{"id":2771,"date":"2024-08-26T15:39:14","date_gmt":"2024-08-26T15:39:14","guid":{"rendered":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2771"},"modified":"2024-08-26T15:39:15","modified_gmt":"2024-08-26T15:39:15","slug":"bayan-korar-sojojin-amurka-daga-nigar-wacce-kasa-zasu-koma-afarka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/?p=2771","title":{"rendered":"Bayan Korar Sojojin Amurka Daga Nigar\u00a0 Wacce Kasa Zasu Koma Afarka."},"content":{"rendered":"\n<p>Bayan da Nijar ta kori sojojin Amurka daga \u0199asar, Amurka ta ce tana kai dakarun nata wasu \u0199asashe \u0199awayenta da ke yankin.Amurka ta sanar da cewar ba ta da wani shiri na kafa sansanin soji a Nijeriya, inda ta kuma ce tana aika sojojinta da ta janye daga Nijar zuwa \u0199asashen Afirka da suke \u0199awance da ita.<\/p>\n\n\n\n<p>Manjo Janar Kenneth P. Ekman, jagoran Dakarun Amurka a Yammacin Afirka da ke \u0199ar\u0199ashin AFRICOM ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da &#8216;yan jarida a \u0199arshen mako a Abuja.<\/p>\n\n\n\n<p>Bayan amincewa da janye dakarunta daga Nijar baki \u0257aya a farkon shekarar nan saboda ta\u0253ar\u0253arewar ala\u0199ar diflomasiyya da gwamnatin sojin \u0199asar ta yankin Sahel, an samu wasu rahotanni da ke cewa Amurka za ta mayar da sansaninta zuwa Nijeriya.<\/p>\n\n\n\n<p>Tuni gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi, wanda Manjo Ekman ya tabbatar da hakan a yanzu.&#8221;Ina son shaida muku cewa babu wasu shirye-shirye na kafa sansanin sojin Amurka a Nijeriya, kuma na so na zanta da ku ne saboda batun na da muhimmanci,&#8221; in ji Ekman.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ce &#8220;Na fahimci yadda wanzuwar sojojin Amurka ke zuwa da amfani da kashe ku\u0257a\u0257e, duba ga yanayin da ake ciki, kuma ina son tabbatar muku cewa ba wannan batun ne ya kawo ni nan ba, babu wannan shiri. <\/p>\n\n\n\n<p>Abin da na zo tattaunawa shi ne batun tsaron yankin wanda yake shafar Nijeriya.&#8221;Jami&#8217;in sojin na Amurka ya \u0199ara da cewar ya zo Nijeriya ne don jin ra&#8217;ayin shugabannin soji da na fararen-hula a \u0199asar kan ayyukan Amurka na samar da tsaro a yankin.<\/p>\n\n\n\n<p>Ana bu\u0199atar sauraro, kuma wannan ce ga\u0253ar, wannan ne babban dalilin zuwan. Na fahimci yadda kasancewa ta a nan ke da amfani, \u0199ari kan ziyarar sauran shugabannin Amurka. Mataimakiyar Minista Stewart ta zo nan kwanakin baya, inda ta tattauna kan Ma&#8217;aikatar Tsaron Amurka da DOD nexus, inda ta ta\u0253o alhakin da ake da shi na amfani da \u0199ir\u0199irarriyar basira wajen ayyukan soji,&#8221; in ji Ekman.<\/p>\n\n\n\n<p>Ya ci gaba da cewa daga batutuwan da suka tattauna da mahukuntan Nijeriya sun ha\u0257a neman mafita ga matsalolin tsaron da ke damun \u0199asar, da yadda taimakon tsaro daga Amurka zai kawo sauyi.<\/p>\n\n\n\n<p>Manjo Janar Ekman ya kuma \u0199ara da cewar tuni aka fara kai sojojin Amurka da aka janye daga Nijar zuwa \u0199asashen Afirka da ke makotaka da Nijar, musamman ma Cote d\u2019Ivoire da Benin.<\/p>\n\n\n\n<p>At-tajdid News.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Bayan da Nijar ta kori sojojin Amurka daga \u0199asar, Amurka ta ce tana kai dakarun nata wasu \u0199asashe \u0199awayenta da ke yankin.Amurka ta sanar da cewar ba ta da wani shiri na kafa sansanin soji a Nijeriya, inda ta kuma ce tana aika sojojinta da ta janye daga Nijar zuwa \u0199asashen Afirka da suke \u0199awance [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2772,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"content-type":"","footnotes":""},"categories":[59],"tags":[],"class_list":{"0":"post-2771","1":"post","2":"type-post","3":"status-publish","4":"format-standard","5":"has-post-thumbnail","7":"category-news"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2771","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=2771"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2771\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2773,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/2771\/revisions\/2773"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/2772"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=2771"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=2771"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/attajdidnews.com.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=2771"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}