{"id":2825,"date":"2024-08-31T10:35:46","date_gmt":"2024-08-31T10:35:46","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2825"},"modified":"2024-08-31T10:38:03","modified_gmt":"2024-08-31T10:38:03","slug":"akwai-barazanar-yaduwar-cutar-faran-kamar-biri-mpox-a-nigeria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2825","title":{"rendered":"Akwai Barazanar Yaduwar Cutar Faran kamar Biri ( Mpox) a Nigeria."},"content":{"rendered":"\n<p> Kamar Yadda NCNC ta Bayyana Kawo Yanzu ba a Samu Wanda ya Mutu baHukumar Ya\u0199i da Cutuka Masu Ya\u0257uwa a Nijeriya (NCDC) ta ce an samu \u0199aruwar mutanen da suka kamu da cutar farankamar biri wato mpox a jihohi 20 da kuma Babban Birnin Tarayya, inda yanzu adadin wa\u0257anda suka kamu da cutar ya kai 48.<\/p>\n\n\n\n<p>NCDC ta bayyana haka ne a sa\u0199on da ta fitar a shafukanta na sada zumunta ranar Juma&#8217;a.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumar ta ce a mako \u0257aya daga ranar 19 zuwa 25 ga watan Agusta ka\u0257ai mutum takwas ne suka kamu da cutar, inda aka samu masu cutar guda hu\u0257u a jihar Enugu, sai \u0257ai-\u0257ai a jihohin Bayelsa, Cross River, Edo da Osun.Nijeriya ta \u0199ara sanya ido a duk hanyoyin shiga \u0199asar don hana ya\u0257uwar cutar Farankamar Biri Ta \u0199ara da cewa cutar ta fi shafar yara daga shekara \u0257aya zuwa shekara biyar.<\/p>\n\n\n\n<p>NCDC ta bayar da sanarwar ce a yayin da \u0199asar ta kar\u0253i allurai 10,000 na rigakafin farankamar biri daga Amurka ranar 27 ga watan Agusta.<\/p>\n\n\n\n<p>Tuni dai \u0198ungiyar Tarayyar Afirka ta ayyana cutar a matsayin wani lamari da ke bu\u0199atar \u0257aukin gaggawa a yayin da take ci gaba da ya\u0257uwa a kasashin Afirka.<\/p>\n\n\n\n<p>MAICECE CUTAR (Mpox) KUMA TAYA AKE KARE KAI DAGA KAMUWA DA ITA ? Mece ce mpox?Mpox cuta ce da ake \u0257auka daga \u0199wayar cutar bairos. Kuma alamunta su ne zazza\u0253i, da ciwon kai da ciwon baya da ciwon ga\u0253o\u0253i da kasala da yawan gajiya da kumburi.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198uraje za su iya fesowa su kuma watsu a gaba \u0257ayan jiki, sai dai sunfi yawa a fuska, sannan daga baya su bushe su ri\u0199a \u0253arewa daga jiki.<\/p>\n\n\n\n<p>\u0198wayar cutar mpox na janyo rashin lafiya a mafi yawan lokuta. Alamunta za su iya bayyana tsakanin kwana biyar zuwa 21 bayan kamuwa.Ya take ya\u0257uwa?\u0198wayar cutar za ta iya ya\u0257uwa idan mutum ya ta\u0253a mai \u0257auke da cutar ko ya ta\u0253a wani abin da mai cutar ya ta\u0253a ya kuma gur\u0253ata shi.Sai dai ha\u0257arin ya\u0257a cutar ga jama\u2019a ba shi da yawa.<\/p>\n\n\n\n<p> \u0198wayar cutar ta fi kama yara kuma zuwa kaso goma cikin \u0257ari na wa\u0257anda suka kamu da mpox za su iya mutuwa.A ina ake samun mpox?Cutar Mpox ta samo asali ne daga dazuzzuka a \u0199asashe masu zafi a Tsakiya da Yammacin Afirka kuma tana ya\u0257uwa tsakanin dabbobin daji.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ba a gano \u2018ainihin inda mpox take tasowa ba\u2019 sai dai \u0199wayar cutar ta fi ya\u0257uwa ne a tsakanin \u0253eraye da birrai.A ina aka fara gano mpox? An fara gano cutar a 1958 bayan cuta mai kama da \u0199yanda ta \u0253arke a cikin birai da aka yi amfani da su wajen bincike.An fara gano cutar a jikin mutane a Jamhuriyar Dimokura\u0257iyyar Kongo a 1970<\/p>\n\n\n\n<p>A ranar 13 ga Agusta, Cibiyar Ya\u0199i da Cututtuka Masu Ya\u0257uwa ta bayyana cutar a matsayin annoba a duka fa\u0257in nahiyar.<\/p>\n\n\n\n<p>A lokacin da \u0199wayar cutar ta mpox nau\u2019in clab 1b mai ha\u0257ari da saurin ya\u0257uwa a baya ta ya\u0257u daga Jamhuriyar Dimokura\u0257iyyar Kongo zuwa iyakokin \u0199asashe ma\u0199ota kamar Burundi da Kenya da Rwanda Uganda.<\/p>\n\n\n\n<p>Shin akwai maganin cutar?A yanzu dai babu wani takamaiman maganin mpox.<\/p>\n\n\n\n<p> Akwai riga-kafi uku da ake da su da kuma a Janairun 2022 Hukumar Magunguna ta Turai ta amince a yi amfani da wani magani da aka samar na cutar agana don jinyar mpox, sai dai bai wadata ba a cikin jama\u2019a.<\/p>\n\n\n\n<p>Hukumar Ya\u0199i da Cutuka Masu Ya\u0257uwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce akwai matakan da za a iya \u0257auka a matsayin riga-kafin cutar, wa\u0257anda suka ha\u0257a da Nisantar duk dabbodin da ke iya ya\u0257a cutar da suka ha\u0257a da marasa lafiya da mushe a wuraren da aka samu mpox da nisantar duk wani abu da dabbar da ba ta da lafiya ta ta\u0253a Killace dabbobin da aka ga alamun sun kamu da cutar, kada su ha\u0257u da sauran dabbobi.Dafa naman dabbobi da \u0199wansu da nononsu sosai kafin a ci ko a sha. <\/p>\n\n\n\n<p>Ke\u0253e mutanen da suka kamu, da kuma saka kayan kariya duk lokacin da za a je wajensu. Wanke hannu a-kai-a-kai bayan kula ko ziyartar marasa lafiya. Wayar da kan mutane kan cutar da matakan kariya.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kamar Yadda NCNC ta Bayyana Kawo Yanzu ba a Samu Wanda ya Mutu baHukumar Ya\u0199i da Cutuka Masu Ya\u0257uwa a Nijeriya (NCDC) ta ce an samu \u0199aruwar mutanen da suka kamu da cutar farankamar biri wato mpox a jihohi 20 da kuma Babban Birnin Tarayya, inda yanzu adadin wa\u0257anda suka kamu da cutar ya kai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2826,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2825","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2825","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2825"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2825\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2827,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2825\/revisions\/2827"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2826"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2825"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2825"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2825"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}