{"id":2884,"date":"2024-09-02T17:09:47","date_gmt":"2024-09-02T17:09:47","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2884"},"modified":"2024-09-02T17:09:48","modified_gmt":"2024-09-02T17:09:48","slug":"da-yuwar-wahalar-fetur-zata-kara-taazzara-a-nigeria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2884","title":{"rendered":"Da Yuwar Wahalar Fetur Zata Kara Ta&#8217;azzara a Nigeria"},"content":{"rendered":"\n<p>Tun da fari kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa bashin da ya yi yiwa NNPCL yana barazana ga tsarinsa na shigo da fetur Nijeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Kamfanin mai na gwamnatin Nijeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya amince cewa &#8220;masu shigo da fetur&#8221; suna binsa &#8220;dimbin bashi&#8221;, wanda ya ce yana barazana ga \u0257orewar tsarinsa na shigo da fetur \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Lahadi, ya ce \u201c\u0257imbin bashin ya sanya matsi sosai kan kamfanin kuma yana barazana ga \u0257orewar shigo da fetur\u201d.<\/p>\n\n\n\n<p>\u201cKamar yadda Dokokin Kamfanonin Man Fetur suka tanada, NNPCL zai ci gaba da sadaukawa a kan aikinsa na kasancewa madogara ta \u0199arshe game da shigo da fetur, domin tabbatar da yalwar makamashi,&#8221; in ji sanarwar.<\/p>\n\n\n\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, &#8220;Muna ha\u0257a kai sosai da hukumomin gwamnati da lamarin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki domin ci gaba da rarraba man fetur a fa\u0257in \u0199asar nan.<\/p>\n\n\n\n<p>NNPCL ya fitar da sanarwar ce a daidai lokacin da &#8216;yan Nijeriya suke shafe awanni da dama suna layi a gidajen mai ba tare da samun fetur ba a galibin lokaci sakamakon \u0199arancinsa a fa\u0257in \u0199asar.<\/p>\n\n\n\n<p>Farashin lita \u0257aya ta fetur ya ninka fiye da sau \u0257aya tun bayan da shugaban \u0199asar Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur a watan Mayu na shekarar 2023 a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, lamarin da &#8216;yan \u0199asar ke gani shi ya haddasa tashin gwauron zabin da kusan komai ya yi a \u0199asar.Yanzu haka dai ana sayar da lita \u0257aya ta fetur a kusan N1000, a wasu sassan kasar amma duk da haka bai wadataba a kasar.<\/p>\n\n\n\n<p>Nijeriya na cikin \u0199asashen da suke samar da \u0257anyen man fetur a duniya, sai dai ba ta iya tace shi sakamakon rashin aikin duka matatun manta, abin da ake \u0257ora alhakinsa kan rashawa da cin-hanci.<\/p>\n\n\n\n<p>Sau da dama NNPCL yana cewa za a gyara matatun sannan su ci gaba da aiki, amma shiru kake ji. <\/p>\n\n\n\n<p>TRT AFRIKA\u00a0 HUASA.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tun da fari kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa bashin da ya yi yiwa NNPCL yana barazana ga tsarinsa na shigo da fetur Nijeriya. Kamfanin mai na gwamnatin Nijeriya, Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya amince cewa &#8220;masu shigo da fetur&#8221; suna binsa &#8220;dimbin bashi&#8221;, wanda ya ce yana barazana ga \u0257orewar tsarinsa na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2885,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2884","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2884","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2884"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2884\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2886,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2884\/revisions\/2886"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2885"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2884"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2884"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2884"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}