiye da 94,154, kuma ana da tabbacin mutum 10,000 na danne a \u0199ar\u0199ashin \u0253araguzan gine-gine da ta rusa. Ma&#8217;aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2888,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2887","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2887","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2887"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2887\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2889,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2887\/revisions\/2889"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2888"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2887"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2887"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2887"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}