{"id":2802,"date":"2024-08-29T16:12:56","date_gmt":"2024-08-29T16:12:56","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2802"},"modified":"2024-08-29T16:12:57","modified_gmt":"2024-08-29T16:12:57","slug":"fetur-din-matatar-mai-ta-dangote-ya-samu-karbuwa-nahiyar-asia","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2802","title":{"rendered":"Fetur din Matatar Mai ta Dangote Ya Samu Karbuwa Nahiyar Asia"},"content":{"rendered":"\n<p>Matatar mai ta Dangote ta sayar da fetur mai \u0199arancin sinadarin sulphur (LSSR) kimanin metrik ton 500,000 ga nahiyar Asiya a 2024, yayin da ake sa ran shigar da tan 255,000 zuwa \u0199arshen watan Satumba, in ji kamfanin bincike na Kpler.<\/p>\n\n\n\n<p>Asiya ce nahiyar da ke kan gaba wajen sayen fetur da ke da \u0199arancin sinadarin sulphur (LSSR) na matatar Dangote a shekarar 2024, kamar yadda bayanai suka nuna, sai dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa adadin man da ake shigarwa zai ragu a watanni masu zuwa.<\/p>\n\n\n\n<p>Fitar da mai na LSSR daga sabuwar matatar ta Dangote na iya taimakawa wajen rage matsalar \u0199arancin mai a Asiya, nahiyar da ke da \u0199arancin fetur mai sinadarin sulfur da ake bu\u0199ata yalwata Singapore, wato babbar cibiyar jiragen ruwa a duniya.<\/p>\n\n\n\n<p>Kimanin metrik ton 500,000 na LSSR ne suka isa nahiyar Asiya daga Nijeriya a wannan shekarar zuwa yanzu, yayin da ake sa ran \u0199arin tan 255,000 za su isa a watan Satumba, kamar yadda bayanan kamfanin bincike na Kpler suka nuna.<\/p>\n\n\n\n<p>Amurka ita ce yanki na biyu mafi girma da ake shigar da man matatar Dangote, inda yawan adadin da aka shigar zuwa Arewacin Amurka da Tsibirin Caribbean ya kusan kai wa tan 700,000 a wannan shekara.<\/p>\n\n\n\n<p>Sau\u0199in farashinsa ya taimaka wajen \u0199ara yawan jigilar man a &#8216;yan watannin nan, inda Asiya ta \u0199arbi kayanta na farko a cikin watan Yuni, ko da yake dai majiyoyin kasuwanci sun yi hasashen cewa matatar Dangote za ta samar tare da fitar da \u0199arancin man LSSR a nan gaba, yayin da take shirin \u0199ara yawan kayayyakin da ake fitarwa daga sassan tace manta.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Tun da muka soma aikin tace mai a yanzu, yawan sinadarin mai na LSSR zai ragu matuka,&#8221; a cewar wanin babban jami&#8217;in kamfanin Dangote, yana mai kari da cewa babu wahala samun \u0257anyen mai a yanzu.<\/p>\n\n\n\n<p>Sarrafa \u0257anyen fetur mai \u0199arancin sinadarin sulphur irin na kamfanin West Texas Intermediate (WTI) yana samar da yawan LSSR, yayin da fitar da kayayyakin ya dogara ga bu\u0199atun mai a cikin gida a Nijeriya, in ji Emril Jamil babban jami&#8217;in bincike kan mai a LSEG Oil Research.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8220;An sayi mai sosai daga WTI. Za mu samar da \u0199arin man mai \u0199arancin sinadarin sulphur LLSR yayin da ake \u0199o\u0199arin ha\u0253aka sassan tace mai,&#8221; in ji Jamil.<\/p>\n\n\n\n<p>&#8221;Da zarar an warware matsalar bu\u0199atun cikin gida, akwai yiwuwar ba za ri\u0199a samun yawan LSSR ba.&#8221;<\/p>\n\n\n\n<p>Matatar man wadda ke samar da ganga 650,000 a kowace rana, kana mafi girma a Afirka, ta \u0199ara yawan \u0257anyen man da ake shigo da shi Nijeriya a cikin yanayi na rashin wadatar man.<\/p>\n\n\n\n<p>A yanzu haka dai ana kan gudanar da gwaje-gwaje a matatar don samar da albarkatun man fetur, a cewar kamfanin IIR Energy da ke nazari kan albarkatun \u0199asa<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Matatar mai ta Dangote ta sayar da fetur mai \u0199arancin sinadarin sulphur (LSSR) kimanin metrik ton 500,000 ga nahiyar Asiya a 2024, yayin da ake sa ran shigar da tan 255,000 zuwa \u0199arshen watan Satumba, in ji kamfanin bincike na Kpler. Asiya ce nahiyar da ke kan gaba wajen sayen fetur da ke da \u0199arancin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2803,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2802","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2802","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2802"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2802\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2804,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2802\/revisions\/2804"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2803"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2802"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2802"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2802"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}