{"id":2864,"date":"2024-09-01T16:35:07","date_gmt":"2024-09-01T16:35:07","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2864"},"modified":"2024-09-01T16:35:08","modified_gmt":"2024-09-01T16:35:08","slug":"facebook-ya-nemi-afuwar-cire-bayanan-firaministan-malaysia-kan-kisan-haniyeh","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2864","title":{"rendered":"Facebook  ya Nemi Afuwar Cire Bayanan Firaministan Malaysia Kan Kisan Haniyeh."},"content":{"rendered":"\n<p>Katafaren kamfanin fasahar sadarwa Meta ya nemi afuwa kan cire wasu bayanai da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya wallafa kan kisan gillar da aka yi wa shugaban bangaren siyasa na \u0199ungiyar Hamas Ismail Haniyeh.<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar Talata ne kamfanin ya nemi afuwar, kwana guda bayan ofishin Anwar ya gayyaci wakilan Meta don neman \u0199arin bayani game da dalilin da ya sa aka cire bayanan da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram kan mutuwar Haniyeh.Meta dai shi ne mallakin manyan shafukan sada zumuntar biyu.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;Muna neman afuwar kuskuren aiki inda aka cire bayanan da ke cikin shafin Facebook da na Instagram \u0257in Firaminista,&#8221; in ji Meta a cikin wata sanarwa da ya fitar.&#8221;Tuni aka dawo da bayanan daidai yadda aka wallafa tare da gasgata alamar tambarin.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Masu amfani da kafofin intanet na zargin manhajojin Meta da goge bayanai, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasar Hamas.An kashe jagoran siyasar \u0199ungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a Tehran babban birnin kasar Iran a ranar Laraba a wani hari da aka danganta da Isra&#8217;ila.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayanan da Anwar ya wallafa sun hada da wani bidiyo da ke nuna Firaministan yayin da yake waya da wani jami&#8217;in Hamas yana masa ta&#8217;aziyya.<\/p>\n\n\n\n<p>A shafin Instagram, akwai wani sa\u0199o daga Meta da Anwar ya bayyana wanda ya ce an cire bayanan ne saboda ala\u0199arsa da &#8221;mutane da \u0199ungiyoyi masu ha\u0257ari.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Ofishin Anwar ya bayyana cire bayanansa da Meta ya yi a matsayin &#8220;take &#8216;yancin fadin albarkacin baki \u0199arara&#8221; tare da neman gafara daga masu fasahar zamani.Anwar wanda ya gana da Haniyeh a Qatar a watan Mayu, ya kare ala\u0199ar da ke tsakanin Malaysia da Hamas. TRT AFRIKA HAUSA.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Katafaren kamfanin fasahar sadarwa Meta ya nemi afuwa kan cire wasu bayanai da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya wallafa kan kisan gillar da aka yi wa shugaban bangaren siyasa na \u0199ungiyar Hamas Ismail Haniyeh. A ranar Talata ne kamfanin ya nemi afuwar, kwana guda bayan ofishin Anwar ya gayyaci wakilan Meta don neman \u0199arin bayani [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2865,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[60],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2864","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-international-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2864","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2864"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2864\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2866,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2864\/revisions\/2866"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2865"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2864"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2864"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2864"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}